40

15 3 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/BDPkkYJFDRj94oTZbxOVAN

*Ko Da So*
*40*

*Muka ce ba, muma dai bari mubi trend ɗin paid book, mu samu mu mori arzikin duniyar ributu, dan Allah Allah ku bamu kunya*

Dariyar da sukayi ta saka su tuno da. Nan suka buɗo shafin yarintar su kafin suyi aure sukayi ta daarawa har sai da sukayi me isarsu. Kamar ba su ba sai shiru ya ratsa a tsakaninsu. Hafsah tayi ajiyar zuciyar da ya zame mata dabi'a duk da zahiri ta bar Mukhtar, ta kuma jingine shi gefe, duk sanda wani abun ya kawo zancen sa sai taji zuciyarta tayi nauyi.

Bilkisu ta zuba mata ido tana jiran abunda zata ce. Hafsah ta kauda kai gefe saboda bata san ta inda zata fara ba, karshe dai ta zabi abun cewa.

"Nazo neman alfarma ne..." ta faɗa cikin sigar tsokana wadda Bilkisun bata lura ba sai dai nutsuwar da ta karayi tana jin cewa ko me Hafsah zata nema a wajenta zata iya yi mata komai wahalar sa.

Hafsahn ta sunkunyar da kai, "dama na yanke shawarar komawa karatun shine nace dan Allah ko Tariq zai nemo min admission..."

Wani kallo da Bilkisu ta watsa mata sai da yasa Hafsahn ta saki dariyar da take riƙewa ita kuwa Bilkisun ta ƙule sosai ta tashi gami da yin tsaki.

"Wallahi kin mugun raina ni. Mtsww dallah matsa." Da haka ta fice a ɗakin Hafsah tabi bayanta sukai kitchen inda ta fara zuba musu abinci.

"Ba don halinki ba dai." Bilkisun ta faɗi yayin da suka zauna.

"Ko don halin nawa ma nasan zaki yi min alfarma..." harara Bilkisun ta sake yi mata saboda kalmar alfarma da Hafsah take ambato tana mugun bata mata rai.

"Allah ya baki haƙuri me gadon zinare!"

Murmushi sukayi.

Tariq da ya shigo da motar sane ya yo ɓangaren Bilkisun samun yaran suna karatu yasa shi yin ɗakin matar tasa, daga baki ƙofar kitchen ɗin ya tsaya, yana kallon su, yadda suke cikin nishaɗi sai suka birgeshi, zuciyar da ke ingiza shi ya yi abinda ba haka ba yasa shi yin saurin barin wurin.

*****

Juyi yake tayi akan gadon don tunda yayi asuba ya kasa komawa bacci, idanunsa suka kumbura. Haka ya wuni daga masallaci sai ɗaki. Ya rasa me yake masa dadi a duniya gaba ɗaya. A yan kwanakin nan duk ya rame ya yi duhu musamman ma in ya tuna cewar Hafsah ta gama idda. Tunanin yana saka shi jin kamar yayi ihu don yana tuna masa da cewa yanzu ba matar sa bace haka zalika kuma ko wanne namiji zai iya aurenta. Idan wannan ya faɗo masa a rai sai yaji kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu. Ba don imani ba sai yace duk sallah sai yayi addu'ar kar ta samu miji.

A gefe guda kuma kewar yaransa tana nuƙurƙusar mishi ƙasusuwa ga kunyar iyayen Hafsah tunda har yau bai waiwayi gidan ba kuma babu wanda ya nemi zuwansa. Ba Mummy ba Abba. Ya rasa ta inda zai bullowa lamarin ya samu sa'ida.

Ko da yajewa da Inna zancen ta je ta amso masa yaran sa cewa tayi babu ruwanta. Hajara kuma ta ce bata da lokaci. So yake ko yaya yaga yaran. A wani bangaren na zuciyarsa ma yana son ganin Hafsah yaga ya ta koma.

Ƙarshe dai yaga gara yaje ya sami Rashida ta bashi shawarar da ta dace. Duk da yasan yanayin tunaninta sai a hankali amma ko meye zata faɗa masa yasan zai bashi mafita in ya haɗa da nasa tunanin.

Haka ya tashi ya shirya ya nufi gidan. Cikin mintuna kaɗan ya isa gidan. Gidane ginin zamani, madaidaici. Kana ganin gidan kasan akwai rufin asiri. Ya jima a motar kafin ya fito.

Ko da ya shiga ya tsaya a kofar part ɗin Rashidan sai da ya shafe mintuna kafin ta fito da kasko a hannunsa. A take wani wari ya daki hancinsa ya kalle ta cike da mamaki.

Ko da soTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang