7

16 2 0
                                    

*Ko da So...*

*7*
Har Hafsa ta shige zuciyar Muktar bugawa take sosai ya kasa yadda ita ya gani da wani cikin ni shaɗi ya kuma kasa yadda da zancen ta da kunnuwan sa suka ji na aure zatai, yaran ne suka dawo dashi daga hayyacin sa ta hanyar yi masa sannun da zuwa Hannun sa ya kalla wanda Aiman ya riƙo yana masa sannu da zuwa "Abie ashe baka manta damu ba" yaron ya faɗa, murmushi Muktar ya yi " ah ka taɓa ganin inda Abie zai manta da Aɗfal ɗin sa am busy ne shi yasa".  Faruk ne ya gaishe shi cike da girmawa kafin ya ce "Abie ashe zaka zo?" yaƙe ya yi kafin yace "zanzo mana yanzu ma zuwa na yi in tafi da ku"

Cike da mamaki Faruk ya ce "tafiya da mu kuma?" gyaɗa kai kawai Muktar ya yi "eh kuje maza ku ɗebo kayan ku sauri nake" su Aiman ne sukai ciki cike da murna ya yin da Abdallah ya bi bayan su jiki ba kwari har Faruk ya juya sai kuma ya jiyo ya ce "Abie Aure ka yi?" kallon yaron ya yi sai yaga ya cika masa ido ya kuma girma haka ne fa yaran su girma suke kuma hankali suke girgiza kai ya yi jiki ba kwari "no" kawai ya ce "maza ku ɗebo kayan Please ya faɗa.

Mum na zaune tana voice message da ƙawayen ta yaran suka shigo, bata damu da su ba ballanta ta musu tsawar da ta saba dan yanzu bata jin haushin su kamar da, dama can haushin Hafsa ta nacewa Ubansu ke bata haushi ta hakke kan su yanzu kuwa sam bata jin haushin su.

Ganin suna fitowa da kaya niƙi niƙi yasa ya aje wayar tare da miƙewa "Kai Faruk ina zaku haka da kaya ba na ce se ending month zaku dinga haɗa wanki ba?" kafin Faruk ya ce wani abu Aiman ya yi wuf ya ce "Ba wanki bane Abie ne ya ce mu haɗo kayan mu zai tafi damu" yaron ya faɗa cike da ɗoki da zirgilli iri na yara.

"what! Mum ta zaro ido shi Muktar ɗin ya ce kuzo ku tafi yana ina?" ta fada cike da ɓacin rai, bata jira amsar su ba ta zari hijabin da ta yi sallah ta fita yana tsaye jikin motar da Hafsa ke hawa tunda ta dawo gidan hango Hajiya da ya yi yasa yaɗan fara sosa kai tare da yake wanda ko laɓɓa bai kawo ba, duk nauyi da kunyar ta ya cika shi domin shi ɗin ya haifu dole yana jin nauyin iyayen Hafsa na sako musu diyar su.

Ɗan russunawa ya yi yana gaidata a hasale ta ce sannu isasshen mara mutunci wato rashin ta idon naka har yakai ka nuna mana iyakar mu ka nuna mana bamu isa ba, wato mu riƙe ma yaran tsawon shekara dan wulaƙanci bamu isa ba ka zo ka same mu kace zaka tafi dasu sedai ka gansu a harabar gida kace suzo ku tafi kai mai yara ko?, ce ma akai ita Hafsan bata da haƙƙi kansu ko me, ko kuwa sakin da ka mata be isa ba se ka zo ka tsinka mata zuciya, tunda kuwa in har aka nemi yaranta har biyar ba'a gani ba kan a gano ubansu ne ya sace su ai zuciyar ta bugawa zatai.

zai yi magana ta ɗaga masa hannu "bani da lokacin jin banzayen kalmomin ka wanda ba mutunci bare ladabi ciki kayi gaggawar barin gidan nan, randa ka shirya ɗaukan su ka dawo" fuuu ta koma ciki.

ajiyar zuciya Mujtar ya yi ransa na masa suya ya rasa wannan wacce irin rayuwa ce, shi bega abin da ya yi na rashin kyauwa ba jiya Innar sa ke faɗa masa Mum ɗin tazo tace yazo ya kwashe yaransa, ya zo kwashe sun abin ya zama masifa. Ya jima a tsaye kan ya bar gidan.

Hajiya na shiga ɗaki ta ce su maida kayan ba wanda ya ce wani abu sukai ciki, inda Aiman ya dire kayan rai ɓace lokaci na farko tun mutuwar auren iyayen su da tausayin yaran me tsanani ya kamata, kamo Aiman ɗin ta yi tana bashi baki abun yaro se gashi ya warware yana cikata da surutu.

Hafsa da ke tsaye jikin taga tanajin su ta koma gado yaraf ta zauna hankalun ta tashe me Muktar yake nufi na zai tafi da yara, wallahi bazai yiwu ba inma aure ya yi ba ruwanta dole ma ita zata riƙe yaranta tunda ba shi ya mata naƙudar ba, a karo na farko tun haɗuwar ta Muktar da bata ji ɓacin ran abinda Mum ta masa ba.

Kai tsaye gidan su Dala Muktar ya nufa Inna na zaune tana gyaran Salak ya shiga da sallamar sa amsawa ta yi tare da ɗagowa dan Muryar sa ta yi kama da ta me damuwa, kamar yadda ta zata fuskar sa ta nuna damuwa sosai gefen ta ya koma ya zauna tare da gaishe ta ya yi ta amsa cike da kulawa tare da tambayar meke damun sa.

Ko da soWhere stories live. Discover now