Page Five

237 24 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
             🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
              🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

Khadeejaht Hydar Young-Novelist

The experienced writer of 👇

IHSAN
UQUBAR UWAR MIJINA
WATARANA SAI LABARI
PRINCE AIRAN AND MAIMOON
KANKI KIKA CUTA
DUNIYAR MU A YAU

And Now with the most enjoyable one 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote  akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

Follow and vote on

WATTPAD
@YoungNovelist4

Blog:
https://khadeejahthydaryoungnovelist.blogspot.com/?m=1

INSTAGRAM
Khadeejaht-hydar -youngnovelist

TWEETER
@Young Novelist II

FACEBOOK
Khadeejaht Hydar YoungNovelist

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ban yarda wani ko wata ba ya juya min littafi ba.

Novel is free just need ur support dearies,visit me on wattpad,,@YoungNovelist4 to read more of my stories.ga link ga masu buƙata ku shige kai tsaye.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb

Page Five

Zaune yake fuskarsa a tamƙe babu walwala,kallon su Bappa yayi,Bappa shine babba acikin yaransa wanda sunfi shaƙuwa sosai sannan Bappa shine wanda yake iya zama da Sabeer Manga na tsawon lokaci batare dasun ɓataba saboda  Bappa akwai haƙuri duk abinda Sabeer zai masa baya fushi sam,Bappa marayane bashida iyaye Allah kuma ya haɗashi da Sabeer,kallon su yasakeyi yace"Bappa yau zankoma gida gun iyayena nagaji da zaman nan zuciyata tanason ganinsu Abba ga Hanan,kuma tabbas nasan Aysha nanan ta tada hankalinta akaina don haka yau Insha Allah zanbar jejin nan,cikin fargaba Bappa cikin muryarsa ta fulanin usul yace"Manga kana nufin anan zaki barmu ki tafi aradun Allah ina iya shiga duniya inkika tafi,kallon sa Sabeer yayi yace"Bappa duk inda zanje a duniya kuna tare dani yau ma haka tare zamu tafi daku,ni daku mutu ka raba ,cikin farinciki dukansu sukafara hamdala sum yarda subishi koda zama a cikin kogo ne,a hankali yace"Bappa kaida Sani ku maida yarinyar nan har bakin ƙauyensu kusamemu a tashar mota daga haka ya tashi yayi gaba sauran yaran suna biye dashi aka bar Bappa da Sani dazasu kai Sabreena.

Ƙofar ɗakin ya buɗe yace"ki fito Allah ya taimakeki zakibar gidan nan,tashi tayi tafito tana mai kallon gidan taga babu kowa batayi mamaki ba don taji wasu daga maganganun da Sabeer yayi na barin gidan harda zancen Aysha wanda tagane budurwarsace ko kuma tanada wani babban matsayi a zuciyarsa jin yadda muryarsa ke rawa da yanayin daya yi maganarta,gabantane ya faɗi amma maganar Bappa ya katse mata tunani yace"muje karki ɓatamana lokaci daga haka sukayi gaba,binsu tayi jiki a sanyaye tana mai baƙincikin rashin ganin Sabeer.

A bakin ƙauyen nasu suka tsaya Bappa yace"ki ƙarasa gidan naku sai watarana,har sun fara tafiya ta juyo tace"dan Allah kubasa haƙurin abinda namasa tafaɗi zancen muryarta na rawa,"zan faɗamasa daga haka suka juya suka bar ƙauyen zuwa tasha inda Manga yake da sauran yara suna isowa suka kama hanyar cikin garin.

SABREENA SABEERWhere stories live. Discover now