Sha daya

21 2 0
                                    

*Ko da So...*

*11*

_*In kin Karanta ki yi sharing please*_

Tsaye take gaban notice board din kamar yadda sauran dalibai suke tsaye da littafan su da biro suna kwafar draft timetable ɗin da aka kafe dazu. Ita kaɗai tazo makaranta a cikin kawayenta yau shiyasa ma take tsayen ita kaɗai.

Hannunta ta kai kan layin course din farko tana karanta da code ɗin cike da damuwa.

"Eh electricity ne. Dashi zamu fara." wani da ke bayan ta ya faɗa, A nan take taji kafafuwanta sunyi mata nauyi. Ita fa bata shiryawa exam ɗinnan ba. A bazata tazo mata kuma ace course din da bata iya ba dashi za'a fara. Test dinma da akayi kwafa tayi kuma malamin bai ma kawo musu sunga nawa suka ci ba.

Jiki a sanyaye ta bar tsakiyar jama'ar da suke ta faman tofa ra'ayinsu. Idanunta suka ciko da hawayen fargaba. Nan da nan ta kara sauri ta bar wurin. Female rest room kawai ta nufa. Tana shigo ta fara hawaye. Sai da suka gama zuba sannan ta wanke fuskarta ta fito. Driver dinta ta kira kawai sannan ta shiga masallaci ta kwanta tana jiransa. Tunaninta bai wuce yadda zatayi ta tsallake jarabawar nan ba.

Tana kwance kiran dreba ya shigo. Jiki ba kwari ta tashi ta tafi in da yayi fakin.

Ko da suka isa gida babu wanda ta tsaya gaisarwa kamar yadda ta saba. Ji take abubuwan sun cunkushe mata a lokaci guda kuma bata san ta inda zata fara ba.

Dakinta ta fara shiga tayi jifa da jakarta sannan ta fada bandaki inda tayi wanka, tana wankan tana hawaye har sai da taji saukin abun da ya tsaya mata a rai sannan tayi alwala ta fito.

Sallar la'asar ta fara yi sannan ta kwanta. Kugin da cikinta ya fara ne yasa ta tuna bata ci abinci ba. Ba'a son ranta ba ta nufi kitchen. Tayi sa'a babu kowa balle a sakata ciwon bakin magana. Tana bude flask taga dambun shinkafa, nan take mood dinta ya fara chanjawa ta diba ta koma daki.

A hankali take cin abinci wanda duk wanda ya hangota cewa zaiyi wasa take da abincin. Sai da ta gama ta sha ruwa sannan ta dauki wayarta ta kira Bilkisu.

Sai da tayi ringing din farko Bilkisu bata dauka ba. Duk da ba son yin magana take ba haka ta sake kiran wayar. Sai da ta kira kusan sau uku sannan kaninta ya daga.

"Bata da lafiya, kuma ta kulle kanta a daki." Gaban Hafsah ya fadi, ta rasa abun cewa.

"Hello?" Ta fada don ya maimaita abunda yace ta tabbatar taji daidai.

"Yaya Bilkin ta rufe dakinta kuma taqi magana dani." Duk da haka Hafsah bata fahimci abunda dan shekara bakwai dinnan yake cewa ba. Mikewa tayi ta nemi abaya ta saka cike da tashin hankali da tunanin me ya sami aminiyarta ta. Banda wayarta babu abunda ta dauka ta fito. Jin shiru sosai har yanzu yasa ta fahimci Mumy bata nan yau. Watakila fitar yamma tayi. Gate kawai ta nufa ba tare da tabi takan dreba ba taga me gadi yana zaune.

"Hajiya Karama sannu da fitowa." Fuskarta babu fara'a kamar yadda ta saba tace,

"Don Allah ara min dari biyu in na dawo zan dauko maka. Bana son komawa ciki ne, sauri nake."

Ba musu ya zura hannunsa a aljihu ya mika mata ita kuma tayi gaba tana godiya. A ransa yake tunanin ko me ya sameta. Ko me yake damunta. Yarinyar tana da mutunci sosai da girmama manya. Ba ruwanta da bambancin da ke tsakanin su na nauyin aljihu. Sosai yake jin dadin aiki a gidan sabanin gidan da ya baro inda yaran gidan suke masa kallon raini da rashin sanin darajar dan Adam.

"Allah yasa lafiya." Bai ma san sanda ya fada ba a fili saboda abun ya dame shi.

Ko da Hafsah ta isa titi kafar ta tayi budu budu saboda saurin da take yi.

Me adaidaita sahu ta tsayar ta shiga sannan ta fada mishi unguwar da zai kai ta. Sauri yake amma gani take kamar ya rage saurin adaidaitar.

"Malam dan Allah ka kara sauri." Ta fada tana kallon gefen titi.  A ranta take tuno wacece Bilki. Ta san duk abunda zai hana Bilkisu zuwa makaranta ba karamin abu bane domin ita din jaruma ce kuma mutum ce mai kwazo da yarda da kanta. Ko kadan bata da wani weakness da Hafsah zata iya cewa gashi. Komai nata a tsare yake, komai nata a lissafe take yin sa. Komai Bilki ta kan kalle shi da zuciya me kyau. Abunda zai karya ta ba karamin abu bane.

Ko da soWhere stories live. Discover now