page twenty one

132 11 3
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
             🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
              🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

~Khadeejaht Hydar~ ~Young-Novelist~

~The experienced~ ~writer of~ 👇

~IHSAN~
~UQUBAR UWAR MIJINA~
~WATARANA SAI LABARI~
~PRINCE AIRAN AND MAIMOON~
~KANKI KIKA CUTA~
~DUNIYAR MU A YAU~

~And Now with the most enjoyable one~ 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

Vote my novels and follow me on wattpad.
https://www.wattpad.com/user/YoungNovelist4
Or @YoungNovelist4

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote  akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

TWEETER
@Young Novelist II

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ga link din  novel din SABREENA SABEER.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb

Facebook page,like pls.
https://www.facebook.com/Khadeejaht-Hydar-Hausa-Novels-YoungNovelist-101121485268631/

Page Twenty One.

Allah sarki jiya mun cire wani gurbi na littafin nan HAFEEZ💔.

   Koda 👨‍⚕️likitan yashigo ya duba Hafeez kallonsu yayi cikin tausayawa yace"Sabeer saidai kuyi haƙuri Hafeez yarigamu gidan gaskiya,cak tunaninsa ya tsaya babu abinda yake tunawa kawai kallon gawar Hafeez yake baya motsi,cikin tashin hankali da ruɗani Shareef yashiga girgiza kai jikinsa na rawa basu ankaraba suka ji ya faɗi sumamme hakama Fawaz ,Lukman yayi saurin zuwa gun Sabeer yace"Sabeer,Sabeer amma ba magana sai kallonsu yake idanuwansa yayi jazir kamar wuta ga jijiyoyin kansa dayayi ruɗu ruɗu,so yake yayu kuka ko zai samu sassaucin abin da yakeji,wani ƙarfi yaji yazo masa yayi saurin zuwa bakin gadon yakama hannun Hafeez cikin cushewar murya yace"Hafeez munma junanmu alƙawarin zamu rayu tare har abada,ko shekaranjiya saida muka sake jaddada hakan,kullum kana kusa dani katashi kar narasa raina nima dan Allah katashi,yaƙarasa zancen da buɗe fuskar Hafeez, Mama da Kausar kuwa sai kuka suke,Kausar tace"Yaya ɗazufa kacemin yau zaku dawo ,ɗazufa kayi magana da Mama kace mata inkun dawo zaka ƙarasa gidanka mukoma,Yaya kamin alƙawarin kai zaka aurar dani dan Allah katashi,kaga Mama tana kuka Allah ne gatanmu kaine gatanmu,jin kalamanta yasa Sabeer wasu zafafan hawaye suka shiga zubo masa Lukman kuwa yakasa tsaida kukansa,da kyer ya watsamat su Fawaz ruwa ,suna tashi suka nufi gadon suna hawaye,nima kaina YOUNGNOVELIST😭saida nayi hawayen tausayawa waennan abokan.

  Ƙanin mahaifin Fawaz ne yazo don su ɗau gawarsa akaisa makwancinsa na gaskiya,a dai dai kuma lokacin su Aysha suka iso,da gudu suk ƙaraso ɗakin suna haki,ganin yadda fuskokinsu yake jazir yasa Hanan baki na rawa tce"Ya Hafeez saikuma tayi saurin zuwa gadon ganin dagaske ya rasu ta fashe da kuka,don duk cikin abokan Sabeer yafi shiga ran mutane sbd akwai shi da barkwanci,babu abinda take tunawa sai maganarsu ta ƙatshe da yake cewa"AMARYAR MU KUKE KIKE KARKU DAMU MIJINKI NATARE DA JARUMIN MAZA ZAMU DAWO LFYA HARDAKE HANAN KI KWANTAR DA HANKALINKI,ashe dai ba rabon dawowar.

AYSHA MA MAGANARSU TA ƘARSHE TA TUNA,DA KUMA randa yazo gidan tana zaune,yakalleta cikin tsokana da barƙwancinsa yace"MADAM WAI DUK TUNANIN MIJIN NAKINE AI INGAYAMAKI NI JARUMINE ZAN NAKULA DASHI..

Sabeer kuma randa zasufita jejin ya tuna lokacin da Hafeez yace"WLH TUNJIƳA NAKEJIN FAƊUWAR GABA ƳANZU KUMA TAFI YAWA..

Lukman ma ƴa tuna randa zasu tafi suna mota Hafeez yace"AI SAINA RIGA DUKANKU AURE KAR NA MUTU MAMA BATAGA JIKOKINTABA BA MUNA DAWOWA ZANNEMI MATA,ashe ba rabon dawowar.

Shareef ma sai ya tuna randa yaje ya tadda Hafeez a gida yace"SHAREEF INA TAUSAYIN MAMA DA KAUSAR WLH NAFISON KO MUTUWACE ZATAZO TO RA ƊAUKENI SU RAYU TARE KAGA KAUSAR ƳA MACECE GA YANAYIN AIKINA GWARA MANA CE ZATA KULA DA'ITA SOSAI KO MAMA TA TSUFA KAGA KAUSAR ZATA KULA DA'ITA,YANZUMA NAFISON MU GAMA GININMU INNAYI AURE NAMAIDA MAMA KUSA DANI.ba rabon hakan😭😭.

Kowa sai kuka yake don rasuwar Hafeez ba kaɗan ta girgiza suba,musamman Sabeer da yake ganin dayasani sun tafi tare baice ƴa jirasaba,ajiƴan dazai rasu saida ya ƙira Mama kafin akai musu hari yace"Mama kinga naji ciwo a hannu kuma inason naganki da kausar bari inmaki vidio call,to suna cikin yin magana da Kausar yaji ƙarar harbi ya katse ƙiran,basu ƙara ji ko ganinsaba sai yanzu da rai yakusa fita.

Haka aka ɗauki Hafeez don zuwa amasa salla,kowa na kuka da faɗan halayansa masu kyau,dakyer sukaja Sabeer aka kaisa gida aka masa wanka aka fito dashi aka ajiye don kowa yamasa sallama,Mama ce tafara zuwa tace"Hafeez nayafemaka duniya da lahira Allah ubangiji ya sa aljanna ce makomarka yadda ka farantamin rabbi yamaka rahama taƙarasa tana hawaye don Hafeez ɗana ɗaya tamkar dubu,koda aka ƙira Kausar rungumesa tayi tana kuka babu abinda take cewa sai "Yaya kamin komai da uba kema ƴarsa ka kula dano tun ina tsummar jarirantaka kasani makaranta ka ciyardamu da Halal ubangiji yamaka rahama ya gafarta maka tafaɗa tana kuka sosai duk tafita hayyacinta don komai shike mata hatta sayan pad shi yake mata komai ma,daga ƙarshe akace Sabeer yazo yayi masa addu'a amatsayinsa  na amininsa,Sabeer duk jarumtarsa yakasa riƙe kukansa,cikin muryar kuka yafara masa addu'ar irin wacce akema mamaci
اللهم اغفر له ورحمه وعا فيهم وعف عنه................
Har zuwa ƙarshenta masuson addu'ar zasu iya tuntuɓata tana da ɗan tsayi ne👏🏻😭😭,Allah yajiƙanka Hafeez ameen,haka suka kaishi makwan cinsa suna hawaye,tunda suka dawo Sabeer bai sake magana ba ko anzo gaisuwa saidai su Shareef su amsa amma shi yana zaune ba uhm ba uhm uhm.

Sabreena kam tana zaune taji news ɗin abundake faruwa kuma kusa da ƙauyen sune da sauri tasa Ahamd yaƙiramata Inna,jin bai shafesuba yasa hankalinta ya ɗan kwanta,Ahmad kuwa ƙiran gaggawa aka masa akan yazo Yola da sauri,don haka yake shirin tafiya inda Sabreena tasamasa rigima akan cewar tunda Yola zaije yaje da'ita,yace"bazai iyuba gun aikine ake ƙirana wani jami'inmu ya rasu kema ai kinsanshi ko?tace"a'a yace"abokin Lukman ne ko har yanzu baki kalli hotunan bikinmu ba ai duk sunzo sai wani abokinsu ne kawai baizoba wanda yanzu haka shima yana asibiti, mutuwar ta girgiza shi sosai,jinjina kai tayi tace"Allah ya gafarta masa ka kawomin hoton nagani naji inason nagansa,yace"shikenan innaje gidan Mama zan karɓo ko kuma gun Lukman.

Koda Ahamd ya ƙarasa Yola dare yayi bai samu damar ganin Sabeer ba,sunyi waya da Sabreena bayan ya isa tanata masa shagwaɓa,shi kuma sai biyemata yakeyi.

   Jikin Sabeer yayi tsanani don haka likitoci suka yanke shawarar afita dashi ƙasar Makka sati mai zuwa don akwai likita mai kula da zuciya na musamman dasuka sani,agun aiki kuma aka shaidama Ahmad zai dawo Yola da aiki kafin Sabeer yasamu lfya,baiso hakanma kodan saboda Mama da Sabreena amma babu yadda ya iya,haka ya amsa ma D.P.O Falalu da sauran manyan dake gun.

  A satin Mama tace"yazo ya ɗauki Sabreena su zauna don babu daɗi babu shi,inyaso ita sana zuwa ganinta,ya kaita gida taga su Inna,hakan ce rafaru a satin ya dira a Jigawa gidan Mama lokacin Mama taje makwafta ita kaɗaice a gidan,da sallama ya shigo parlourn,da saurinta tafito don taji muryarsa daga ɗakin datake,hannuwansa ya buɗe mata da sauri taje ta rungumesa tana dariya shima rungumeta yayi dakyau tace"sannu da zuwa Habeebi ya hanya,cikin jindaɗi yace"wow Habeebi inason sunannan ɗan sake faɗa,cikin cusa kanta a ƙirjinsa tace"Habeebii"har gajiyar dana kwaso ta tafi,daga haka ya ɗauketa sai kan kujera,ajiyeta yayi yace"i missed u,kafin tayi magana Mama tayi sallama,gyara zamansa yayi itakuma Sabreena ta zauna tana ma Mama sannu da zuwa

"Sannu Ahmad yanzu ka dawo?yace"eh mama,munsameku lfya?lfya lau,je kayi wanka saikau wuce gidan tunda kace gobe zaku wuce,wanka yayi daga haka suka wuce gidansu don ɗakko kayansu don a gobe zasu wuce ,koda suka isa gidan yaɗanyi ƙura,gyarawa tashigayi yace"muje mu gyara inda zamu kwana kawai mu kwanta da wuri kinga gobe da sassafe saimu haɗa kayan mu wuce,ɗakin suka wuce suka gyara,wanka tayi tasa kayan baccinta tahaye gado tace"Hubby saida safe ,murmushi yamata shima ya haye gadon,jikinta ya shige kamar zai manne mata da fata,a hankali yace"i missed u,murmushi tayi tace"me too,daga haka yafara kissing ɗinta tare da bata hottest romance ever,cikin shagwaɓa da tsoron daya fara shigarta tafara turasa tace"Ya Ahmad ka daina zanma kukaahh,shiru yayi yana sauƙe ajiyar zuciya,daga haka sukayi bacci.

Washegari suka wuce Yola,tun a hanya Lukman yaƙirasa yace"su zarto Airport za'a wuce da Sabeer,donhaka saiya karkata motarsa zuwa airport,wani sanyi ne yafara shigarta,ƙirjinta na bugawa,sun shigo airport ɗin dai dai motar ambulance ta shigo itama.

Comment
Vote
Share

Autar🖊️💃💃
Billyn Hamma

SABREENA SABEERDove le storie prendono vita. Scoprilo ora