Ashirin da shida

31 5 0
                                    

*Ko da So.....*

*26*

Tunda Hafsa ta dawo gida ranta yake a cinkushe, kasa daurewa ta yi, ji take kamar ta sa kuka saboda damuwa, tunanin Muktar da halin da yake ciki duk ya cika mata rai, miƙewa ta yi daga gadon da take kwance ta nufi wardrobe ɗin ta, doguwar riga milk da ta sha adon zaiba ta zaro ta sanya kafin ta fice daga ɗakin.

Falon Mum ta leƙa, bata ciki da alamu tana bed room, daurewa Hafsa ta yi ta ƙarasa "Momy zani Babban gida ganin babin,"

Mum da ke kwance ta ɗan ɗago, "naga shekaran jiya kinma fi yau dawowa da wuri, anma still kika ce kin gaji bare yau da kuka kai yanma".

Fuszar da Iska Hafsa ta yi, "ai Mum gani nayi inna biyewa gajiyar nan sai baby din ta yi wayo banje ba,"

"sai kin dawo" kawai Mum ta ce ta maida kanta jikin filo.

Ko mai ta tuna kuma oho, zumbur Mum ta miƙe tare da fitowa tana ƙwalawa Hafsa kira wadda ta ja ta tsaya a falo tana roƙon Allah yasa kar Mum ta ce mata ta bari sai gobe, dan zuciyar ta zata iya bugawa kan tunanin ko ya jikin Muktar ɗin yake.

"Kin ɗauki kayan barkar da nace ki kai mata kuwa?"

"Af kinga na manta, da sai naje duk kunya ta ishen nazo hannu rabbana,"

Juyawa kawai Momy ta yi inda Hafsa ta ɗauko ledar kayan jariran da Mum tasa aka kawo mata daga ɗaya cikin shagunan ta.

A harabar gidan nasu ta ci karo da Yaya Usman ya dawo, kallon agogon da ke dantsen sa ya yi kan ya ce "Malama ina zaki da magaribar nan?"

"Sannu da zuwa yaya ta fara faɗa, kafin ta ce "Babban gida zani barka kullum ba lokaci."

"Ki Bari gobe sai muje nima ina so in je ban samu dama ba."

Girgiza kai ta yi "No yaya jibi ina da test inna ce zanje gobe bani da damar karatu," ta yi ƙarya dan tasan abinda kawai zata ce kenan ya barta.

Ɗan shiru ya yi inda ta yi gaba cikin daƙiƙu ya juyo "muje kawai naci abinci acan," ya faɗa tare da danna remote ɗin motar sa da ke hannun sa, kujerar gaba mai zaman banza ta zauna inda ya shiga tare da jan motar suka bar gidan.

Wayar sa ya zaro tare da fara kira, minti kaɗan aka ɗaga, "Please Mabaruka ɗan bawa Hajiya wayar," abinda ya ce kenan kafin daga baya ya ce "Hajiya ina wuni?" bayan ya ɗan yi shiru da alamu na ta amsa gaisuwar tasa ne, sai kuma ya ce "dama yanzu zamu zo walllahi, yunwa nake ji Please kisa a ɗan tuƙan samo ko da miyar dage dage ne na ci, ah da akwai ma miyar kuka kenan ya faɗa yana murmushi tare da cewa sai mun zo." Indai son tuwo miyar yauƙi ne to wurin Usman ba daga nan ba.

Hafsa da tunda suka hau titin ta langaɓar da kanta jikin glass ɗin tagar motar idanun ta a lumshe ya kalla kafin ya ce "Hafsa mai ke damun ki ne?," Ahankali ta buɗe dara daran idanun ta ta ɗora su a titi kafin ta ɗan gyara zama, "ba komai yaya kawai na gaji ne yau sosai."

"Ni kinsan banson ƙarya, kinsan nasan ƙarya kike tunda kuwa ko Momy ba zata nuna min sanin halin ki ba."

Murmushi ta yi "to dai yau baka fahincen dai dai ba sam." Ta faɗa tare da komar da kan ta jikin glass ɗin.

Muryar sa da abin ya ce ne suka daki kunnen ta aɗan razane ta kalle shi kafin ta basar.

"Soyayya kika fara?" Shine abinda ya ce hankalin sa kusan rabi kanta.

Daurewa ta yi ta janyo nutsuwar ta danma kar ya gano dan tun jiya ta gama yadda soyayyar Muktar ta gama kama ta, a nutse ta yi murmushin ƙarfin hali "No Soyayya da wa?" Nida ba ni da saurayi, kawai school ɗin ce ba daɗi sam karatun na ban takaici, kaga last semester na faɗi electricity ga this semester shima Physics ɗin ba daɗi, ga Mum ta kafe sai dai a dena min lesson ɗin nan, kuma wallahi ina fahinta tunda da akayi test ɗin ma nayi ƙoƙarin amsawa fiye da last term da banma gane mai ake a electricity ɗin." Ta faɗa fuskar ta na nuna alamun rashin jin daɗi da damuwa.

Ko da soWhere stories live. Discover now