Biyu

40 3 0
                                    

*Ko da so...*

*2*

Jiki ba kwari Hafsa ta bi shi da kallo lokacin da ya bar ajin,idanunta ta maida kan takardar da sunayen masu neman aikin ke kai Muktar ta kuma mai-maitamana, murmushi ta yi kafin ta ja biro jikin sunan nasa kamar yadda ta yiwa matashiyar matar ɗazu alamar ya ci interview ɗin.

Ahankali ta miƙe tana duba agogo kafin ta miƙawa Malamin da suke interview ɗin tare, wanda  ke kusa da ita bari in je gun Abba, karɓa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, bata damu da rashin maganar tasa ba ta bar ofishin.

Har ta wuce ta dawo, fuskar ta ɗauke da murmushi "lah Anti ina kwana?"  ta faɗa cikin har shen turanci matar ma murmushi ta mayar mata, "kyace ina kwana mana, anya Hafsa? ace tunda kukai candy ko a ɗan leƙowa a gaisa," matar ta mayar cikin turanci.

"Kai Anti wallahi abububuwa sukai yawa, kuma gani na na yi in nazo ai duk kuna aji zan ɗauke muku hankali, anma ai ina cewa Abba ya gaisar mun da ku."

"Eh fa ya na faɗe wataran, bari in je sauri nake Hafsa ta faɗa"

" nima kin ga aji zan shiga" matar ta fada kafin ta yi gaba.

Abba na zaune yana duba takardu Hafsa ta shigo da Sallamar ta, ɗagowa ya yi yana kallon ta kafin ya ce "to sarkin rikici badai nufin ki anan zaki zauna ba?," girgizar kai ta yi a'a tafiya ma zan yanzun nan naga an mana fixing class 2-4 gwanda in je.

"Towo class kuma gashi ni yanzu ina som mu tattaunawa da team ɗin da sukai interview ɗin, dan mu samu mu a turawa waɗan da suka samu nasara sakon kar ta kwana zuwa gobe su fara zuwa, musanman wanda zai ɗauki Physics ɗin nan."

"Tom shikenan kawai bani kuɗin ɗan sahu da na ƙara masa 200 a kan normal price zai kaini,  dan innace sai driver ya zo kaini zan makara."

Dubu Uku Abba muƙo mata "Allah ya bada sa'a," murmushi ta yi "Amin sunma yi yawa ai, Allah ya saka da alkairi" ta faɗa kafin ta wuce.

A nitse Muktar yake tafiya tun da ya baro ɗakin gwajin ya kasa tunanin hukuncin da mutanen zasu yanke tsaf ya tsaya dan naƙaltar su sai dai fuskokinsu ba su nuna sun yi maraba ko akasin haka da jawabin da ya gudanar ba, duda cewa shi a ransa yana jin kwarin gwiwar ya yi abin da ya da ce ko da bai samu Malamin senior ba to su ɗauke shi a matsayin malamin primary.

Har ya wuce mai lemon ya dawo soyayyar Umman sa da lemo mai ɓawo yasan ya bazai iya ganin lemo ya wuce bai sai mata ba, Ɗari biyun sa kenan, "na ɗari za'a bani" ya faɗa a takaice, Baba Yakubu ne ya yi miƙo masa bakar ledar kai dai Muntari kana son siyan lemon ɗari naga randa zaka sai na du ɗari biyun.

Dariya Muktar ya yi, " adai ci gaba da tayamu da addu'a wataran na dubu zan siya," Allah dai yasa ai nima zan so haka.

A kishin giɗe Innan take tana jin radiyo ganin shigowar Muktar ya sata gyara zama, yanayin fuskar ta ya nuna ɗoƙi da son jin labari mai daɗi na an ɗauke shi aikin, ajiyar zuciya ya yi kafin ya zauna kusa da ita ledar lemon ya miƙo mata kafun ya ce "wanne shirin suke?"

"Kaji dai shirin Muda likita nake son ji, ta yau ƴan siyasa sun siye filin shine nake saurara, ya aikin kuma fatan an dace.,?" Iska ya ɗan furzar "to gashi nan dai sunce zuwa dare zasu turo mana sako," ya faɗa jiki ba kwari.

"To Ai shikenan, ai mutun baya wuce ƙaddarar sa in ba'a dace ba sai mu cigaba da jarrabawa" Umman ta faɗa ga. Shiru kawai sukai kowa da abin da ke zarya a ransa yayin da sautin Radio ke ta shi a tsakar gidan.

***********
Sam Hafsa ta gaji da ajin na farko ba son Physics take ba sabida bata ganewa, na biyu malamin da ke koya musun yada ya wani haɗe rai yasa duk haushi ya cikata, ga kuma haushin kanta da take ji tun ɗazu da take tawowa idanun ta sun gaza goge mata hoton mutumin ɗazun ita a yanzu ba zata iya faɗin asalin mai take tunani akan sa ba.

Ko da soWhere stories live. Discover now