page thirty three

452 27 15
                                    


SABREENA SABEER
Story and written by
~Khadeejaht Hydar~ ~Young-Novelist~
~The experienced~ ~writer of~
~IHSAN~
~UQUBAR UWAR MIJINA~
~WATARANA SAI LABARI~
~PRINCE AIRAN AND MAIMOON~
~KANKI KIKA CUTA~
~DUNIYAR MU A YAU~
~And Now with the most enjoyable one~
SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).
Vote my novels and follow me on wattpad.
https://www.wattpad.com/user/YoungNovelist4
Or @YoungNovelist4
Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.
Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.
TWEETER
@Young Novelist II
BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar
GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com
Ga link din novel din SABREENA SABEER.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb
Facebook page,like pls.
https://www.facebook.com/Khadeejaht-Hydar-Hausa-Novels-YoungNovelist-101121485268631/

PAGE THIRTY THREE

@YOUNGNOVELIST4
Dont forget follow and vote plss
Masu voting sauran novels ɗina a wattpad ina godiya Allah yabar ƙauna .
Da sauri Laɗeefa ta ƙaraso gun Fadeela ta ce ; "me ya faru kike ashar da daddare haka ne yau fa kika dawo amma zaki fara bawa kanki aiki?,cikin masifa ta miƙawa Laɗeefa wayar ba tare da tayi magana ba, ƙarɓa tayi ta fara kallo idanuwanta ta zaro ta ce; "subhanallahi tabɗijam me nake gani kamar ana dinner ɗin Sabeer? Yaushe aka yi hakan bamu sani ba?, Ba ance sai next week bane? Zama Fadeela tayi ta ce "kidaina tambayata ai kina garin na barki amma baki min amfani ba tunda har angama komai kin ɓata mana shiri,Laɗeefa tace"wlh wlh ko labarin banji ba sai yanzu daga haka ta fara duba hotunan bikin na dinner Sabeer da Aysha ne sunyi kyau sosai,tace"karɓi wayarki ai ƙanwar sace tasaka,ƙarɓa Fadeela tayi tana mai sake kallon hotunan zuciyarta na tafarfasa kamar ta zauce,"lalle an taɓo bala'i tafurta a fili,Laɗeefa ƙiramana sarkin yanka don wlh bazan ƙyale taba,"Fadeela kina ganin ba matsala yin aikin yanzun?,"ba yanzu zamuyi aikinba sai nan gaba damar mu ta yanzu ta kwacemana.
Gidan amarya
Misalin ƙarfe uku na dare Aysha tafarka,kallon gefenta babu kowa yasa ta tashi zaune cikin ƙarfin hali ganin Sabeer akan sallaya yasa ta saƙƙo ƙasa ta daura kanta saman cinyarsa tana nishi sama-sama,addu'arsa ya taƙaita cikin kula ya taɓa jikinta,jin yadda jikin yayi zafi sosai yasa ya ɗaurata kan gado cikin marairaicewa yace"Matar Sabeer meke damunki haka?,cikin kallonsa tace"zazzaɓine yake damuna tun ɗazun,yace"bari in ɗakko maki magani kisha,zakisha tea in haɗamaki?kai ta girgiza,yace"haba kinga bazai iyu kisha magani ba abinciba ki daure ko kaɗanne,batayi magana ba,shayin ya haɗa dayake akwai komai a ɗakinta,kaɗan tasha yabata maganin tasha,a hankali tace"kaima kasha ko paracetamol ne naga jikinka kaima da zafi,murmushi yayi yace"karki damu zan warke kema kinsan gari na wayewa an wuce gun,lallaɓata yayi tayi bacci tukun shima ya kwanta yana mai nemar mata sauƙin wahalar cikin agun Allah,don yana bala'in tausayamata ga kuma alamun cikinta mai laulayine.
Yau juma'a kuma yayi dai-dai da fitar Sabreena daga takaba,ƴan uwanta da abokan arziki sunzo gidan don tayata murna,harda hajiyar Ahmad,wacce ita tasa aka dafa abinci harda abun soyawa don sadaka,sannan takawoma Sabreena kyauta ciki kuwa harda makullin mota da kujerar makka da sabbin kaya fil tace duk kayanta tabadasu ,amma Sabreena tace banda wanda Ahmad yabata na aure.
Kallonta Hafsa tayi tace"Sabreena kinganki kuwa wlh kamar asaceki a gudu kinyi kyau sosai,Sabreena cikin murmushi tace"kinsan zaman gu ɗaya baka zuwa ko'ina ba aiki mai yawa sai isa,takalli Hafsa dakyau tace"Hafsa jiya danahau tweeter naga ansaka hoton wata amarya wlh kamar ni,kamar tamu harta ɓaci da'ita saidai nafita haske ita kuma taɗan fini jiki ni abun yaban mamaki sosai donma data ta taƙare da sai nagama kallon hotunan kuma abun haushinma bansan wacece tasaka hotunan ba,amma akwai hoton danayi saving guda ɗaya tafaɗa tana mai ɗaukar wayarta,miƙawa Hafsa tayi tace"kinganta,k
allon hoton Hafsa tayi na tsawon minti ɗaya tace"gaskiya kamar tayi yawa,amma zakicemin baki gane taba Sabreena?,cikin kallon Hafsa tace"gaskiya bangane taba,Hafsa tace"zaki tuna lokacin da mukaje cikin yola gyaran jiki lokacin aurenmu har wasu suka watsamana ruwan datti abakin gate ɗinsu wanda daga bayama har Lukman yazo ganinki,kaɗa kai tayi tace"tabbas hakane na tunata wacce ta tsaya kallona itada wata yarinya ko?"tabbas kin tuna to ai itace wannan saboda dai makeup ne baki gane taba kuma taƙara kyau,Sabreena tace"hakane kam ko alokkacinma naga kamar mu da'ita kenan aure tayi,Allah ya tabbatar da alkhairi,ameen Hafsa ta amsa.
Cikin gidansu Sabreena kuwa saida suka gama murnar kyautar da Hajiyar Ahmad tama Sabreena tukun aka ƙirata don ita kyautar kaya kawai tasan da zancen,lokacin da'aka sanar mata da tafiya hajj aka kuma danƙa mata makullin mota ,rungume Hajiyar Ahmad tayi tasaki kuka,don ta tuna wannan alƙawarin Ahmad hajiya tacika,donshi yamata alƙawarin inhar ta haihu sabuwar mota zai sayamata kuma yakaita aikin hajji,Hajiya ce ke rarrashinta da mutanen gun tukun tayi shiru,haka taro ya tashi kowa na tayata murna,Hajiyar Ahmad ma ta tafi da alƙawarin da Sabreena tamata nacewar zatazo mata kwana 2.
A daren ranar Hafsa ta haihu inda aka samu ɗiya mace,farinciki gun Sabreena kamar ita tahaihu,a ranar aka sallamesu don babu wata matsala,Sabreena ƙin komawa gida tayi ta kwana da babyn ita da Hafsa suka sata a tsakiya,dayake babyn bamai kuka bace yasa sukayi bacci a kwnaciyar hankali.
Washegari mijin Hafsa mai suna Mus'ab yazo sai murnar ganin baby yake,kamar ya maida Hafsa ciki,ganin hakan ya tunama Sabreena da Ahmad don tasan da'ita ce yau ta haihu hakan Allah kaɗai yasan murnar da Ahmad da hajiyarsa zasuyi,kauda tunanin tayi,Mus'ab yakalleta yace"Mamar Baby ya kuke don kece mamarta ba Hafsa ba,cikin murmushi tace"hh aikam dama nice mamarta haka dai sukayita barkwancinsu.
Ran suna babu tsammani don dama sunyi niyyar mata bazata ne,suna cikin ɗaki suna fira da ƙawayensu dasukazo suna mai jego da Sabreena sunsaka kaya iri ɗaya sunata hayaniya da dariya kawai sukaji ana sanarce sunan yarinya Sabreena,tsit ɗakin yayi saikuma sukasa kabbara,da gudu Sabreena tafito taje ta rungumi Inna tace"Ummi kinji sunan yarinyar Sabreena,Inna Hafsa tamin takwara tafaɗa cikeda murna,Innama cikin murna tace"naji Sabreena Allah yabarku tare ya raya mana takwarar auta ta,kowa dariya yayi yana yaba halacci da kara irinta Hafsa,ɗakin takoma ta rungume Hafsa saikuma hawaye ya sauƙarmata,tace"ngd sosai Hafsa rabbi yabarni dake ngd sosai da karamcinki,rungumeta Hafsa tayi tace"bakomai Sabreena kuma Insha Allahu Little ƴar kice ko bayan raina,murna duk yacika Sabreena,yarinyar ta ɗauka cikeda sonta tace"masha Allah little na Allah maki albarka," yasa kibiyo mai sunanki gun ilimi cewar wata class mate ɗinsu,ɗaya kuma tace"banda neman tsokana da shirme duka suka sheƙe da dariya,Sabreena ta kwaɓe fuska tace"Mama Hafsa kingansu ko,aikuwa suka sake sa dariya wai Mama Hafsa,murmushi Hafsa tayi tace"kinga kyalesu kudaina taɓamin bestie na.
Bayan suna da kwana biyu Sabreena da Hafsa na zaune ga tulin kayan sunan da aka samu agabansu Hafsa ta kwanta akan gado tace"Mamar Little ki raba kayan nan kibawa su Inna kiɗau naki keda ƴarki,Sabreena baki buɗe tace"ya zaki kwanta kinga Malama gwara ki tashi donni kayan little kawai zan ɗauka da nawa daga haka tafara ɗebe kayan jaririyar tana jerawa a ƙaramin box,saida tagama kap taɗau atamfa biyu ta ɗau Little ta goya tasaka hijab ɗinta tace"kinga tafiyata,ganin dagaske fita zatayi yasa Hafsa tace"haba Mamar little duk kayan nan ya zanyi dasu dan Allah ki taimaka,komawa tayi ta zauna tana hararar Hafsa,shirya kayan sukayi tsaf bayan sun ajiye na Mama da Inna,turamen atamfa uku Hafsa taƙarawa Sabreena tace"aikece da ƴar baniba ki ɗauka,Sabreena tace"aikam baki isaba ni biyun nan sun isheni,musu suka shigayi har saida Mama tashigo tasamesu,bayanin meke faruwa Hafsa tamata Mama tace"Sabreeena ki ɗau kayan ai kece babba ki ɗauka kuje ku ɗinka da ƴarki,badon tasoba ta ɗauka tama Mama godiya tukun tafice da Little abayanta,dama haka sukeyi inkaga little agun mamarta to abinci za'a bata tana ƙoshi zata ɗauketa,basa rabuwa sai bacci.
Bayan Hafsa tagama arba'in zata koma jigawa da Little Sabreena duk tabi ta damu kanta,har kuka takanyi a ɗakinta,wannan abun yasa Hafsa da Mus'ab jin tausayinta.
Ana washegari zata koma duka iyayennasu na zaune cikin gidansu Hafsa suna haɗa mata tarkacenta batare data kalli kowaba tace"Mama dan Allah ina zansamu maganin dazai kawo ruwan nono?da mamaki Innar Sabreena tace"ke kuma Hafsa mezai saki neman maganin ruwan nono bayan masha Allah kina dashi,Mama tace"ah to kyaleta da shirmenta aini haryanzu Hafsa da sauranta,bata kallesuba tace"so nake Sabreena tasha zamu barmata Little ne,a tare suka ɗago suna kallonta,kallo na irin kinada hankali kuwa,Inna ce tace"Hafsa lafiyarki ƙalau kuwa Sabreena zakibarwa jaririyar dako wata uku batayiba eh lalle fa hankali bai ishekiba,Mama tayi murmushi tace"keda wa kuka yanke wannan shawarar?cikin murmushi Hafsa tace"Yaya Mus'ab ne yace damubarmata Little tana ɗebe mata kewa amma batakai yayeba,Inna tace"shine kekuma kike neman maganin ruwan nono kibarwa Sabreen ko?anya yarannan kunada hankakali kuwa?Mamar Hafsa tace"tunda keda mijinki kukayi zancen nan yazauna inada maganin acikin ɗaki kije ki ɗakko Allah ya rayata ai Sabreenama uwarta ce,Sabreena wacce tunda suka fara maganar tayi shiru tana kallon Hafsa da jaririyar dake hannunta,a hankali hawaye suka saƙƙo mata sai kuma murmushi tace"Hafsa dama zaki iyamin halacci bayan na takwara dakikamin,Hafsa dama kinasona fiyeda tunanina,ubangiji Allah yabaki abinda kikeso,tunfarko dakikace Sabreena ƴatace ban taɓa kawowa zaki barmin itaba tun tana yarintar ta,ngd sosai,maganin Hafsa takawo inna tajiƙa tabata tasha,Innar Sabreena kam sai godiya take musu don ko b komai sunsa ƴarta farinciki kyautar ɗan fari ba abune mai sauƙi ba kuma itace kaɗai agunsu,suna haka saiga Mus'ab ,har ƙasa yagaidasu Inna yakalli Sabreena daketa faman gyara yarinyar hannunta yace"Mamar little sannu,tace"Yaya Mus'ab ngd sosai da karamci Insha Allahu zan riƙe amana gam,da murmushi yace"ni nasan da hakan sbd ko Hafsa iya kular dazata mata kenan balantana nasan saima kinfi Hafsa kula da'ita,yace"Mama inba damuwa zamu tafi yau tunda Allah yasa abokina zai tafi jigawa zamu bisa sai watarana,Inna tace"tafiyar harta tashi muda mukace sai jibi,yace"eh wlh Mama gun aikine suke nemana innatafi bazan samu dawowa jibi ba,ƙarasa haɗamata kayan sukayi,har bakin titi Sabreena tarakasu Little goye a bayanta,Hafsa tace"intanamaki kuka ki zaneta,duka Sabreena takaimata tace"ke kizo kizaneta kiga yadda zan zaneki gaban Yaya Mus'ab daga haka ta juya tafara tafiya farinciki fal ranta,ko jin ƙiran da Hafsa takemata barayiba,Mus'ab yace"kinga ki kyaleta hankalinta yayi gida,kamar a mafarki wanda ke zaune gaban motar dasu Ahmad ke ciki yaji muryarta bai ɗagoba sai lokacin dayaji Mus'ab nacewa a kyaleta yaso yaganta don tun lokacin dasuka ƙaraso yaji sanyi nashigarsa to kowanne ƙofar gashin dake jikinsa,dumm ƙirjinsa ya buga tabbas wannan muryar yanajinta a mafarki,a hankali ya furzar da iskar bakinsa ya shafa kansa da sajensa yace"why all this,Mus'ab ne ya katse masa hanzari da cewar Sabeer yane lafiya kuwa?cikin sanyi yace"lfya,Mus'ab wacece wacce tabar nan yanzun?,cikin mamaki Mus'ab cikin murmushi yace"ƙawar mata tace mai irin sunanka Sabreena wani abunne?,ki kayi kamune?"a'a daga haka ya tada motar,Hafsa najinsu amma bataga mai fuskarba amma kamar taso gane mai muryar.
Vote
Comment
Share
Autar
YoungNovelist
Billyn Hamma
Billyn Hamma (@YoungNovelist4)

SABREENA SABEERWhere stories live. Discover now