36

13 4 1
                                    

*Ko da so....*

*36*

Zaune suke a carpet ɗin ɗakin Khulsum na rubutu, Aiman nata tsalle tsalle tsakanin Khulsul da gado, inda Hafsa ke gefe tana addu'a idar da Sallar ta kenan Abdallah na da Faruk na kan kujerar madubi, idar da addu'a ɗin da ta yi ne ta miƙe tana ninke sallayar da ta yi sallar akai duban su ta yi duk sun yi wani jugun jugun kamar waɗanda ke a gidan mutuwa, "ina buƙatar sawa kaina jarumta da haƙuri ko dan yaran nan" abinda ta ce da kanta kenan afim tace "Yaya zaman me kuke anan?"

Kallon ta Faruk ya yi kafin ya ce " ba komai Mami"

Girgiza kai Hafsa ta yi " a'a da komai in muka zo gidan nan dama wuri na keke zuwa ku takure?"

Wannan karan Abdallah ne ya yi magana " yanzu ai ba zuwa mukai ba, dawowa mukai"

Dan ɗaga gira tayi tare da furzar da iska kaɗan " dan kun dawo sai aka ce ku takure, kumma ci abinci kuwa?"

Aiman ne ya miƙe "Mami bamu ci ba tun ɗazu nake cewa suzo muje muci sunƙi" hijabin jikinta ta aje jikin alharga kafin ta ce "kuje ku ci abincin ku nima ina buƙatar privacy," ba wanda ya ce wani abu suka miƙe sukai falon ta bisu da ido tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

A falon suka zauna inda Faruk yaje dining area ɗin ya zuzzubo musu ya dawo falon, Abdallah ne ya miƙe ya nufi in da Faruk ɗin ya baro, "nafa zuboma ina kuma zaka?" Faruk ya faɗa da ɗan karfi.

Juyowa Abdallah ya yi " Mami zan zubawa tun safe banga ta ci komai ba" Faruk bai ce komai ba ya miƙawa Kulsum da Aiman na su, suna ci Mum ta  shigo da alamu daga unguwa take Faruk da Kulsum ne suka mata sannu da zuwa inda Aiman ya miƙe Mum mai kika siyo mata " hararar sa ta yi in ubanka ya ban ajiya ai sai in sayo ma" taja tsaki ta wuce ɗaki yadda take jin Haushin Muktar haka ma yaran.

A kwance Abdallah ya tarar da Hafsa hannun ta bisa fuskar ta da alamu tunani take, kamar yadda ɗabi'ar su take da Sallama ya isa, a hankali ta amsa tare da janje hannun nata bisa fuskar tata, yunƙurawa ta yi taɗan gyara zama, ahankali tace "a'a Abdallah bana ce kuje ku ci abinci ba eyyi?"

Kwanon da yake ɗauke dashi ya ajiye gefen ta " yanzu zanje inci kema kici wannan"

Buɗewa ta yi ta kalla sannan ta mayar ta rufe " tom shikenan zanci, kaje ka ci naka"

"Tom zanje inci anma dan Allah Mami ki tashi kici ko yaya ne, tun jiya ina kula ba abinda kika ci, in kin bari yunwa ta illata ki mu zaki sa wani hali, ki barmu muji da korar Abie dan Allah" kallon yaron ta yi itakam da ba ita ta haifi Abdallah ba sai tace yayi shekaru talatin dudu yanzu zai shiga 13yrs baima kusa shiga ba.

"Tom shikenan naji zanci, tashi kaje kar naka ya huce" maimakon ya tashi buɗewq ya yi da zummar ɗebowa ya bata cikin fushi ta ce ka tashi "ka tafi nace zanci a'a"

Narai narai ya yi da ido, ya miƙe jiki ba kwari ya yi bakin ƙofa, tausayin yaron ne ya kamata ko mai ta tuna cikin sanyin murya tace "Abdallah " juyowa ya yi fuskar nan ta yi abin tausayi, buɗe abincin ta yi tare da ɗiba ta kai baki " ka gani zanci, ko banci da yawa ba, karka damu kaji" gyaɗa kai ya yi tace " yawwa to maza kane kuci naku"

Falon ya wuce yadda yaga aiman yayi jigum yasan da wani abu duban yaron ya yi " Aiman menene mai yasa baka cin abincin?"

Narai narai Aiman ya yi da idanu cikin muryar ɓacin rai irin ta yara yace "ba Mun bace ta zageni, kuma ba abinda na mata" shiru Abdallah ya yi kafin ya ce " bakai ta zaga ba, ranta ne a ɓace" murmushi Aiman ya yi " Au" sai kuma yasa dariya ya koma cin abincin sa.


*******

Zaune Bilkisu take ta rafka uban tagumi, tun ɗazu baccin ya kasa ɗaukan ta, ranta a cinkushe yaje, haushi da takaicin maza duk ya cika ta, kallon Tariq da ke kwance gefen ta yana bacci ta yi, ta kuma jin wani ƙululun takaici, haannu da yakai gefen ta yaji alamun bata nan ya sa shi miƙewa.

Ko da soWhere stories live. Discover now