Sha hudu

20 1 0
                                    

*Ko da So.....*

*14*

_*in kin Karanta kiyu sharing please*_

Faka motar da Malam Musa ya yi cikin harabar school of hygiene yasa Muktar buɗewa ya fito, ɗan sunkuyowa ya yi bakin tagar "ina zuwa yanzu  zan miƙa in fito" murmushi kawai Hafsa ta yi ya yi gaba, yadda zuciyarta ta kasa yadda cewar wannan Makaranta ce ta gaba da secondry yasa ta buɗe motar ta fito, a nutse take tafiya tana bin tsirarin daliban da ke kai kawo, zagaye makarantar ta yi duka makarantar a idanun ta bata fi Faculty ɗin su ba, sai da ta gama yawon ta sannan ta dawo riƙe da alawar madara da ta gani gurin wata ɗaliba ta siya, Hango Muktar tsaye jikin mota yasa ta yin sauri ta karaso.

" Lah har ka dawo, Na bar ku kuna ta jira ko?"

Murmushi ya yi "a'a nima yanzu na fito" ya faɗa tare da matsawa daga jikin ƙofar motar bayan ya buɗe ta shiga shi kuma ya buɗe ƙofar gaba Malam Musa ya ja motar sukai gaba.

Kasancewar zasu sauke Muktar a Dala yasa Malam Musa bi ta cikin gari, ganin an biyo ta kasuwar kurmi ya sa Hafsa tunawa sunyi da Hidaya zasu so kamar ta ce su tsaya sai kuma ta tuna da halin Hidaya in taji ta zo ita kaɗai akwai rikici, adai dai ƴan Kado suka sauke Muktar yana ta faman zuba godiya kafin su wuce.

Hangar Malam da Hafsa ta yi yana alwala lokacin da suka shigo layin yasata faɗaɗa murmushin ta tamkar ta matso kusa da shi. 

Cike da fara'a ta ƙarasa inda ya ke alwalar, shima murumushin yake, rissinawa ta yi ta gai da shi kafin ta ce " yau zuwan nawa a sa'a na yi tunda ns fara tozali da rabin raina"

Dariya yi "assha ashema rabin rai ne abu bai yi daɗi ni da nake son fadar duka" itama dariya tasa a'a inna saka duka ran ina zan kai su Abba?" Karasowar Malam Musa riƙe da Jakar ta yasa ta amsa ta yi gaba tare da barin su suna gaisawa.

Kai tsaye gidan ta nufa, ƙarami ne ba can ba yafi rabin fuloti anma baza'a ce fuloti bane ginin ya yi kyau sosai dai dai misali ginin siminti ne ba shi da gate anma ba zaka kira shi gidan talakawa ba, gidan masu rufun asiri yafi dacewa da shi, da Sallama Hafsa ta shiga lokacin da ta wuce zauren farko, "a'a muryar waye nake ji kamar Muryar Bebilo" Gwaggo da ke zaune kan ƴar ƙaramar kujera ta mata tana wanke wanke ta faɗa" turo baki Hafsa ta yi lokacin da ta shiga riƙe da Jakar ta " Ni sai in koma, kurum dan mutun ya tsufa sai ya dinga faɗamin sunan tsoffi"

Dariya Gwaggo ta yi " kajimin ja'irar yarinya Ba sai ki koma ba, ai kinfi ni sanin hanya tunda ta ita kika bi kika shigo"

Malam da ya shigo riƙe da buta ne ya ce "koma kinji Hafsatu na, kyale ta kishi take"

murmushi Hafsa ta yi kamar dama da gaske komawar zata yi kafin ta ce "to ba inda zani tunds dai wanda nazo gunsa yana maraba"

Dariya suka sa dukkan su sannan suka soma tambayarta mutanen gida.

"Duk suna lafiya. Ina kawu Halipha?" Ta tambaya tana shigar da akwatin ta dakin Goggon. Kamshin turaren wuta ya doki hancinta har yasa ta rufe idonta. Son kamshi a jinin kakarta da mamanta yake amma ita bata wani damu ba. Tana yabawa da kamshi in taji sai dai bai dameta har ta saka da kanta ba.

Da akwatin ta a baya ta karasa shiga ɗakin wanda yake matsakaici ne. Gefen wardrobe ta hanga inda zata saka akwatin nata. Kamar ta tuna wani abun ta daga kai ta kalli jerin tukwane da tangaren da suke saman wardrobe din. A kullum burgeta sukeyi saboda babu inda ta taba ganin irinsu banda wajen Goggon. Kallon jeren take yi, girma girma kuma samfuri daban daban yasa ta soma kirga su.

Tana kirgen ne Goggo ta daga labule ta shigo ta tarar da ita. "Bebilo..." ta kira tana katse Hafsah wanda yasa ta buga kafa.

"Oh Allah, Goggo kin katse ni." Goggon tayi dariya.

Ko da soWhere stories live. Discover now