Ashirin

51 5 0
                                    

*Ko Da So*
*20*

*In kin Karanta kiyi sharing please*

Zumudin da Mukhtar yake ciki ya saka sau biyu yana farkawa daga bacci kafin asuba tayi. Sai da yayi sallahr asubah ne ma ya tuna ashe lahadi ce ba litinin ba. Duk da haka, farin cikin da yake ciki ba mai misaltuwa bane. Ko da ya sanar da Inna sai yaga farin cikinta yafi nasa yawa hakan yasa ko kokwanto kan aikin baya yi. Aiki ne da koyar da Hafsah zai kaishi gidan ba wani abu daban ba. Abunda yake ta jaddadawa kansa da zuciyarsa kenan musamman ma da ya rasa dalilin tsananin dokin da yake ciki.

Cike da walwala ya karasa inda Inna take wanki ya gaishe ta wanda ya sanya ta tsura masa ido kafin tayi ajiyar suciya mai nauyi.

"Inna?" Ya kira sunan ta yana jin tsoro kar dai ta chanja shawara ne amma ganin nisan kiwon tunanin da tayi ya saka ya fara tunanin wani abun ne daban da bai shafi aikin sa ba. Ganin bata ji ba yasa shima ya zuba mata idon yana kokarin karantar ta.

Murmushi yaga tayi sannan ta goge wani hawaye da ya fito daga idonta kafin ta maida shi. Ta sake murmushi wanda Mukhtar yake gani sam ba na farin ciki bane.

"Yau da ka fito dinnan ka sa min hannu ya tuna min da sanda ina amarya. Allah yaji kan mahaifin ku." Ta fada, tana sauke ajiyar zuciya cike da kewa da son mijin nata da ya tafi ya barta shekara da shekaru.

Mukhtar ya sake jinjina son dake tsakanin iyayen sa amma mutuwa da ba ruwanta sai da ta raba su.

"Ameen." Ya amsa, a take yana sake nazarin yadda shi kuma tashi rayuwar zata kasance. Zai so ace shima su shimfida makamanciyar soyayyar nan a gidansu shi da matarsa.

Inna ta tsame hannunta ta mike daga durkuson da tayi. "Nayi ciki."

Ko da yaji hakan sai da kwalla tazo idanunsa. Yasan yadda irin wannan ranakun suke kasancewa Inna. Haka zata wuni a daki cike da alhini da kewa. Ba zata cika magana ba, ranar ma ba za'ayi abincin sayarwa ba.

Wankin ya cigaba da yi zuciyarsa tana masa nauyi. Ana cewa soyayyar yara da iyayensu tafi ko wacce girma amma shi sai yake gani kamar Innar su tafi su san Baban su. Ko dan tafi su dadewa ne da shi bai gane ba. Watakila ita ta fi su iya nunawa ko kuma sabon da ke tsakanin su ya zarce tunanin kowa. Tunani yake yi kala kala game da mahaifin nasa yana kwatanta yadda zaiyi ya zama kamar sa ga matar sa da yayan sa. Tabbas shima yasan mahaifin sa mutum ne mai kirki da son kyautatawa iyalansa. Ko iya wannan ne halinsa nagari, yaci a yaba masa.

Shi ma hawayen ne ya fara zarya a kumatun sa sanda ya fara tuno irin sabon da sukayi, da sunan fulatancin da yake kiransa, da wasan da suke yi tun suna kanana. Ya share hawayen tare da addua sannan ya fara gaggauta dauraye kayan saboda ranar da ta kwalle a kansa.

*****

Idan tayi kyau, dukkan jiki yayi kyau. Idan ta baci, dukkan jiki ya baci. Wannan aba mara qashi da ake kira zuciya itace a kirjin ko wanne dan Adam da take bugawa, take rinjayar al'amura da ra'ayoyin mutane. Rashin qashin nata ya sanya soyyayar Tariq ta kama Bilkisu har ta manta da cewar soyayyarta gare shi haramtacciyar abu ce a gareta a gidan su.

Bata ji, bata gani. Domin ta daina jin maganganu da habaice habaicen yan gidan nasu. Ta dena ganin zunde da hararar da ake mata. Tariq take ji, Tariq take gani.

Zaune take a kasan kafet din wajen tana zuba mishi shinkafa da ta dafa da kanta taji takun takalmi yana karasowa gareta.

Daga kan da zatayi taga Ya Iftee tana takowa cikin wata doguwar riga da ta kama ta tsam ta bayyana dukkan adon jikinta. Fuskarta fayau take sai man lebe. A bayan ta yar aikin gidance take binta da tray. Suka karaso da murmushi a fuskarta.

Ta kalli Bilkisu sannan ta kalli Tariq. "Hello Tee."

Ya kalle ta cike da mamakin ganinta don tunda yake zuwa bai taba sanin nan ne gidan su ba. Ba kuma su taba haduwa ba tun bayan rabuwarsu. Jami'ar Legas sukayi tare har sukayi soyayya suka rabu kafin ma su kammala karatun su.

Ko da soWhere stories live. Discover now