BIYAYYAH

Von maryamad856

41.9K 1.9K 467

Labari ne akan wasu masoya guda biyu da suka had'u wajen yiwa iyayensu BIYAYYA. 'Kir'kirarran labari ne b... Mehr

BIYAYYAH
BIYAYYAH
BIYAYYAH....
BIYAYYAH...
BIYAYYAH...
BIYAYYAH......
BIYAYYAH....
BIYAYYAH.....
BIYAYYAH....
BIYAYYAH....
BIYAYYAH......
Biyayyah......
biyayyah.......!
biyayyah.....!
biyayyah.....!
biyayyah....!
biyayyah....!
Biyayyah....!
Biyayyah.....!
Biyayyah.....!
Biyayyah....!
biyayyah.....!
biyayyah....! 59-60
Biyayya....61-62
biyayya....62-63
biyayya.... 65-66
part.....67
biyayy.....68
biyayy....70
biyayya......
biyayya.....
biyayya....73
biyayya......73
biyayya.....74
biyayy......75
biyayya......76
biyayya....77
biyayya.....78
biyayya.....79
biyayya.....80
biyayya....81
biyayya.....82
Last page....83
Appology/Biyayya....12-14

biyayy....69

859 39 0
Von maryamad856

*BIYAYYA*

By
*Maryam Abduul*

Wattpad@Maryamad856

💫 *DA BAZARMU WRITERS ASS*💫

*page....69*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

---------------Bata jima da shigaba baba mai gadi yabi bayanta, mom na mata sannu da zuwa ita da auta, yai sallama falon tare da dire ledojin kayan agabansu.

Itakam Dije sanin tasan daga ina suke yasa bata tambayeshiba, haka nan mom da auta ganim abiye yake da ita yasa basu cemasa komiba illa kawai" sannu" da sukai mai.shima ganin hakan yasa shi ficewa tare da amsawa.

Mom ce ta kalli Dije tace" Khadija daga ina kayan suke badai su suka bakikba?" duk tajeho mata tambayar lokaci guda.

Sai da tadai-dai taa nutsuwarta dan tasan muddin ta fad'i gaskiya to ta mutu eajen mom, sunkuyar da kanta tai kan tace" mom tilas tamin sukai akan hakan bayadda banyi dasu su bariba amma sunqi, tare ma muka zo da Fiddauseen ita da yayanta"

Mom taja nunfashi kan tace" shikkenan amma dai ki kiyaye gaba bansan wannan halin duk da su suka takurakin, meyasa basu shigoba?

Dije ta dan rausayar da murya kan tace" casukai rakiya kawai sukai shiyasa, insha Allahu zan kiyaye gaba"

"Ok" kawai mom tace ta miqe tare da haurawa samanta.

Ganin hakan yasa Dije qwallawa Hanne kira, koda tazo catai mata" ta d'auke kayan gaba d'aya " dan jitai sunma fice mata daga rai gaba d'aya

Ganin hakan yasa auta miqewa tare da surar leda d'aya ta hayewarta saman su Dijen batare da tace qalaba.

Girgiza kai kawai Dije tai itama ta haura saman.koda tashiga d'akin nan ta tadda auta kan gado ta baje kaya tana dubawa, kallo d'aya tayimata ita da kayan ta wuce toilet dan watsa ruwa.

Koda ta fito ma bata kalletaba, ganin hakan yasa auta miqewa tsaye tare da matsawa kusa da ita tace" plz aunty in nai laifi kiyi haquri"

Ko kallonta batai ba ta cigaba da abinda take, still bata haquraba tasake furta" plz aunty na kada kisa yaya ya daken in yaji ranki yana 'baci kuma sanadiyata"

Hararata tai kan tace" ai kakkaryake zaiyi ba dukaba mits, amma kinsan mom ta nuna battaso meyasa na bada zaki d'auka"

Auta ta zun'buro baki tace" nifa kawai jinai ina sha'awar ganin kayan, amma kiyi haquri" ta qarasa fad'a tare da miqewa tana tattara kayan.

Kamar Dije tasan abinda take shirin aikatawa yasata janyota tare da fad'in " bawai ina nufin ki maida bane, kawai inaso ki dinga lura da abinda mom keso ko battaso, kefa kin girma kin zama manya"

Jin ance mata babba yasa ta harda wani fad'ad'a fuska tace" nadaina aunty insha Allahu daga yau bazan sakeba kayi haquri kinji" ta qarasa tana had'e hannayenta biyu.

Ganin hakan yasa Dije sa hannayenta ta raba hannayen autan tace" ya wuce".

Koda suka kammala abinda zasuyi zamansu sukai asaman har saida hanne ta musu maganar an gama abincin dare, sannan suka sakko.

Anan din ma kamar had'in baki suka sakya baiwa mim haquri. Mom tai murmushi tace" bakomi 'ya'yana Allah dai ya muku albarka "

Nan suka amsa dab"ameen".

........
Yanzu watan Dije biyi da fara makaranta yayinda Ashraf ke wata uku da tafiyarsa.

Masha Allah komi yana tafiya mata da sauqi dad'in da d'awa kuma da lesson d'in da ake mata, yanzu kam har qananun turanci take yi.

Wannan qoqari da jajircewa da take nunawa yasanya dad yimata gagarumar kyauta, gashi test d'in da sukaima tayi nasara.

Yanzu haka anbasu hutun midterm, sai dai mai lesson bai fasa zuwaba yana kuma iya bakin qoqarinsa wajen ganin ta gane abubuwan da yakeson fahimtar abinda yake kiya mata.

Wannan hutu da suka tafi duk da bawani yawa gareshiba dan sati biyune kad'ai, sannan kuma da sun koma zasuyi jarrabawar zanhin karatu na farko.

Duk da hutun baida yawa hakan baisa dije ta shagala dashiba, sosai ta nutsu akan karatunta tana son ace taci jarrabawar dazasuyi batason taga ta watsawa dad da mom qasa a ido.

Fiddausee takanzo kusan kullum ma, kuma jikin mom d'in nata yayi sauqi, idan tazo kam basa aikin komi sai karatu yini sukeyi akansa.hakan yasa mom tasakya sakin jiki da ita ga wata qaunarta data keji tanayi tunda itama tanason 'ya'yanta.

Ana e gobe zasu koma makaranta auta ce ta kalli Dije tace" aunty yanzu gobe zaku koma school sai naji ba dad'i wllh kwana biyun nan ana zama ayini aita hira"

Dije ta kalle auta tare da girgiza kai kana tace" kedai auta Allah yashiryeki wau yaushe zakison kin girmane, a haka zamu aurar dake kije kinawa mijin shirme, yanzu fisabilillahi meye abin damuwa akan komaqata school nida ba boarding nakeba"

Auta ta turo baki yayo gaba kan tace" yanzu kawai dan na nuwa damuwata shine zakice haka, to kita komawa ma ni ina ruwana nima ai zan koma tawa makarantar" tana qarasa fadin haka ta miqe daniyar ficewa daga d'akin.

Cikin sauri dije ta riqota tare da fadin" haba tawan ni na isa nace haka, sorry mai da wuqar kinji autar mom"

Murmushi tai takoma ta kwanta ba tare da tace" uffanba" itama Dijen ganin hakan yasata rabuwa da ita, miqewatai ta fad'a toilet dan wankeahi taga yayi datti ba laifi, kusan kwana biyi bata bi takansaba, sai dai kusan duk lokacin dazata wanke takan tuna da wasu abubuwan da Ashraf yakemata, takanyi murmushi kawai in ta tuna dahakan.



.......
Ashraf kam ba abinda yake acan sai aikinsa bashi da damuwar komi akansa illa kawai yadda zai 'bullowa da maganar dad akan komawarsa gidan sa, sam baison maganar nan ko kad'anma, yakanji wani zafi acikim qasan zuciyarsa meyasa za'aso yakebe da wacce sam baison ta ko kad'an.

Wayarshi ya janyo tare da danna lambar mom yau kusan watan uku amma bai kiraba tunda ya kira yasanar dasu yasauka lafiya, badan komiba sai dan jin haushin maganar da yabaro agida.

Ringin biyi tai aka d'aga cikin farin ciki da kewar d'an nata tace" son ka kyauta abinda kai kaji"

Sosa qeya yashiga yi kamar yana gabanta kan yace" kiyi haquri Mom bana samun kowama sabida matsalar netwrk, sannan aiki yamun yawa ni kad'ai nefa akan abubuwan"

Mom tace" yayi amma ko baka nememuba ai ka nemi matarka ko, yau wata uku cif bajin lafiyarta, yatake duk ba wannan, meyasa haka son yaushane zaka canza?"

Turo baki yai kamar yana gabanta duk duniya ba abinda yatsana irin yadda su mom da dad ke nuna damuwa da wannan kucakar yarinyar.

A hankali ya furta" sorry mom, aikine sukamin yawafa shiyasa"

Mom tai murmushi dan tasan tabbas bawai aikin ne yamasa yawa ba a'a kawai dai baison mu'amala da itan ne kamar yadda har yanzu baisonta, yaushane mafarkinsu zai cikane, kullum dai addu'ar take, Allah yaganar dashi.

"Naji Allah yakyauta, bara na bata wayar sai ku gaisa"

Kamar saukar aradu haka yaji akansa, sam baison abinda zai had'a shi da ita, amma bayadda zaiyi ba zai iya cemata "a'a ba" baison 'bacin ranta.

Janye wayar yai daga kunnensa, tare da sata a handsfree, yayi dai-dai da fad'in " salamu alikum" da dije tai.

Kamar bazai amsaba can kuma ya amsa ciki-ciki bawai dan tajiba ko kar taji.

Tsawon mintina goma ba wanda yasakya cewa" uffan" ganin hakan yasa Dije datse kiran tare da fad'in " inaga mom kudin sun qare." ta qarasa tana miqa mata wayar.

Mom kam da tason ba wani kudi da suka yanke amma bata ci komiba sai kar'bar wayar kawai tai ta adanata agefenta.azuciyarta kam neman shiriya kawai takewa Ashraf.

'Bangarensa kam wani tuquqin baqin cikine ya mamaye zuciyarsa, lallaima har akwai wanda zasuna magana awaya yakatse masa kira, wato taga makwancinsa kenan, ba shakka zaiyi maganinta ba kad'anba" da wannan tunanin ya fad'a toilet dan watsa ruwa.

Itakam dije wani wawan tsaki taja kan tace" mutum sai baqar zuciya, ko shed'an sai haka" ta haura part d'inta.


.......Washe gari kam da wuri ta shirya ko auta bata tsayaba tai tafiyarta, wanda yanzun dad ya ware mata mota da driver shiyasa yanzu basu fiya tafiya tare da autaba.

Allah yatemaketa ba malamin da yazo da yakema jarrabawa garesu kuma english ce dasu, hakan yabasu damar zama tare da qara duba littafinsu.

Basu suka shiga exam d'in ba sai wajen qarfe takwas sannan suka fara.

Alhmdulillah bakamr yadda suka zata bama dan sun d'auka zatai wahala amma sai sukaga sa'banin hakan, sai dai 'bangaren dije sosai gabanta ke fafuwa tunda ita din bawata gwanar english bace, gashi ance suyi wasiqa tasan kam awannan babin sai ahankali, gwarama inda aka tambayesu abu surubuta tunda tayi hadda sosai.

Fiddausee ce ta fuskanci kamar tana cikin damuwa hakan yasata janta gefe tare da tambayarta ko lafiya?.

Nan tashaida mata fargabar datake damunta da yanayin datake ciki, jin abinda tace d'in ma sai yabata dariya, amma sai ta 'boye hakan dan tasan halin qawar tata, nan tashiga kwantar mata da hankali tare da lallashinta.a haka har driver yazo ya d'auketa.


............
Jummai nagani zaune gabanta tulun takaddu gaba dayansu rubutune ajiki, sai dai duk iya qoqarin nasan ganin me ta rubuta hakan yagagareni, dan bansamu damar ganiba.

D'aya daga cikin takaddun ta d'auka tare da mannawa asaman qirjinta, wasu hawayene suka biyo kan kumatunta a hankali naga ta furta" inasonka masoyina, kai nake kwana nake tashi dashi, dan Allah kasoni kamar yadda nake son ka, ka taho gareni"

Share hawayen tai tare da miqewa tamaida dukka takaddun qarqashin kayanta sanan ta fice daga gidan zuwa wajen Iya.

..........Hanne ce zaune tana faman had'a danbu dan yau mom tace" shi za'ayi musu" dije ce ta fad'o kitchen d'in wacca tun da tadawo daga school cikinta ke ta kukan yunwa, gashi mom tace" ba'a gama abincinba" shine tashigo taga meke faruwa.

Turus tai tatsaya tana kallon Hannen kan tace" yau kuma me ake mana ne?"

Hanne tai murmushi kan tace" danbu akeyi"

Dije tai murmushi kan tace" amma ba irin wanda muke bako, dan naga wannan har kala ya canza, me kikasa?"

Hanne tai dariya tace" kai dije bakki rabo da abin dariya, kalar da kikaga ya janza ba komi bane face corry, shine yasa yazama yellow haka, kuma na shinkafane ba natsakiba"

Dije ta sakya matsowa tare da d'iban danbun duk da zafin dake dashi hakan bai hanata kaiwa bakinta ba tace" kai amma yayi dad'i, bakiji wani qamshe da yake yiba"

Hanne tai dariya akaro na biyi tace" lallai kam kice wannan danbu yatafi dake"

Dije tace" hmm kedai bari, amma wai ya akai duk kika iya abincin 'yan birni ne kodai kema anan aka haifeki?"

Tambayar taso bawa Hanne dariya sai dai tasan yadda tai ta gimtseta kan tace" a'a daga qauye nema nazo, kinsan qiru to daga qauyen nan nake, anan duk na koya, zuwa yasa Mom take koyan abubuwa da yawa har na iya, gashi kuma inayi"

Dije ta riqe baki tare da fad'in " kece nima in ana koyon zan iya"

Hanne tace" sosaima me zai hana"

Dije tace" yawwa kinga yaya Imran yace zai kaine wajen wata tadinga koyan to naga kamar yafasa daga yanzu ke sai ki dinga koyan ko?"

Hanne ta rausayar dakai kan tace" a'a bazan hana yayanki samun ladaba, nasan yana sane da cewar zai kaikin, ni yanzu abu d'aya nake son muzauna dake mu tattauna, amma in kinsami lokaci fa"

Jin hakan yasa dije fad'in " ai ni koyanzu ashirye nake fad'i inajinki"

Hanne tace" a'a bana tsaiwabane dole sai anzauna, kuma naga ai yinwa ma kikeji kije inna gama zan kawo"

Girgiza kai Dije tai kan tace" ai nadaina ji, yanzuma tsayawa zanyi mu qarasa tare"

To sanin halin Dijen yasata bata musa mata.Hanne matashiyar yarinyace me kimanin shekaru ashirin da biyar, tun tana da shekara goma sha takwas mom ta d'akkota aqauyen qiru, su suka sata a islamiya har tasauke, boko kam iya scendory tayi tace" ita ta gama" koda suka matsa mata catai ita battaso, hakan yasa suka qyaleta.

Sai dai ayanzu tanajin inama batai wasa da wannan damar ba dan taga yadda 'yan mata ke tururuwa kan karatun butin kowacce ace tazama wance, sai dai ba yadda zatai hakan yasa ta cire wannan burin. Sai dai zamanta anan da kuma huld'a da mutane yasa ta koyi abubuwa da dama, tasan wasu abubuwan sosai fiye da yadda batai tsammaniba.

To ki bayan dasu kammala a falo suka baje dan yau ba'a hau dinning ba mom ce tace" aci a qasa" hakankwa ya musu dad'i.

Dije kam sai cewa take" ita tai girkin" mom kwa dariya kawai takeyi tare da yabawa abincin nata, duk da tasan ba itan taiba.

Koda suka kammala kitchen tayi wajen Hanne dan ta mugun matsowa taji zancan me zata mata.

Hanne kam sai dariya take mata akan wai tanason jin gulma.ita dai kawai gyad'a mata kai take akan ehhh din ta matsu"

Hanne ce ta gayra zama tare da riqo hannayen Dijen cikin lafazi mai dad'i tace" da farko dai inaso in miki wani tambihi akan abu gida daya ko nace kalma d'aya wato kalmar *aure*"

"Maganar gaskiya kalmar aure tana da tasiri babba akan dukkan wani musulmi, matuqar kalmar nan tasauka a ko ina yakamata adinga darajata.maganar gaskiya shine sam bakya daraja kalmar ko kad'an balle ki bata haqqin ta"

Dije ta zaro ido tare da fad'in " ni kuma na shiga uku"

Hanne ta kalleta tare da sakye had'a hannayenta waje guda tace" a'a baki shigaba, kawai dai ina so na miki nuni ne akan kalmar, kalmar aure ba'abar wasa bace ko sakaci, kisani dani dake ba d'aya ba da akwai babban banbanci, banbancin kuwa shine aure"

"Ya kamata kisan me kikeyi me kuma zakiyi, kisani aure kikazo gidannan kuma bauta yakawoki ga wa? Ga mijinki ya kamata kisan haqqinsa akanki kisan girmansa da darajarsa da kuma qimarsa"

Ta dora da fadin"Maganar gaskiya abinda kike banajin dad'insa ko kad'an, mijinki ne amma kina d'aga masa murya kina mai rashin kunya, duk da bansan auren me kukaiba amma koda bakko san juna bai kamata kina mai hakanba, kisani duk macen da take d'aga wa mijinta murya to tana cikin fushin ubangiji, balle har tamaida mai da raddi wato martani yazamana suna sa'insa, yafada ta fad'a "

"Sam wannan ba d'abi'a ta qwarai bace yakamata ki kama mijinki kuzauna dashi zaman lafiya, duba da yadda yanzu lamuran suka sauya saikiga mace na bin namiji akan yasota, balle ki da Ashraf yake kyakkyawa san kowa qin wanda yarasa, tun wuri kiyiwa kanki karatun ta nustsu ki kama mijinki hannu bibbiyu in ba hakaba watarana zakiyi danansin sakyen da kikai, kina zaune wata zata zo ta qwace miki miji, ya kamata kiyi d'amarat shawo kansa duk da banda tabbacin hasashen danakeyi akanku"

Dije ta sauke ajjiyar zuciya tabbas duk abinda Hanne ta fad'i mata gaskiyane, amma battajin zata iya d'amara akan na mijin da bai sonta.duban Hanne tai kan tace" bazan 'boye mikiba amma nida Ashraf sam bamason junanmu auren had'i akamana bana soyayyaba, taya zance zan d'aura d'amarar zama dashi alhalin bai sona kum ban tunanin zai sonin"

Hanne ta gyara zama kan tace" wannan duk mai sauqine, da fari ni kaina nayi hasashen hakan, dan na tabbata da auren soyayyane hakan bazai dinga faruwaba, amma kada ki manta shifa ba dutse bane, shi d'in d'an adam ne kamar sauran mutane, kuma yana da rai da lafiya, dole zai buqaci mace wacca zata dinga kulawa da buqatunsa da kuma sauran al'amuransa, dan haka ke yakamata keyi wannan aikin wato ki shawo kansa zuwa gareki"

Dije ta fidda ido waje yare da dafe qirji tace" nikam taya zan iya hakan, bashifa da kirki kokad'an"

Hanne tace" kul kar naqara jin kince haka, ai shi miji komi yamaka kada kaduba kabarshi da Allah, in ba hakaba sai ki kwashe ladan naki, sannan daga yanzu banso na sakya jin kince masa Ashraf gatsal koba komi kina ganin su dad da mom zasuji dad'i kina cewa d'an su Ashraf ba kara, amma kuma kina cewa Imran yaya"

Dije ta girgiza kai alamar "a'a" yayinda Hanne ta d'ora da fad'in " to kinga, dan haka daga yau shima kina kiransa da yaya, dan Allah kinji khadija"

Dije ta d'aga kai alamar tagane, " to amma kina ganin zai kalline amatsayin matarsa kuwa kamar yadda ake fada.

Hanne tai murmushi kan tace" mai zai hana ke kuwa, sai dai idan har bakibi yadda yakamata kibi dan wajen jawo hankalin nasaba, matso kiji" ta qarasa tana rad'a mata wani abu a kunne.

Ganinai dije tai saurin rufe idanuwanta tare da fad'in" anya kuwa zan iya Hanne?"

Hanne ta kashe mata ido d'aya tace" mai zai hana ki jarraba ki gane, amma yakasance kuna ake'bene bawai cikin jama'a ba"

Dike tace" to zan gwada insha Allahu, nagode da tunasar dani da kikai"

Hanne tace" bakomi ai yiwa kaine, abu nagaba kuma shine dole kisan wasu sirrika musamman akan gyaran jiki da yadda ake kula da miji, wannan zai tai makamiki dan cimma burinki"

Dije tace" to a ina zan sani nikam banda wanda zai koyan"

Hanne tace" kwantar da hankalinki ni nan zan dinga koya miki wasu abubuwan sannan zan kawo miki litattafai da dama da akai magana akan rayuwara aure, abu na qarshe inaso kiyi anfani da iliminki na addini da kuma boko wajen kare martabar aurenki, huld'a tsakaninki da namiji sam bata tashiba domin ked'in matar wanice, kidinga tuna hakan aranki da zuciyarki"

Dije tace" insha Allahu zan dinga qoqarin hakan, na gode aunty Hanne"

Hanne tai dariya tace" au yau kuma aunty na koma?"

Dike itama tai dariyar tace" ai daga yauma kin koma hakan, tunda kina min lesson danma bance malama aunty Hanne ba"

Hanne ta riqe baki kan tace" a hakanma ya wadatar, kije kada mom tace na riqe mata 'yar tayin hirar"

Dije tace" ok, anjima zan dawo fa auntynah"

Ita dai hanne batace komiba, koda dije ta fita Hanne ta sauke wata ajjiyar zuciya, ba shakka tana matuqar san yarinyar, tanason taga takasance da Ashraf tun randa ta fara ganinta amatsayin matar sa, tana musu sha'awar juna amatsayin ma'aurata, kuma tana musu fatan kasancewa tahar abada, fatan daya shine Allah yasa zuciyar Ashraf tai sanyi akan khadijan, ubangiji yasa yasota fiye da yadda base tsammaniba" nan tasha da ameen.

Editing is not allow.....

Vote,
Comment,
Share and like.....

*Mrs.Abduul ce*

*Page...69*

BISIMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

----------Koda ta fito daga wajen hannen samanta ta haura ganin ba mom a qasan, tana fad'awa d'akin tayi zaune gefen gadinta tare ta sanya hannayenta kan kumatinta, tabbas abinda hanne tagaya mata gaskiyane, meyasa takeaon yin fatali da karatunta da kuma ililminta ba addini wanda mahaifinta ya koyamata, ba shakka zatai mai biyayya kamar yadda taiwa iyayenta biyayya, sannan kuma zata gwada sa'arta akan hakan, zatai haquri da kuma juriya akan duk abinda zai biyo bayan wajen jajircewarta akan yarda da auren da kuma yi masa biyayya.

Da wannan tunanin ta fad'a toilet saida ta watsa ruwa sannan ta fito qasa.

Mom da dad ne zaune yayinda dad ke cin abinci ita kuma mom na masa hira.

Tsugunnawa tai tare da gaidasu dan ayanzu kam tasaba da duk wata had'uwarsu da gaisuwarsu, dayake wannan al'adar gidance.

Cikin fara'a dad yace" yanzu ake ban labari mai dad'i ashe diyar tawace tamana abinci"

Da fara'a dije tace" ehh dad yafi na kowa dad'i ko?"

Dad yai murmushi kan yace" sosai ma kuwa, ai ko bakomi kinfi wannan sukowar 'yar uwar taki" hakan yayi dai-dai da sakkowar auta daga part din ta.

Auta ta zun'boro baki game da fad'in "Allah dad itama ba ita taiba aunyy Hanne cefa tai"

Mom tai saurin cafe wa da fadin" a'a ba wani hanne datai ko hannu bata sa mataba, ita tai dakanta"

Jin hakan yasa auta miqewa tare da fashewa da kukan shagwaba tai hanyar part d'in ta.

Ganin hakan dad yasa shi miqewa tare da fad'in " rabu dasu autana ai kinma fisu iyawa, ni wannan d'in ma kamar kashi na keci"

Jin hakan yasa auta juyowa harda 'yar fara'arta tace" yawwa dad daman nasan ai baiyi dad'iba mom ce kawai take zugata"

Mom tai dariya irin tasu ta manya tace" ah nifa gaskiya na fad'i"

Dije tace" ehh man mom"

Ai kam auta ganim sun had'e mata kai yasata komawa kujera daban tace" ni daga yauma ba 'yar gidan nan bace, na daina cin abincin ku gaba d'aya "

Mom da hanne mai zasuyi inba dariya ba, mom ce tace" yafi komi sauqi, awajenmufa amma banda ke"

Ana kwa cikin hakan saiga auta ta sakko qasa kusa da dad tare da miqa hannu wai zataci abincin.

Habawa me kwa so Mom zasuyi inba dariyaba dike kam harda qwallar ta dan dariya, shikansa dad saida ya dara, dan tabashi dariya.ganin dukkansu dariya sukemata yasata tsame hannunta ta bar wajen.

Tana barin wajen Dije ta miqe tare da d'aukar flet ta zuba abinci aciki tabita.

Dad da mom kwa 'yan kallo suka koma.tana shiga ta taddata a zaune gefen gado, abincin ta turamata batare da tace" komiba"

Kallon abincim kna ta tureshi gefe, dije da dariya nacinta amma ba dama hakan yasa ta sakya gimtse kayarta, kallon auta tai tare da riqo hannunta tace" haba autan mom meyayi zafi kuma, plz kici abincin kinji dan Allah"

Auta ta qara ture abincim kana tace" ni banaci badai dariya kukeminba"

Dije tace" plz ai mundaina kuma kinga bani ko?"

Batasake maganaba ta juya tai kwanciyarta, ganin hakan yasa itama dije d'aukar abincin ta d'ora mata kan bed side, tai ficewarta tare da jamata qofar.

Auta kam jin anja qofa yasata miqewa tsaye, zuwa tai tasawa qofar key ta dawo taja farantin ta hauci. Nikam nace" ashe dai baki zuciyarba"


Bayan sati biyu.

..........Su dije kam ankammala jarrabawa kuma ayu dinne zasu kar'bi result d'in su, sai faman fargaba take dan batason wani mataki tazoba.

Koda aka basu batai gigin bud'ewaba dan jin yadda ake ta yada mata da habaici musamman su zuby itakam yanzu in tabud'e bataciba fa ai kam taji kunya kuma bata son ina zata sa kantaba.

Fiddausee kam har gida ta rakota, wai bata gaji da ganintaba, kuma tace" tasa ran ganinta gobe ko jibi", da wannan batu suka rabu.

Koda tashiga cikin gidan kai tsaye d'akibta ta wuce batare da tace da mom komiba, itama ganin hakan yasa bata cemata komiba.

Koda tashiga bata bi takan littafin result d'in naataba, duk da cikin zuciyarta ba'abinda takeson tagani illa shi.

Sai da tayi wanka ta kintsa sannan ta d'akko tare da bud'ewa da bisimilla.ga mamakinta ta goma tagani ajiki acikin su ashirin da biyar.

Takye bakinta ya bud'e murna da farin ciki suka lullu'beta tarasa ina zatasa kanta dan farin ciki, ita bata ta'ba tunani ko tsammanin hakanba ma.

Da gudu tai qasa tana qwalawa mom da auta kira, auta da qiris daman take jira ta fito a milion mom kwa cikim murmushi tafito daga kitchen d'in.


Dije ta tafi da gudu ta d'ani mom tare da fad'in " mom nayi nasara ban zama daqiqiyaba ban zama shakatafiba ban baku kunyaba."

Mom tace" wai daughter mai a kaine, kin qanqameni balle nasani"

Sakinta tai tare da miqa mata littafin, mom na kar'ba ta bud'a littafin, ganin result d'in nata yasata fad'ad'a murmuahinta kana tace" ah lallai d'iyata anyi qoqari, aikam kina da kyauta ta musamman, musamman ma wajen son ai dole a jinjina miki, masha Allah, Allah yasa kifi haka"

Dije kam ta amsa da "ameen" tare da rufe fuskarta da tafin hannunta alamar kunya.

Auta ma rungumeta tai tare da fad'in " kai aubty na amma kin matuqar burgeni" kowa farin ciki yake da wannan result d'in.

Koda dad ya dawo aka nunamai, shima ba qaramin mutna yai da ganin sakamakon ba, aikam atake yabata kyautar naira dubu goma.wanda daqyar dije ta amsa saida mom tasa baki tare nuna hakan bai musu dad'iba, sannan ta amsa.

Mom kwa bazata tamata dan wata had'ad'd'iyar atamfa da turare ta bata, acewarta somin ta'bune sai ma son ya dawo.

Itakam dije aranta na ayyana hakan fa bazai yiwuba dankwa ita tasan halin kayanta.




.......Wannan hutun da aka musu yasa dije roqar mom akan tanason taje taga Iya.

Batasha wahalar hakanba dan kwa tana nema aka batta, aikam washegari da wuri suka shirya dan itama auta tace" zata bita" sai rimin gado.

Basu wani jimaba suka sauka, wayyo murna wajen jummai ba'a magana, Iya kam baki yaqi rufuwa da ganin jikar tata.

Koda dare dije ta baje hajar dasu dad suka bata ta kawo musu, aikam au dad sunsah albarka, duk da cewar dad yana yawon kawo musu ziyara.

Nanfa aka bawa kowa nasa, ciki kwa harda su inna da baba tsalha.matar kawu kam tsarabar kayan jarirai tasha wanda washe gari suka kai mata.

A hanyarsu kam ta dawowa siada dije tace" suzo suje gidan Ramai"

Ai kam hakan akai, sai gasu a gidan Ramai.sallama sukai yayinda Ramai ke zaune tana kad'i na lagwani.

Ganinsu yasata had'a rai dan tagane muryar kuma ko shakka babu dijen ce tunda ga jummai ta gani.

Dije ta sunkuya tare da cewa" ah baba Ramai kad'i kikeyi?"

Ramai ta cunu baki tace" eh ya akayi kina jin haushi ina yi ko?"

Dije ta zaro idanu waje tace" wa ni na shigesu haba baba Ramai nifa alkhairi ne yakaqo ne ba fad'aba, dan Allah kiyi haquri wancan lokacinma yarintaci tasa namiki haka kinji"

Bata jira amsawarta ba suka miqe nan dije ta ajjiyemata qullin wata leda tare da fadin" sai anjimanki baba Ramai"

Ramai kam ba abinda yafi mata dad'i irin yadda dije ke anbatonta da baba, hakan sai yasa taji duk wata tsanarta ta gogo aranta, batare da tasami damar yimusu magana ba suka fice daga gidan.aranta kam tad'au alwashin zuwa har gida tabata haquri akan sa'banin da suka samu.

Ko lokacin da ta bud'i ledar sai da gabanta ya fad'i ganin irin shatara ta ariziqin da tamata, lallai dije kam anyi hankali.

A gida kam dasuka koma hirarsu kawai suke, inda jummai ke tambayat dije ya Imran d'in ta.

Dije tai murmushi kan tace" nikam wannan yawon tambayar tasa yasa nafar zargin qani abu kodai kina sonsane Jummai? "

Jummai ta had'a rai tare da fad'in " haba dai Allah ya kyauta, nikam narasa wazansu sai d'an birnin wanda nasanbyafi qarfina, kawai naga kuna shiri dashi, kuma kinga koba komi ai yana dadad'i na tambayi wanda ya damu dakai da da naka"

Dije tace" hakane, Allah yasa dai da gaske kike"

Jummai tace" to da dame nake"

Itakam auta dariya tai kan tace" aunty Jummai au ni nacema na daina cemiki jummai juwairiyya ai shine sunanko?"

Bata jira amsartaba ta d'ora da fad'in" ai kam inda hakan zata kasanci zanfi kowa farin ciki domin duk macen da tasamu ya imran to ta gama samun miji na gari, kuma ai shi na miji baya kada'n balle yafi qarfin ki dan haka indai kina yi kawai ki gayamana mu munsan sauran aikin, in bahakaba kyaji wata ta qawace miki shi"

Jummai gabanta sai da ya fad'i amma cikin nuna harumta da dakewa tace" nifa na gayamuku ba simsa nakeba, haba"

Auta da dije suka had'a baki wajen fad'in" ai shikkenan intai tsami da wari maji"

Ita dai Jummai batace komiba sai juyawa tai ta tada kanta da matashi tai kwanciyarta. Sukam basu suka kwanta ba saida suka sha hirarsu.

Jummai kam bawai baccin takeba a'a kaeai tunani take maganar dasukai d'azun, " ina bazai yiwuba, bazan iyaba kuyi haquri 'yan uwana koda ace son ya Imran zai kasheni bazan ta'ba gaya mukuba, ina dai fatan Allah yacikan burina" da wannan tunanin bacci ya sureta.

Koda asuba duk farkawarta da wuri bata tashiba, salla kwa tanayi ta maida kai tacigaba da baccinta, tunda jiyan bata samo tai bacci sosaiba.suma ganin hakan yasa su maida kai suka kwanta.

Basu suka tashiba sai wajen goma da rabi na safe shima din Iya ce tatashesu.

Kwata-kwata yinin yau jinta take qata iri tun maganar dasukai da dije tun jiya takasa sakat da samun nutsuwa.

Dije ce ta zungureta tare da fadin" yadai anya kwa lafiyarki qalau"

Girgiza mata kai tayi tare da fad'in " bakomi, lafiya lau"

'Dagya kafad'a tai alamar shikkenan, nan suka cigaba da sabgoginsu, sai dai duk wanda yasan walwalar Jummai to alokacin yaganta sai yasan da walakin goro amiya.


To kwanan su dije hud'u suka jiyo kasancewar hutun nasu bayada yawa har gwanda autama su sati hud'u aka basu sa'banin dije da akabasu sati uku.koda zasu tafi Jummai jitai kamar ta bisu sai dai bayadda zasuyi, tanaji tana gani suka tafi suka barta ita kad'ai cike da kewar 'yan uwan nata.

A 'bangaren su daf kam shirye-shiryen tar'bar baki suke daga libya, dan su hajiya kakane zasu zo, duk da dad yaso hanaso zuwan acewarsa su zasuje tunda sun jima basu jeba.amma hajiya kaka ta dage akan itafa lallai su zasu zo.hakan yasa ya qyalesu badan yasoba.

Koda su Dije suka dawo nan suka tadda gidan ya hautsine, dan shirye-shirye ake soaai na tar'barsu, nan suma suka shiga aciki gaba dayi dasu.

Mutam libya kam basu suka saukaba sai wajen magrib wai danma jirgi suka hau.

Hajiya kaka kam baki yaqi rufuwa tunda tai ido biyu da Dije amatsayin matar bababn jikanta.

Ai kam taqi barinta taje konan da can, sukam su dad sai dariya sukemata suna tsokanarta. Yayinda auta keta tsokanar hajiya kaka wai anga sabin jini an nanuqemata"

Hajiya kaka kam sai dai tace" yasan ranki, aiki kin tsofa daman"

Auta kam sai ta cunu baki tace" hmm uhmm sai dai ke"

Haka suke tayi dayake ansan halin nasu in sun had'u sai dai agaji abarsu ko kuma in sungaji su dan kansu sai su haqura kodan bakinsu ya huta.

Da dare kam hajiya kaka catai tare da dije zata kwana, sai da dad yace" hajiya kina buqatar hutuba yakamat ki huta zuwa gobe kya kwana da itan"

Nan ma catai bata yadda ba ganin hakan yasa suka qyale mata Dijen, itakam dine bataji ko d'ar ba tunda batun yau tasab kwana da tsofaffiba, tasan duk yadda zata 'bullowa da lalurorinsu.

Ko a d'akin ma basu suaki bacci ba sai wajen sha d'aya na dare, ba abinda suke sai hira.

Itakam auta ta samu 'yar wata kawunsu Ashfa da ita suke hirar, wacca kusan hirar tasuma akan Ashraf ne.

Ashfa taso Ashraf sai dai har yanzu battajin sonsa na raguwa acikin zuciyarta duk kuwa da auren da akace yayi, kuma zata iya zama dashi koda ace itace cikon ta hud'un, sai dai kawai matsalar da take fuskanta yadda baya nuna kulawarsa gareta tunda tace tanasonsa ya d'aukemata wuta, ko yaje musu baya bi takanta sa'banin da da inyaje har fita suknayi zaga gari.

Ko zuwan nan daza'ai ba'aso tahowa da itaba to kafiyarta yasa aka taho da ita, badan komiba sai dan taga masoyin nata, sai kuma gashi taji auta nace mata baya gari, sai nan da wata uku zai dawo, to su da zasuyi sati biyu ai bakanta.

Da safe hajiya kaka da qyar tabar dije ta matsa daga kusa da ita, bawai kuma wabi abin akeba kawai hirace irin ta tsofaffi.

Itakam dije soaai matar ke burgeta, tana da faran-faran, sai dai a yadda ta lura bata d'aukar raini.

Auta ce tashigo d'akin, yayin da dije ke nin kewa hajiya kaka kaya, auta tai murmushi tace" oh su kakus an ga sabon jini anqi barinsa ya huta"

Hajia kaka tai dariya game da fad'in " kin ci gidanku ja'ira, to yasan ranki"

Auta tai dariya har da buga qafa, kan tace" ah ko daya babu, yanzu kuzo muje falo za'a karya, sai abarmana mata ta huta ko"

Hajiya kaka tace" zan kamakine yarinyar kawai"

Auta tace" ai baki da qarfin nan"

Kan auta tai magana dine ta katseta da fad'in " jeki gamunan"

Cikim sauya fuska auta tace" au gwale nima zaki dan ina tare miki" tana gama fad'a tai juyawarta ta fice.

Hajiya kaka kam dariya kawai tayi, yayinda itama dije haka.


........To zuwan su hajiya kaka sai ya dad'a d'ebewa dije kewa musamman ta iyanta dan sosai takejinta kamar iyan nata.hakanan itama hajiya kaka na matuqar san ganin takasance da dijen dan ta lura yarinya ce mai san jama'a dasan kyautatawa, duba da yadda kullum takeaata nishad'i.

Dije tsaye a kitchen tana qoqarin damawa hajiya kaka kunin gyad'a, duk da bawani qwarewa taiba amma battajin zata iya bari adama mata.

Ashfa da shigowarta kitchen din kenan tana neman abin sawa abaki na qwalama, ganin dije tsaye kan gas tana qoqarin yin anfani dashi yasata qarasawa wajen tare da ture dijen gefe.

Dije jin anyi hefe da ita yasata kallon wandabya ture tan, ganin ashfa yasata murmusawa dan azatonta ko bata sanibane.

Ashfa kam sauke tukunyar tai qasa tare da d'ora wata tai sanwarta, azahiri batajin kwad'ayin kayan abinci amma ganin dije yasa tsiro da dafa indomie.

Dije ganin ta sauke mata tukunyar ne yasata cewa" ah lafiya kuwa, hajiya kaka fa zan damawa kunu"

Mutgud'a baki ashfa tai kan tace" nikuma indomie zan dafawa cikina, ko bakki ganewa"

Dije tai tyrus tare da sauke duk ka idanuwanta kan ashfa take tagama karantarta dan dama ta lura tunda zukazo take mata kallon wani haka-haka.

Matsawa tai daf da ita tare da sa hannunta kan na Ashfa ta damqesu waje d'aya.

Ashfa dake qoqarin zuba indomie dan ruwan yatafasa, jin an riqe hannunta yasata kallon dijen.

Itakam dije gefe tai da hannun tare da sauke tukunyar tamaida tata, tacigaba da abinda takeyi.

Ashfa kuwa bawai ta karaya bane amma jin yadda dijen ta riqe mata hannu kamar ba mutunba yasata ja da baya, lallai ashe duk iskancinta akwai wacca ta takata, tana mata kallon yarinya ashe da wayont.

Batare da tabi takanta ba tai waje tare da fashewa da kuka, azuciyarta catake inkinsan wata ai bakisin wataba.

Dukkansu suna zaune hajiya kaka na jiran kunun gyad'a, itakam mom tace 'yar kalloce yadda za'ayi wannan kunu har ashashi.

Kallonta sukai yadda ta taqarqare tana kukan nata bilhaqqi, Mom ce tace" lafiya Ashaf meyafaru kuma kike kuka haka?"

Hajiya kaka da tasan halinta ko kulata bataiba, amma sanjin dalilin kukan nata yasata maida hankali wajemsu.

Ashfa kam dad'a matse hawayen tai kan tace" wai mom naji d'ora indomie cikina yana zafi shine wannan yarinyar tace" ai gas din bana ubana bane dan haka hajiya kaka takewa kunu na bari sai ta kammala"

Mom da jikinta yai la'asar duk da cewa ta tabbata dije bazata ta'ba fad'in hakanba, amma kar kai shaidar d'an yau, hakan yasa tace da auta ta kira mata dijen.

Koda dije tazo durqusawa tai tare da fad'in " gani mom"

Mom ta kalle dije tace" daughter me had'a ku da Ashfa? "

Dije batare da ta 'boyemata komiba ta gayamata duk abinda ya faru tundag kan zuwanta kitchen din har fitowarta"

Mom ta jinjina kai, tabbas tasan ashfa ce bata da gaskiya, amma gudun kada ranta yasakya 'baci, kuma gaban kaka ne sai ta kalleta tace" kiyi haquri ashaf, jike d'ora girkin , ke kuma dije d'ora a d'aya gas d'in kinji"

Ai kam caraf hajiya kaka taceafe da fad'in " a'a banasin wannan rashin gaskiya, ita dan uabnta batason wa akewa kununba, ai daman nasan itace ba gaskiya, kawai na qyaleta kuma ba indomien da zata dafa yarinyar da sam taqi jinta ma halin masifane kawai irin nata, kuma idan baki bar wajen nanba sai na kakkartaki, ke kuma wuce ki qarasa min kununa"

Jin yadda hajiya kaka ke surfa fad'a yasa dukkansu sukai tsit, musamman ashfa da sum-sum ta haura part din su auta, dan tasan sauran zancan.

Mom kwa da auta hajiya kaka suka shiga baiwa haquri, akan abinda ya faru.

Kunu kam ba'a gamashiba saida aka d'au tsawon rabin awa, kida hanne tace zata temaka mata catai a'a battaso, ai zata iya.ahaka aka gama kwamacalar aka kaiwa hajiya kaka.

Hajiya kaka kam sai zuba santi take, catake" bata ta'ba shan kunu mai dad'in irinsaba" nikam nace" ah hajiya kaka fad'i gaskiya dai"

Sudai su mom da auta sai darya sukewa hajiya kaka, aikam wannan kunu sai da kowa yashashi, hatta da dad sai da aka ajjiyewa.ashfa ce kawai bata shaba, hasalima tunda ta haura saman bata sakya sakkowaba.

Koda da dad yasha kunun shima sai da ya yabamata dan ba laifi yayi dad'i sosai, aikam dije sai yaqe haqora take akan tayi abin arziqi.



.........Hajiya kaka ce zaune ita da dije suna ta'ba hirarsu, cikin hirar ne hajiya kaka ke tambayar ta akan abinci kala-kala wad'anda ta iya.

Dije ta dan rausayar dakai kan tace" ni ba abinda na iya sabida ko agida ruwan zafi kawai na iya dafawa, sai yanzu da mom da hanne ke koyamin"

Jin hakan yasa hajiya kaka rufeta da fad'a, akan me zatayi sakye da abinci, batason da shi kad'ai kana iya jawo hankalin mijiba, aikam nan tatasa agaba akan daga yau zasu ahiga kitchen tare tana koya mata kalolin girki irin nasu, dan Ashraf na matuqar son abincinsu.

Ai kam daga ranar hanne ta daina shiga kitchen, sai dai hajiya kaka da Dije suke aiki a kitchen, abinci kam yanzu dije ba wanda bata sarrafawa indai na garinsu hajiya kakane, sai dai wanda bata koyamataba amma indai sunyi takan riqeshi a qwaqwalwarta kuma yazauna kenan, wai bataso tabawa hajiya kaka kunya.

Tun su mom na cin abinci da qauri ko bai gama da huwaba har takai sunacinsa dai-dai.

Editing is not allow......

Vote,
Commet,
Share and like....

*Mrs.Abduul ce*

Weiterlesen

Das wird dir gefallen

4.4M 499K 92
Title - The True Conqueror (အောင်နိုင်သူအရှင်) တောင်ပိုင်ဘုရင်ကြီးလင်းမိုနှင့် မြောက်ပိုင်းအိမ်ရှေ့စံ လီချန်းယုံတို့၏ ကြည်နူးဖွယ် ဒဏ္ဍာရီတစ်ပုဒ်... N...
206K 21.7K 103
ဘာသာပြန်သူ - စွဲညို့အသင်း
1.2M 80.5K 114
Cover- edited from google Start Date -22.4.22 End Date- 22.3.23 အနံ့သင်းတဲ့ သဇင်မင်းကမှ ပန်းထင်သလား မထင်ပါနဲ့ အဲလိုမထင်ပါနဲ့ အနံ့မဖက်တဲ့ သပြေခက်ကလဲ...
568K 66.1K 186
Divine doctor : Daughter of the first wife [ မြန်မာ ဘာသာပြန် ] Author : 杨十六 (Yang Shi Liu) English Translator : Spring Rain Translations Group Discla...