Sha takwas

20 2 0
                                    

*Ko Da So*
*18*

Harabar makarantar cike take da hayaniyar yara suna ta wasa da ciye ciye sakamakon sports day din da sukayi da yake ranar juma'a ce. Yan red house sune team din uncle Mukhtar kuma su suka cinye. A gajiya ya samu wuri ya zauna sannan ya dauki ruwan gefen sa ya fasa yana sha idan sa akan daliban.

Lokaci lokaci daliban sukan wuce ta gaban shi su masa hi sannan su wuce. Murmushi ne ya kubce masa ganin yadda malamtar dai da aka raina tafi komai jawowa mutum farin jini a wajen yara in yayi ta yadda ya kamata. A yanzu yaran har kallonsa suke yi a matsayin abun kwaikwayo. Hakan yasa yaji son yaran da koyarwar ya kara shigar sa sosai. Jin su yake kamar kannensa ne.

Yana kallonsu ne idonsa ya fada kan wani yaro dan ss1 Umar Sadiq ya kifa kan shi a kan gwiwar sa. Yaron dama sam bei cike walwala ba da surutu kuma komai nashi shi kadai yake yi. Ganin kowa yana tare da yan team din sa yau shi kuma ya ware yasa uncle Mukhtar jin babu dadi. A hankali ya taka inda yake ya dafa kafadar sa.

"A minute?" Ya tambaya, yana kallon yadda idon yaron yayi ja duk da ba kuka yake ba. Ba musu ya bishi.

Mukhtar ya gyara murya. "You can trust me." Ya fadawa yaron wanda yanzu yake kallonsa da alamar shakku a ranshi. Ajiyar zuciyarsa kawai yaji sannan ya dan yi shiru yace.

"Failure has always been my identity. Nasan saboda a yellow house nake shiyasa muka fadi..." Mukhtar ya zuba masa ido cike da mamaki da rashin sanin abun cewa.

Ya dafa shi. "Why do you think so?"

Umar ya daga kafada sama sannan ya tabe baki. "Babana ne ya gaya min. Kuma it's true. Ko fifth position ma ban taba yi ba. Whenever i want to focus, my whole attention freezes. Sai naji ba zan iya ba. Ko yau ma ina tsoron gaya mishi we failed."

Mukhtar ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa yana nazarin ta inda zai soma. Shi malami ne kuma his opinion matters. Yara suna kallon malaman su tamkar iyayen su ne kuma tunda uban wannan yaron ya sanya wa yaron gwiwa, shi ne in a good place ya karafafa masa gwiwa.

"Yadda nake gani ni kuma shine your future is bright. I wish dama ni ne kai, all qualities of perfection ka hada su you just need a little push. Ka san waye zai yi pushing dinka?"

Ya girgiza kan shi. "Kai ne. Kai zaka gayawa kanka zaka iya because no matter what, sai ka fara yadda da kanka zaka iya cimma wani abu. Ka sani na yarda zaka iya, all teachers ma naji suna zancen ka rannan a staff room. They all wish sune kai saboda yadda kake daban a dalibai. Ba hayaniya, ba surutu, just goodness."

Yaron yayi murmushi ya gyada kai. Uncle Mukhtar ya cigaba. "Baba kuma yana gaya maka hakane saboda yana so kafi shi."

Umar ya zare ido. "He's a great man fa. Major general ne."

Mukhtar yace, "wow, he's pushing you to do better in his own language."

Umar yaji dadi yace, "I will try. But please don't tell anyone not even him akan maganar mu."

"You have my word." Mukhtar ya bashi amsa sannan yaron ya mike da fara'ar sa. Daidai lokacin mahaifin Hafsah ya shigo school din.

Yara da yawa suka je suna gaishe shi. Malamai ma duk suka je suna gaishe shi yana amsawa. Mikewa Mukhtar yayi cike da jin nauyin mutumin ya taka har inda yake sannan ya russuna yana mika masa hannu su gaisa.

"Yauwa uncle Mukhtar dama saboda kai na shigo. Gashi ma lokacin masallaci yayi. In ba matsala, ka bini zuwa masallacin, akwai maganar da nake so muyi." Mukhatr ya daga kai ya kalle shi saboda yaga ko mene dalilin neman sa amma ya rasa. Gaban shi ya fadi, Allah yasa ba wani abu yayi ba.

"Yes sir. Let me round up." Da nauyin zuciya ya juya ya nufi staff room inda shi kuma mahaifin Hafsah ya shiga zaga school din yana jin dadin yadda komai yake tafiya. Shi mutum ne mai son farantawa jama'a. Mutum ne me kaunar taimako.

Ko da soWhere stories live. Discover now