Ashirin da uku

22 3 0
                                    

*Ko da So...*

*23*

Hafsa na zaune a falo tana kallo Momy ta shigo riƙe da leda gefen Hafsa ta ajiye, ya yin da Hafsan ya ɗago ta kalle ta kafin ta ce "Momy sannu da zuwa" ta faɗa tana ƙolarin buɗe ledar.

"Yawwa, sannu" kin dawo ashe itama ta tambaya.

"Eh tun ɗazu ma, kuma mai Umman su Basman ta samu?"

Zama kan kujera Mum ɗin ta yi tare da taɓe baki, mace ce, sai wani firiri ta tame wai ita tasa leshin da ya fi nawa"

Murmushi kawai Hafsa ta yi kan ce Momy waye ya baki alkaki?, kamar kinsan kwaɗayi nake ji walllahi"

"Hajiya Babba ce ta baki har na fito ta ce in kawo miki nama ce mata gobe zaki je ganin babin ta ce adai kawo"

Murmushi Hafsa ta yi "woo ni Hafsa mai kakanni" dariya Mum ta yi yo waye baida su ai sai dai in mutuwa sukai, wayar Hafsa da ta yi alamun an turo saƙo yasa ta dubawa Yaya Usman ne, Momy ta kalla tare da yin murmushi.

"Lafiya kike kallona kina wani dariya?," Wayar dake hannun ta, ta dan haskawa Momin wadda ta Karanta _Momy na falo kuwa_ abinda Usman ɗin ya ce kenan.

Rai Momy ta haɗe tare da cewa "cene masa bama na gidan," Ba musu Hafsa ta rubuta tare da miƙewa ta shige kitchen tabar wayar jikin Momy tana ta sheƙa dariya so take in yazo yaga wayar gun Mum ɗin ya yi tsammanin ita ce ta masa reply.

Daga ɗan nesa ta laɓe tana hangen falon har ya shigo ganin Momy yasa shi ƙoƙarin juyawa ta ce "Kai Usman zo nan"

Jiki ba ƙwari ya matso Hafsa ta fito kamar ba ita ke dariya ba ta matse "lah yaya ka dawo?"

Watsa mata harara ya yi tayi kamar bata ganshi ba ta hau lalube "Mum ina wayata?"

Ɗago wayar Momy ta yi daga cinyar ta, ta miƙo mata, ta amsa tare da zama gefen Momy wadda le faman faɗan mayar da su Khalil da Usman ɗin ya yi, ɗagowa ya yi rai cinkushe ya ce "anma  fisabilillahi nida gidan shikenan sai akawo wasu jarirai su takura mun?"

"Eyye sannu issasshe, gidan ku ai ka ce ba gidan ka ba," Momy ta katse shi.

Langwaɓar da kai ya yi tamkar wani ƙaramin ya ro, "aiko tafkar su zan koma tunda dole sai an kawo su"

Hafsa ce ta ɗago " Kai yaya dan Allah, kai lokacin da kake zuwa gidan Gwaggo ko Hajiya Babba kana takura musu ai b wanda ya tafke ka, su da gidan Kakan nin su"

Miƙewa ya yi a kufule "na fahinci ke kike zuga Mum kan ya rannan"

Momy ce ta ɗaga masa hannu "Malam dakata, ba wanda yake zugani, tunda abin naka haka ne ka fito da mata kayi aure ka bar yara su huta ai dama kana da abinyi, in kuma kaƙi zan nemo ma koma wace in haɗa ka da ita"

Dariya yasa Haba Hajiya Momy sai kace a lokacin da ai ko Yaya Sadik da ya haƙura da auren dolen da kika masa dan shi ɗan da ne"

Tsuke fuska Mum ta yi " kana wasa ko to mu zuba" ta faɗa tare da miƙewa tabar wurin Hafsa ta yi saurin bin bayan ta tare da shigewa ɗaki.

Faɗawa jikin kujera ya yi yana dariya Finally faɗan da yake gudu dai sun haɗu da momy ya sha shi.

Washegari da wuri Hafsa ta shirya zuwa makaranta, lectures ɗaya sukayi ta safe sai kuma ta 2 to 4 da Malamin ya mayar 12-2 ana fitowa daga Morning lectures ɗin kasan benen ASN suka nufa ita da Bilkisu domin siyan takardun da aka bayar sunyi sa'a babu mutane sosai wannan yasa suna zuwa aka sallame su, har sun wuce gaban exam office suka dawo ganin tabarmar shinfide ba kowa suna zuwa Hafsa ta faɗa kai tana faɗin kai har naji daɗi, yayin da Bilkisu ta mike ta hau duba fuskar ta jikin madubin da ke manne jikin bango.

Ko da soWhere stories live. Discover now