Talatin

26 3 1
                                    

*Ko da So....*

*30*

Tafe suke a mota zuwa filin jirgi inda Hidaya zata koma makaranta, a wurin faka motocin driver ya faka motar, Hidaya ta ɓata rai tare da yin narai narai da ido tamkar zata yi kuka, Hafsa ta ce " Hajiya ki fita mana kin takura mun rakoki kin san ina da abinyi sai ka ce akwai wanda ya miki dole sai kin je nesa karatun"

Hidaya turo baki ta yi cikin shagwaɓa ta ce " Maimakon ma kuyi kuka, haka ma fa Ammi tama ƙi rakono"

" zan fa tura ki waje, a'a to ya zata rakoki lokacin da tace kiyi BUK mai kika ce?" Hafsa ta faɗa.

Tsaki Hidaya ta yi " you are not helping matters " ta faɗa tare da barin motar, sai da ta ɗanyi nisa Hafsa ta fito da ɗan saurin ta, ta rungume ta ,"Zan missing ɗin ki, Allah ya kaiku lafiya."

sun ɗan jima a haka kafin su rabu, kuma sallama sukai kafin tayi ciki ita kuma Hafsa ta koma mota, Malam Musa ya ja su ka ɗau hanya. Wayar ta ɗauko daga aljihun jakar ta, Number ɗin Bilkisu ta hau kira sai dai taƙi shiga Number busy, tsaki ta yi, duban Baba Musa ta yi bata son takura masa sai dai kuma tana matuƙar son ji daga bakin Bilkin.

kai tsaye gidan su Bilkisu tasa ya kaita, a harabar gidan suka haɗu da yaya Ifti,  wadda tana ganin Hafsan ta ɗan tsuke fuska, kusan tunda akai abin Bilkisu da Tariq Yaya Ifti ɗin ke jin hsushin Hafsan, Sam bata nuna ta gane tana jin haushin nata ba ta ce " Ya Ifti ina kwana?, tana nan kuwa"

" lafiya ƙalau, ni da ba ɗaki guda muke kwana sannan ba faɗan rayuwar ta take ba ina zan sani"

Hafsa bata ce komai ba ta yi shigewar ta ranta fal cike da jin Haushin Iftin, sam abin na bata haushi yadda Iftin ke wa Bilkisun bacin yadda Bilkisun ta damu da farin cikin ƴan uwan ta.

Falon ba kowa wannan yasa Hafsan yin sama nan ɗakunan ƴan matan gidan yake, kai tsaye ɗakin Bilkisun ta nufa, bugu ɗaya ta ce ta shigo. kwance ta same ta rib da ciki ƙafafun ta sun yi sama waya manne a kunnen ta tana zuba dariya.  Murmushi Hafsa ta yi tare da samun wuri ta zauna.

"Hafsa ta zo muyi magana anjima, ok zata ji " Ta faɗa tare da aje wayar ta dubi Hafsa Tariq ne, yace a gaishe ki"

murmushi Hafsa ta yi "ai ba sai kin faɗa ba yadda farin cikin ki ya nuna, nasan shi ɗin ne, ina amsawa, walllahi ganin ki da nayi ya kuma tayar mun da abin da ya kawo ni"

Tashi zaune Bilkisu ta yi "towo mai ya kawo ki, kin san nayi mamakin ganin ki sabida nasan kina da lesson ko an gama?"

Kwafa Hafsa ta yi "uhumm! Wanne gamawa ai abinda ya kawo ni kenan, Bilkisu I am In love"

"Wow! What ke ɗin?" Bilkisu ta faɗa cike da mamaki.

"Eh nidai Hafsan da kika sai, ina son sa sosai walllahi, problem ɗin  Mum bata son sa, that's not it only kamar shima bai sona, even though he confessed loving me"

Kallon ta Bilkisu ta yi duk ta faɗa, "Matar nan kin ɗauki soyayya da zafi, but batun Momy ke zaki sa ta so shi, shi mai yasa kika ce baya sonki?"

Numfashi Hafsa ta furzar "tunda ya zo yamin maganar yana sona bai kuma bi ta kaina ba, kuma fa  ya fa amshi Number ta, amma ko da wasa bai kira ni ba,  he should have chased me at least before given up, ba daga ya faɗa ban bashi amsa ba ya janye is that love?, ni da nake mace kullun sai naji ina son kiran sa, sai in daure at least I have some pride left"

"He might be busy fa, ko kuma wani abu ya samu wayar sa, ko kuma wani abun daban bawai dan baya sonki ba." Bilkisu ta faɗa.

Shiru Hafsa ta yi kafin ta ce "kin tabbata, abinda kika faɗa har ranki?" Hafsa ta fada tana Kallon Bilkisun.

Dariya Bilkisu ta yi "kedai Hafsa na fahinci zafin so ne da ke, ai ba zan faɗa miki what did I not mean."

"  Bari kiga to in tafi kar yazo baya nan nassn tas Mum zata ce ace masa an dena lesson ɗin."

Ko da soWhere stories live. Discover now