Bakwai

21 1 0
                                    

*Ko Da So...*

*7*

_*in kin Karanta ki yi sharing please*_

Tunda dare ya raba Khairi ta dasa kuka, gajiya da rarrashinta da Mum ta yi yasa ta ɗauke ta takaiwa Hafsa wadda ke bacci, kukan Kairin ya tashe ta, Mum ta ɗora mata ita a cinya tare da ficewa daga ɗakin.

Ko dan Hafsan ce ta ɗauko ta daga gidan Kakannin ta oho anma Hafsan na kunna fitila ta kalle ta sai ta yi shiru wannan yasa Hafsan miƙewa ya haɗo mata abincin ta sannan ta bata ta goya ta, ta jima tana jijjigata kafin ta yi bacci, kwantar da ita tayi kafin ta samu itama ta kwanta.

Huɗu saura Khairi ta tashi ta hau kuka, Hafsa na hanma ta miƙe ta kuma bata abinci sannan ta goya sa sai dai taƙi bacci, haka ta sauke ta yarinyar ta hau wasanta yayin da Hafsan ke gyangyaɗi.

Gari na wayewa Hafsa ta shirya itakam ba zata iya ba gidan Yaya Sadik zata tayi Bacci, wanka ma a toilet din falo ta yi dan khairi na Bacci bata son ta tashi Mum tace ba zata ba.

***********

A kwance ya same ta tana daddana waya. Kamar ba zai magana ba, har ya wuce sai dai hango tulin kayan abincin da suka ci jiya da daddare akan dining table har yanzu bata ɗauke ba ballantana a yi batun wankewa yasa shi kallon Lokaci cike da takaici, uku saura idanun sa suka gane masa. Sake kallonta yayi yaga yadda tasha kwalliya kamar ba gobe, jewelries dinta ma duk sunyi matching da kayan da tasa, A kallon farko tayi bala'in burge shi don son kwalliyarta na daga dalilan da yasa ya aure ta, wannan yasa bacin ransa game da kwanukan ya yi sauƙi.

"Ameerah!" Ya faɗa muryar sa cike da emotions din da ba ma zai tantance me yake ji a lokacin ba. A hankali ta dago ta kalle shi kafin ta maida hankalinta kan wayar.

"Haba Ameerah, this is not right. Kalli gidan ki fa!" Bata fuska tayi a ranta tana cewa yanzu zai fara wannan faɗan nasa mara amfani yabi ya cika min kunne.

"Oh sweetheart..." ta fada a shagwabe lokacin da take ƙoƙarin ta shi zaune duk da bata ajiye wayar ba amma hankalinta na kan shi.

Sai da taga yana kallon ta sannan ta haɗe hannu. "Ban san me yasa kai baka fara kallon abu me kyau ba kafin ka nemo lefi. Look at me, duk kwalliyar nan taka ce! Da ace na tsaya wani wanke wanke i would have wasted alot of my time... wannan kwalliyar sam ba zan samu lokacin yinta ba."

Cike da rashin sanin abun fada ya shafa fuskarsa sannan ya nemi wajen zama.

"You can always manage your time Ameerah. Idan kika tashi da wuri ki ka gama da aikin gidan kikayi kwalliyar you have all the day to press your phone. Wallahi ana shigowa falon nan tsamin miya ake ji." Ya fada yana mikewa don da ganin yanayin fuskarta ma ba zata bashi amsa me dadin ji ba.

Dining din ya nufa ya kwashe kwanukan sannan Yayi kitchen dasu. Ko da ya shiga kitchen dinma sai yaji kunya ta kama shi saboda kurar da yayi ga wani wari da yake tashi sama sama. Bude fridge yayi ya ga vegetables din ciki sun rube. A take ran sa ya baci sosai. Ya tsaya, ya zaga, ya juya, ya tsaya ya rasa ta inda zai kamo lamarin. Sai kawai yayi tsaki ya fita.

"Okay okay ki taso muyi aikin nan don wallahi saura kadan dai gidan nan ya zama bola. Ki zo muyi aikin, i have something for you. Very special!" Yayi winking a karshe yana kakaro murmushin karfin hali ya yaba a fuskar sa. Tana magana kasa kasa ta taso ba da son ranta ba.

Rahina fa zata zo tayi anjima..." bai tsaya jinta ba yaja hannunta sukayi kitchen din. nade hannun rigaarsa ya yi, inda ya kaɗa kumfa, malama ina wankewa kina ɗaurayewa,  ya faɗa lokacin da hau kiciniyar wanke kofi, tsai kawai ta yi da idon ta kansa ita kam bata shirya taɓa ruwa yanzu ba amma tasa in ta yi magana faɗa zai yi, wayarsa da tayi ringing ya da shi jan tsaki hannun sa ya fara gogewa da towel  kafin ya zaro ta.

Ko da soWhere stories live. Discover now