Daya

216 16 3
                                    

*Ko Da So...*

Bismillahir rahmanir raheem

*1*

Idon ta cike da hawaye take kallon sa, fuskar ta ɗauke da mamaki gami da tsoron yadda lokaci guda ya birkice kamar ba masoyin ta abin alfaharinta ba.

Anya shi dinne kuwa?

Hannu tasa ta goge hawayen da ke famar zarya a kuncin ta, don tafi ganinsa da kyau, duk da tasan gogen su bawai shi zai sa zafafan hawayen nata su tsaya ba.

Warware manyan idanunwanta akan sa.

Shi dinne dai, Mukhtar. Mukhtar dinta. Mijinta, uban yayanta. Sanye yake da farar shadda kamar ko wacce ranar juma'a. Farin kaya ba karamin ƙara masa kwarjini da kyau da haiba yake ba.

Ta sake goge wasu hawayen dake zuba daga kwarmin idonta ta kalle shi.

"Kar kayi mana haka Abban Abdallah... dan Allah..." ta faɗa cikin karaya. Bata san me zata ce masa ba amma abunda yake bukata daga gareta yafi girman tunaninta. Ba zata iya ba.Shima yafi kowa sani.

Kamar ba zaice komai, kamar yanayin nata ya bashi tausayi sai dai ɗan guntun tunanin da ya yi yasa shi kauda kai daga kallon, saitin da ya juya ta matsa ta ko yi nasarar jefa kwayar idanun ta cikin nasa.

Ta sa ni Muktar ɗin ta na son ta domin tana iya ganin zallar tausayin ta gami da madarar son ta a idanun sa, ta sani soyayyar Muktar gare ta  bata gushewa a zuciyar sa. Takan gane haka ne a Idaniyar sa da basa taɓa iya boye zallar ƙaunar ta, duk kuwa da tsananin bacin ran da yake ciki. Take taji hawayen idonta sun fara ƙafewa, saboda wani hope da taji ya ziyarci zuciyar ta.

Karkarwar da take yi tuni ta tsaya, hawayen ma kamar an ce su tsaya. Cike da kwarin gwiwa ta matsa kusa dashi, murmushin kwarin gwiwa tuni ya mamaye fuskar ta, kallon sa take tana neman irin nata murmushin a fuskarsa. A hankali ta kamo hannun sa tana tsara mai zata ce a ranta da zai sa ya sauko daga fushin nan, sai dai yadda ya juyo a fusace ya  sata sakin sa da sauri kamar wadda ta taɓa wuta.

Cikin daƙiƙu idanunsa suka gauraye jajir kamar garwashi cikin kausasasshiyar murya mara amo yafara magana wadda inda ace Hafsa tasan abinda zai furta kenan da tuni ta toshe masa baki tahau magiyar kar ya furta.

"Na sake ki Hafsa. Na sake ki saki daya. Ki bar mun gida yanzun nan..."

Kalmomin da bata taɓa koda da wasa tsanmanin jin su daga bakin Muktar ba, kallmomin da suka saka dukkan wata gaba jikinta ta sage. Kalaman da ta jisu tamkar saukar dalma a zuciyarta.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un... Muktar ka sake ni fa kace?" Sam sam idaniyar ta sun dena gane komai yayin da ɗakin ya hau juyawa da ita tamkar fanka.

Yaraf ta zube a gurin, a ruɗe ya yi kanta yana Faɗin, "Ummu Abdallah..."

Yadda ya yi maganar yasa yaran su da basu san mai ke wakana ba suka yo falon da sauri, kamar wata ƙaramar ɗiyar sa haka ya ɗauke ta ya yi waje yaran suka bi shi yuuu...

A karo na farko kenan a rayuwarsu. Tun  tasowar su da suka taɓa ganin Mamin ta su a irin wannan yanayin. Tuni  jikin su yayi mugun sanyi. Mami mace ce mai kuzari gami da jarumtar ɓoye ciyo, duk runtsi tana daurewa ta farantawa yaranta sun shaƙu da ita ita ce koman su, kamar yadda suke koman ta. Ko kadan basu san menene rashinta ba a rayuwar su. Ko wannen su yana samun lokaci daga gareta dai-dai gwargwado. Wasu lokutan in suna hira takan ce musu su zama masu dogaro da kansu domin wataran zasu tashi babu ita a duniyar ma gaba daya.

Sai gashi yau rashin lafiya ta kwantar da ita ji suke tamkar duniyar ta tsaya musu. Ko da yake a wajensu duniyar ce ta tsaya domin Mami ita ce rayuwar su.

Ko da soDonde viven las historias. Descúbrelo ahora