Page Four

255 25 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
             🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
              🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

Khadeejaht Hydar Young-Novelist

The experienced writer of 👇

IHSAN
UQUBAR UWAR MIJINA
WATARANA SAI LABARI
PRINCE AIRAN AND MAIMOON
KANKI KIKA CUTA
DUNIYAR MU A YAU

And Now with the most enjoyable one 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote  akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

Follow and vote on

WATTPAD
@YoungNovelist4

Blog:
https://khadeejahthydaryoungnovelist.blogspot.com/?m=1

INSTAGRAM
Khadeejaht-hydar -youngnovelist

TWEETER
@Young Novelist II

FACEBOOK
Khadeejaht Hydar YoungNovelist

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ban yarda wani ko wata ba ya juya min littafi ba.

Novel is free just need ur support dearies,visit me on wattpad,,@YoungNovelist4 to read more of my stories.ga link ga masu buƙata ku shige kai tsaye.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb

PAGE FOUR

Abee yace"yanzu Sabeer ni zaka kalla ka faɗamin bakason ƴar abokina ka zaɓi wata akanta yanzu me kakeson nafaɗawa mahaifinta,yace"Abee kayi haƙuri amma gaskiya bana sonta daga haka ya tashi yafita,shi Aishar ma bawai wani sonta yakeba amma halayyarta na kirki yana burgesa ko babu komai zai auri mai tarbiyya daga baya zai koyi sonta.

Mufeeda kuwa hakata wuni cike da baƙin ciki mara misaltuwa,wai akan wata Ayshar banza zai mareta ya wulaƙanta ta wlh dole saita gyara masa zama saita salwanta ran wacce yakeso ɗin saitaga ya zaiyi kuma wlh dole sai ya aureta.

Abee fa ya tubure yaƙi maganar Sabeer akan Aisha yanzu ma faɗa yakema Sabeer ɗin yace"tunkafin naɓata maka rai don sam bazan fasa aura maka Mufeeda ba,Sabeer mutum ne mai taurin kai gamida kafiya ga zuciya kamar me,yace"Abee a wannan zamanin aiko mace ba'ama auren dole balantana ni gaskiya am sorry i can't hurt Aisha,Ammee tace"Mai gida daka barshi da zaɓinsa nakeganin hakan shine mafita,cikin zafin rai yace"wlh Sabeer baka isa nasaka kaƙi ba zamuga waya haifi wani daga haka yafice daga gidan,shim Sabeer tashi yayi yaje gun Aysha,bayan sun zauna ne yace"zanbar gidannan yau inzaki bini ki haɗa kayanki a ɗaura mana aure acan,cikin mamaki take kallonsa to mai yafaru ira kanta ya ɗaure tace"meyafaru haka Ya Manga ko wani abunne kafaɗamin kasani a duhu,bai sake mata maganaba yatashi yakoma cikin gidan,yabarta da ɗaukar zancensa shirme.

Hajiya na yanke shawarar  nan da sati biyu zan ɗaurawa Sabeer aure saboda naga alamun yanason ya watsamin ƙasa a ido,"hakan ma yayi Alhaji Allah yasanya alkhairi,dumm gaban Sabeer dayake niyyar shigowa ya buga, kansa ya dafe dayaji lokaci ɗaya ya sara masa,part ɗinsa ya wuce,atm ɗinsa kawai ya ɗauka yabar gidan,bai zarce koinaba sai wani ƙauye dake nesa sosai daga gidansu amma nan cikin adamawa ne,babban  daji dake kusa da wani ƙauye yaje,Sabeer baida tsoro sai isa koda ya isa jejin rumfa ya buga yafara zama shikaɗai cikin ƙunci da ƙunar rai,ƙadan-ƙadan yasamu yara matasa waenda suka zama yaransa haka suka haɗu suka gina gidaje da kara kamar na fulani ,kuma ko wacce ranar kasuwa sukanje suyi siyayyarsu su dawo, a hankali yazamema mutanen ƙauyen kusa dashi garkuwa ,ɓarayi da masu garkuwa basa zuwarmusu,don duk wanda yazo dajin dasuka sama sunansa wato Dajin MANGA to sunanka gawa inhar da niyyar cuta kaje,kuma sunan Manga yasamu asaline daga abokansa,dukda yana taimakonsu amma hakan baya hana ya musu hukunci don shi baya shiga sabgar kowa ɗan inka masa raini kagane kuranka,to a wannan yanayinne ya haɗu da sarauniyar rashin kunya da tsiwa,wato Sabreena.

Wai yanzu Aisha bazaki daina kukannanba kullum abu ɗaya saikin haifar ma kanki wata cutar ne wlh ni nafara gajiya da wannan halin naki,tunda wannan yaro Sabi yake koya kika daina walwala har kowa ya fuskanta to inbai dawo ba kenan mutuwa zakiyi ko kuma bazakiyi aure ba tunda naga alama duk wanda yazo gunki saikin koreshi ke sam bakima kanki faɗa ko haryanzu ke yarinyace kike gani,mu a zamaninmu kamar ki ansamata lalle ankaita ɗaki harda haihuwa,haba Hajiya taya zaki na daɗa mata damuwa akan wacce take ciki kede ki tayata da addu'a saboda ni nasan ciwon irin wannan abun amma insha Allah,Allah zai kawo mafita,zo Aisha ta zoki zauna kifaɗamin abunda zanmaki,tashi tayi taje kusa da Abbunta ta zauna sai kawai tafashe da kuka wiwi tace"Abbu dan Allah kayi addu'a Sabeer ya dawo nasan zaka'iya tunda kai Malamine don Allah,wallahi ko bazai aureniba inna gansa hankalina zai kwanta taƙarasa maganar tana sheshsheƙar kuka,dafa kanta yayi yace"Insha Allah kwananna Sabeer zai dawo zanmaki addu'a kinji amma saikin min alƙawarin bazaki sake kuka ba ,share hawayenta tayi amma wasu na zuwa tace"Abba dan Allah kayi haƙuri karka fasa addu'ar wlh na daina kukan,yace"yauwa ƴar albarka ta maza zo zauna muci abinci.

Kuka take wiwi tace"Dan Allah Manga ka tausayamin wlh na tuba nabi Allah nabika wlh bazan sake yima kowa rashin kunya ba namaka alƙawari,wani wawam tsawa ya bugamata don ako yaushe ya kalleta sai ya tuna sauƙar hannunta akan fuskarsa wanda hakan yakesa koyayi niyyar barinta sai ya fasa,cikin murya mai firgitarwa yace"bakiyi hankali ba tukun da sauranki yau kwata-kwata kwananki huɗu nikuma saikin cika wa'adin shekara ɗayar dana ɗaukar maki tukuna zan barki nasan alokacin kin koyi tarbiyya da girmama na gaba,wani kuka ta rushe dashi tace"dan Allah kamin rai wlh na tuba,zan..bai bari tasake maganaba yabar gun don sam ya tsani kukan mace hakan nasashi rauni da kuma tuno masa da Aisha wacce sanyayyar halinta ke burgeshi,yana bala'in tausaya wa Aisha kodan haƙurinta sam ba irin wannan mara kunyar bace mara tarbiyya,ni yarinyar nan ma banasonta sam batada kyau,Aisha tafita kyau dama komai,tunanin gidane ya faɗo masa amma ya kawar don baison komawa kar a aura masa Fadeela.

"Haba Ummin Sabreena kiyi haƙuri za'a ganta insha Allah,cikin kuka tace"Malam yaufa kwana huɗu kenan da rashin yarinyar nan  bansaniba ko taci abinci ko bataciba ko a wane hali take duk bamu saniba ni ko gawar ta ma agani hakan zaifi mana daɗi,ko kuma Malam dan Allah a duba dajin Manga koza'a dace ko gawarta a kawomin zan dangana da ƙarɓe kyautar da Allah yamin ya ƙarɓa taƙarasa maganar tana kuka sosai,nan idon Malam yaciko donshima kawai dauriya ce amma rashin ƴartasa tilo na ɓaƙanta masa rai da ruhi duk basuda sukuni mutanen ƙauyanma duk sun damu anata addu'a dai,tohm FANS BARI MUGA CIKIN ADDU'AR ƳAN ƘAUYEN SU SABREENA DA TA BABAN AISHA WACCW ZATA FARA AIKI.

Gaskiya mu girmama UWA don bamuda kamarta a duniya,Allah yasakama iyayenmu da aljanna maɗauka kiya ameen🤲🤲

Malam ya nisa yace"hakan zamuyi amma saimu bari tunda mai gari yayi tafiya sai nan da kwana biyar zai dawo kinga saimu gayamasa yabamu tsaro muje kafin nna dai muci gaba da addu'a,tacw"shikenan Malam Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ameen..

Kwance yake a ɗakinsa yana bacci amma ransa ba daɗi tashi yayi ya zauna yana tunanin komawa gida ga wannan fitsararriyar bai gama hora taba ya zaiyi kenan,wata zuciyar ta raya masa cewar kawai ya zauna inya gama horata sai shima yakoma gida da yaransa ya nemar musu aiki don yayi alƙawarin mutu ka rabashi dasu sbd ƴan amana ne,kwanciyar sa yayi yanajin kukanta sbd ɗakin daya ajiyeta kusa da nashine sannan makullin a hannunsa yake dalilin yin hakan shine duk abinda zatayi yanaji sannan dlilin ƙarɓar makullin kuma shine kar  yaransa su buɗeta bayanan su mata wani abun dukda ya yarda dasu sosai to amma akwai shaiɗan mai rayama mutum aikin banza,shikuma so yake yadda tazo takoma a haka amma bada wannan halayyarta taba.

Sabreena ce a zaune a ɗakin tasa abincin da'aka kawo mata bata ciba tana tunanin ina Manga yaje kwata-kwata yau baizo ganintaba amma taji lokacin daya bada umarnin akaimata abinci a kulleta abasa makullin,so take taga fuskarsa ko zataji daɗi amma har dare sai kawai tasa kuka wai ko zaijita yazo yamata tsawar ta daima amma shiru,shikuwa Manga yanajinta yayi banza da'ita don bayason ma yana kulata kar kanta ya daɗa girma..

Ammee,Abee dan Allah ku janye maganar auren Yaya da Fadeela ku barsa ya auri Aisha kunga tanada hali masu kyau Yaya saida irinsu amma in ya auri mai zafi irinsa abun babu kyau ,gidannan babu daɗi im babu Yaya dan Allah ku haƙura ku bar zancen Fadeela kabawa abokinnaka ƙoƙari ,dukda bansan ran dawowar Yaya ba amma dan Allah kubar znacen Fadeela nima sam batamin ba batada kamun kai,Abee yace"shikenan na yarda ya auri Aishan,hugging ɗinsa tayi tace"tnz Abeen mu.

To nima Tnx Fans ɗina.
YoungNovelist nasonku sosai.

Masu wattpad dai aje ayi follow ayi karatu sannan kumin vote iya iyawarku akan novels ɗina .

A karshe kuma sharhinku wato comment yana sani nishaɗi kunaƴi inasonsa sosai tnx.Deeja's care.

Vote
Follow
Share
Comment

SABREENA SABEERKde žijí příběhy. Začni objevovat