page fifteen

124 10 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
             🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
              🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

~Khadeejaht Hydar~ ~Young-Novelist~

~The experienced~ ~writer of~ 👇

~IHSAN~
~UQUBAR UWAR MIJINA~
~WATARANA SAI LABARI~
~PRINCE AIRAN AND MAIMOON~
~KANKI KIKA CUTA~
~DUNIYAR MU A YAU~

~And Now with the most enjoyable one~ 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

Vote my novels and follow me on wattpad.
https://www.wattpad.com/user/YoungNovelist4
Or @YoungNovelist4

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote  akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

TWEETER
@Young Novelist II

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ga link din  novel din SABREENA SABEER.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb

Facebook page,like pls.
https://www.facebook.com/Khadeejaht-Hydar-Hausa-Novels-YoungNovelist-101121485268631/

Wannan page din nakine kiyi yadda kikaso dashi.

Rabee'ahtuh comment ɗinki nasani nishaɗi a kullum,har rasa wanne comment ne yafi daɗi nake,Allah yabar ƙauna sosai👏🏻.

  ~Page Fifeteen~
    
     Yakalli Lukman yace"mushiga ciki mana,Lukman yace"a'a gaskiya kuzo muje naga ko itace wlh hankalina yakasa kwanciya,a ransa da zuciyarsa yanason zuwa amma miskilancinsa ya hana yanuna hakan saima yi yayi kamar bayason zuwa tursa sasa akayi,haka suka kama hanyar gidan dayaga sunshiga a ƙafa sbd ba nisa,har sun kusa kaiwa wayarsa tafara ringing ganin Abee ne mai ƙiran yasa ya dakata daga tafiyar ya ɗauki ƙiran ya musu alamar dasuje kawai,komawa yayi yazauna saman motar yana hangensu daga inda yake.

         Sallama Lukman yayi mai gadi ya leƙo yace"wakuke nema?yace"eh uhmm Baba dama wata ƙanwata nazo gani yanzu suka shige,mai gadin bai kawo komai ba sbd yasan ana kawo amare gyaran jiki gidan donhaka sai yace"ah to gasu canma basu shige ba bari naƙira makasu,zuwa yayi yaƙirasu,Sabreena tace"Hafsa kinsan wasu a unguwar nan ne,tace"gaskiya a"a,to kodai mai motar ɗazunne,Hafsa tace"muje mugani ko shagon damuka sayi abune,zuwa sukayi,da sallama abakinsu suka fito suka tsaya a gate ɗin,cikin mamaki Lukman yace"ashedai keɗin ce,itama cikin mamaki tace"Ya Lukman kaine ina wuni ta gaidasu suka amsa dukansu sun zuba mata ido suna kallo,Lukman yace"ai nan nake da zama amma yanzu munzo gun abokin mune shine naganki to nayi mamaki tunda nasan dai ba anan kikeba namayi tunanin koba ke bace ashedai ke ɗince,tace"wlh nice munzo gun Addar Hafsa ne amma gobe ma zamu koma gida Insha Allah,yace"amaryarmu kenan mu zamu koma ,rufe 🙈fuskarta tayi da tafin hannunta tace"uhm to shikenan,daga haka suka koma ciki.

   Sabeer kuwa yana wayar yaga fitowarsu,sallama yaima Abee,ya tsura musu ido,gabansa ne yafaɗi sanyi yafara bi ta ƙofar gashinsa yana shigarsa,so yake yaje yaga wacece donhaka ya dira akan motar yanufi gun nasu,amma kafin ya ƙaraso harsun shige,su Lukman ne suka jiyo gareshi yace"kaga harta shige bakazoba,cikin basarwa Sabeer yace"ba matsala ai amma a ransa ba hakan yasoba,koda sukabar gun Fawaz yace"wlh Sabeer daka ganta kaga Aysha ikon Allah kenan,Shareef yace"ni babu abinda yasake ban mamaki sai yadda take magana wlh kamar Aysha itadai da alama tafi Aysha wayo da magana,Hafeez yace"ni ikon Allah ko babu abinda yaban mamaki kamar zoben danagani a hannunta wlh kamar nasan meshi amma nakasa tunawa,Lukman yace"nima naga zoben nan tun randa naraka Ahmad gunta amma wlh namanta maishi kuma kamar nasan me zoben,Sabeer de bai sake magana ba har suka ƙarasa cikin gidan.

   👧suna shiga ta zube kan kujera tana lumshe ido da kame jikinta,Hafsa tace"wai miye hakane naga muna magana dasu jikinki na rawar sanyi kuma kin shigo kin kwanta ko zazzaɓi kikeji ne?,"wlh Hafsa kawai munacikin magana ne naji wani irin sanyi na shigata gabana na faɗuwa,Hafsa tace"to Allah ya sawwaƙe yanzu goben zamu tafine ko yau da daddare?eh to mu tafi gobe da safen kawai tunda lahadi ce ba hayaniya.

       👦Suna shiga gida suka tadda Bappa a tsaye suna magana dasu Aysha amma hankalinsa naga Hanan,Sabeer ne ya lura da hakan kallon Lukman yayi yaga shi hankalinsa baikai can ba don haka sai shima ya basar ya miƙama Bappan hannu yace"ya akayi ƙannan naka suka dawo gida ko har antashi daga islamiyyar ne,Bappa yace"toh nima dai abinda nake tambaya kenan yanzu suka fira kuma naga sun dawo,Sabeer yakalli Hanan yace"amma ai naga har kun wuce meyafaru haka,Hanan tace"Aysha ce naga jikinta na rawa wai kanta namata ciwo shine muka dawo,kallon Ayshan yayi ya matso kusa da'ita yace"meke damunki ko muje asibiti ne amaki allura yafaɗa yana gimtse dariyarsa ganin yadda yana ƙiran allura idanuwanta suka kawo ruwa,baki ta tsuke tace"ni zansamu sauƙi innayi bacci basai munje asibiti b,murmushi kawai yayi yace"to gimbiyata muje narakaki kishig ki huta..

Washegari da sassafe   suka koma ƙauye wanda a lissafi saura kwana huɗu aure ,inda harsu Sabeer zasuje saboda yima Lukman kara,koina a ƙauye ana jiran auren Sabreena tauraruwar ƙauyen su,Inna kam babu wanda yakaita murna zata aurar da ƴarta tilo ga Ahmad yaro mai tarbiyya da nagarta,Sabreena kam an dangana tabarwa Allah lamuranta,Uhmm hakane duk wanda yamaida lamuransa ga Allah bai taɓewa.

   BAYAN KWANA UKU.

   Yau takama ɗaurin auren Sabreena da Ahmad sai Hafsa da nata angon,sunyi kyau cikin fararen shadda mai tsaɗa amma sam Sabreena taƙi amata kwalliya ba yadda Hafsa batayi ba a ƙarshedai ta kyaleta amma dukda haka tayi ainun don sai wani ƙamshi da sheƙi fatar ta keyi,bayan sallar jumma'ah dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren Sabreena Abdul'azeez Bappa da Ahmad Hassan akan sadaki dubu ɗari,haka Hafsat da angonta,taron aurene wanda yatara jama'a kamar hawan sallah don anyi mamakin mutanen gun Angwaye sai faman murna suke suna karɓar saƙon taya murna daga jama'a,,wata daga cikin ƙawayensu ce tashigo ɗakin dasuke zaune tasa guɗa tace"Allah ubangiji yayi an ɗaura amare Allah bada zaman lfya,wata wawiyar zabura Sabreena tayi zata miƙe Hafsa tariƙeta,komawa tayi ta zauna ta haɗa kai da gwuiwa tana kuka sosai tasan yau za'a ɗaura mata aure da wani ba Sabeer ba amma taji wani sabon ɗaci a ranta,zoben hannunta ta kalla sai kawai gani sukayi ta sulale ba numfashi ajikinta ta suma😢😭🥺😩😫.
    
      Wata mummunar faɗuwar gaba yaji ta ziyarceshi lokaci ɗaya yaji jiri na ɗibarsa idanuwansa na rufewa,sunan Allah yafara ambato ya nemi gu ya zauna ya dafe kansa ,ya rasa meke dunsa tun da safe yakeji kamar wani sashi na zuciyarsa na neman agaji kamar ya rasa wani abu,jiyayi dama yasani dayabi su Lukman ɗaurin auren tunda su duka sunje shima yayi niyya Abbee ne yaƙirasa akan yakai Ammee check up tunjiya jikinta ya motsa,dayasani daya bi bayansu tunda yasan gun,haka yasha magani ya kwanta nan da nan bacci ya ɗaukesa,hannunsa saitin zuciyarsa.

Sabreena!Sabreena!Nafeesa bani ruwa ta suma,da sauri ta kawo ruwan Hafsa ta yayayfamata aikuwa saita ja dogon numfashi sai tari ya biyo baya amai taji yazo mata tana wani tarin aikuwa saigashi yazo,cikin zare idanuwa😳Hafsa takalleta tace"Sabreena jinifa kike zubdawa,cikin sauri takai dubanta kan abinda tazubar,cikin tsoro,mamaki da fashewa da kuka tace"Hafsa jini daga bakina Hafsa nasmau matsala na kusa mutuwa,cikin tausayinta Hafsa tace"noo kibar cewa haka Insha Allah zakisamu lfya,amma dole saikin cire Sabeer a ranki don nasan shike damunki.
 

  Tohm Fans kuma fa dole kucire ganda kuna comment.

Kuna manage da typing kaɗan ayyuka sunmin yawa,ngd.

Vote#
Comment#
Share#

Kuyimin sharedan Allah.

Ƴan wattpad vote fa sun jaa baya gskiya ku dage ko indaina muku post.

Autar✍️💃
Billyn Hamma.

SABREENA SABEERWhere stories live. Discover now