page fourteen

125 10 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
             🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
              🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

~Khadeejaht Hydar~ ~Young-Novelist~

~The experienced~ ~writer of~ 👇

~IHSAN~
~UQUBAR UWAR MIJINA~
~WATARANA SAI LABARI~
~PRINCE AIRAN AND MAIMOON~
~KANKI KIKA CUTA~
~DUNIYAR MU A YAU~

~And Now with the most enjoyable one~ 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

Vote my novels and follow me on wattpad.
https://www.wattpad.com/user/YoungNovelist4
Or @YoungNovelist4

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote  akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

TWEETER
@Young Novelist II

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ga link din  novel din SABREENA SABEER.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb

Facebook page,like pls.
https://www.facebook.com/Khadeejaht-Hydar-Hausa-Novels-YoungNovelist-101121485268631/

Wannan page din nakune ƴan amana aminiyata kuma Habibty ta.

Ummu Najma ,tawa ta hannun dama ta Marubuciyar(Matar Kulle)/(Ƙaramar bazawara),inamiki fatan alkhairi Allah yaƙara girma da ɗaukaka.

Nuseey ƴar amana jinjinarki daban kema inayinki over dear.

~Page Fourteen~
  
      Washegari suka tadda abin mamaki da tashin hankali a office don mutumin dasuka harba jiya sun tadda an kashesa kuma D.P.O baizoba,Lukman ne ya ƙirasa ya sanar masa abinda ke faruwa,cikin tashin hankali ya iso office ɗin ,kallonsa yakai kan gawar data fari wari alamun tunjiya aka kasheta,kallonsa yakai ga dukansu fuska a ɗaure yace"kuje ku kaita matuary afara bincike,waye yake duty jiya,cikin girmamawa Shareef yace"Sir Inspecter Daniel ne kuma yana asibiti munxo munsamu shima an raunatasa dagani gun kare amamcinne aka jimasa ciwo,ya mutu ko yana raye??da sauri suka kalleshi mamaki a fuskarsa Hafeez yace"Sir bai mutu ba yana asibiti dai rai a hannun Allah don sunji masa ciwo sosai,cikin ƙare tamƙe fuska yace"ayi bincike agane wanda ya aikata hakan,kai Sabeer kaina ɗaura akan aikin nan,cikin girmamawa yace"yes Sir,daga haka ya sallamesu suka wuce office,suna zama Sabeer yace"Allah yasa Daniel ya rayu don anmasa illa dayawa amma nayi mamakin hakan bayan Daniel akwai ƙwazo gun aiki akwai dai yadda akayi Insha Allah zanje asibitin anjuma,Fawaz yace"ni abinda yabani mamaki shine  yadda masu gadi basu san an shigo ba,Sabeer yace"zamuyi bincike don dolene mugano mai yake faruwa abubuwan sunyi fara yawa," atunanina duk abindake faruwa wani acikin station ɗinnan yana da saka hannu amma waye?meyasa?duk bamu saniba".

   Zaune take acikin a ɗakinta ta haɗa kai da gwuiwa,dafata Inna tayi tayi saurin ɗagowa takalli Inna tace"Inna yaushe kika shigo,cikin jinjina kai Inna tace"lfyarki kuwa Sabreena kinadai ganin Hafsa ƙawarki tare za'amuku auren nan amma bata lalace ta rame irinkiba inda damuwa kifaɗamin meke damunki?,murmushi tayi tace"a'a Inna bakomai fa kawai dai zanyi kewarku ne tafaɗa muryarta na rawa a sanyaye,dafata Inna tayi tace"haba ƴata ƴar auta ta kiyi haƙuri kinji,ai zanna zuwa kuma Ahamd ɗinma zaina kawoki kinji,gyaɗa kai tayi tace"tohm Inna,"yauwa ƴata kiɗanyi jiki kinga yanzu auren saura wata ɗaya to ki dage kibar damuwa".


     Hannunsa ne acikin na Sabeer dakyer yake magana yace"Sir  in our station there is some one behind all the problems happening(ranka ya daɗe akwai wanda shine makasudin abubuwan dake faruwa a station ɗinmu)nasan bazan rayuwa ba amma inaso kazama mai kula akwai masu farautar rayuwarka data ahalinki ka zama mai kiyayewa inasonka kuma banason komai yasameka yafaɗa hawaye na gangaro masa,Sabeer ma hawayen ya share yace"no Daniel u will be well kaji,tari yayi saida ya tsagaita yace"jiya ina banɗaki kafin abinnan yafaru naji wanda yayi kisan nan yana cewa,karka damu Oga za'a kashesu gaba ɗaya har mai gadin nasa to kafin nafito ne harya wuce gun da aka ajiye shi,kafin naƙarasa gunma har ya caccaka masa wuƙa koda nayi yunƙurin kamasa nima yamin illah amma kafin wancan ya mutu naji yaƙira sunan wannan dayazo da...bai ƙarasa zancenba yafara tari jini nafita a bakinsa ,cikin tashin hankali Fawaz yaƙira Doctor amma kafin yaƙaraso har Daniel yayi give up idonsa kyem akan Sabeer ga hannunsa na cikin nasa,fuskarsa na nuna cewar baigama faɗa masa abinda zai faɗa ba ya mutu,wani abu Sabeer yaji ya caki ƙirjinsa ransa yayi rauni a dalilinsa an kashe Daniel,wata zufa ya share yace"ku ƙira su Emma su kaisa matuary,idanuwansu duk sunyi ja zur jin furucin Daniel akanSabeer,haka ranar suka wuni cikim tunani,Shareef yace"dole mu farga akan wannan al'amarin.

   
       Da yamma a MANGA ya dawo gidan don fuskarsa sa ba walwala,part ɗin Ammie yaje ya kwanta a parour ,Aysha dabata san da mutum a parlourn ba tafito ɗaukar wayarta dake ringing daga ita sai towel iya gwuiwa ,tana ɗauka kamar ance kalli gefenki kawai ta haɗa ido dashi wanda shima tafiyar dayaji ce tasashi ɗagowa,kasa tafiya tayi shikuma da sauri yacire idonsa akanta aikuwa da gudu ta shige ɗakinsu tana sauƙe ajiyar zuciya,Hanan tace"me yafaru?tace"wlh Hanan Yaya nagani a parlour yana kwance naje ɗaukar wayata,Hanan naji kunya kamar ƙasa ta tsage nashige wlh,wata dariya Hanan tayi tace"wayyo yau Yayana yaga abinda zai biya kuɗi yasamu kinga yagansu masu kyau waɗannan fararen ƙafafun da wannan dogon hancin,gwarama dayagani kinga sai yaƙara kuɗi da kayan lefw tunda yaga matar tasa tafi haka,wata uwar harara Aysha ta zabga mata tace"Allah ke gara ce kema Allah yasa watarana Lukman yaganki haka da sainayi murna harda sadaka.

Sabeer kam kansa yaji ya saramasa ga abindake damunsa ga Aysha tafito zata ƙaramasa wata damuwar,ko alokacin data yi salatin yacire fuskarsa kansa ne ya sara don haka yatashi ya nufi part ɗinsu,yana zuwa ya tadda mazan gidan dukansu ashirin cip sai fira suke ba hayaniya banda Bappa dake ta kallon abu a wayarsa,Sabeer ne yakai dubansa gunsu yayi sallama yaje ya zauna kusa da Bappa,shikuwa Bappa da sauri ya ɓoye wayarsa donkar Sabeer yaga me yake kallo wanda shikuwa yagani kawai damuwar dake damunsa ta isa,Bappa ne yace"Sabeer wai kwananan ka canza fa nasan abubuwan dake faruwa a office ɗinku amma kana haƙuri kuma kazama mai juriya da dakewa,maƙiya fa dama haka sukeso sugane weaking point ɗinka su cutar dakai Insha Allah babu abinda zai samu koda ɗaya daga cikinmu,Sabeer ji yayi wani abu mai kamada jarumtar dayake ɓoyewa ta daki zuciyarsa tsoron wani abu yasamini nashi yabar ransa yace"hakane Bappa cikin abokaine kaine wanda na haɗu dakai a ƙarshe amma kafi kowa sona haka nima nafisonka kuma nafi yarda dakai Insha Allah zamu rayu tarw,rungumesa Bappa yayi yace"tnz Bandirawo na..

    AURE SAURA SATI BIYU.

  Shirye shiryen bikin Sabreena da Ahmad sai Hafsa da Kabeer ake kowacce ƴace tilo agun iyayenta ce don haka sosai ake shirin musu auren gata na kece sa'a,babu wani maganin matan da'ake basu don Inna tace taya zata aurar da ƴa budurwa ta tsaya bata wani magani,saidai suna yawaita shan ruwa da kayan itatuwa wanda shi yakamata budurwa tana amfani dashi sai gyaran dilkan dasukesha don agidan wata ƴar sudan aka kaisu cikin garin yola sai ana saura kwana biyu zasu koma.

      Zaune suke da Hafsa matar dake musu gyaran jiki tace"Dan Allah kuje nan shagon unguwarnan kusayo min tissue yaran basana ba nisa kuje,Sabreena dakejin faɗuwar gaba taɗau Hijab suka fito tana kyenkyama jikinta don sanyine ke shigarta harsaida Hafsa tace"Malama ya haka ne,tace"wlh sanyifa nafara ji tunda muka fito".

    Sunsaya tissue ɗin daidai sunzo wucewa tawani gida aka aka buɗe gate mota tafito da gudu,aibata yi wata wataba takusa bige Sabreena itakuwa cikin zare idona takoma gefe mai motar yafito yace"dan Allah kuyi haƙuri waenda suke cikin motar ne suka fito ɗayarsu tace"dan Allah kuyi haƙuri ɗayar ma tace"kuyi haƙuri,kallonta take ko ƙiftawa babu tace"Aysha wlh kuna kama da wannan sosai,itama Hafsa tace"Sabreena wannan taa dake sosai wlh ,kallon juna Aysha da Sabreena sukayi saikuma Sabreena takauda kai tace"Hafsa mutafi kawai kar anememu,tafiya sukayi batare da sun juyo ba,sunkusa shiga gidan dasuke ne wata baƙar mota tazo tawuce,buɗe glass ɗin akayi don zubda ruwan dayasa abaki,ware idanuwa yayi zaiyi magana amma harsun shige gidan,ƙarasawa sukayi,amma su Aysha ganinsu Sabeer yasa suka tsaya daga shiga motar,suma fitowa sukayi daga motar Sabeer yakallesu yace"ya haka baku tafi makarantarba ,Hanan tace"wlh wata maka kusan kaɗewa,nan dai suka labarta musu,Hanan tace"wlh Bb saika ganta suna kama da Aysha,Lukman yace"nidai inba zance meyakawo ta nan ba da zance nasanta don sosai tayi kama da matar da Ahmad zai aura  wacce nake baku labari wlh,kawai ji yayi yanason ganinta kodan yawan faɗar tana kama da Ayshansa da ake faɗa,Lukman  ya faɗa ga Hanan ma tafaɗa.

Fans kuyi manage da wannan dan Allah.

Karku manta damin likes da comment sannan ku raba zuwa ga sauran groups dan Allah👏🏻👏🏻...

Vote
Comment
Like

Ƴan wattpad karkumanta damin vote da comment tnx👏🏻👏🏻💃INA SONKU SONSO..

Gskiya vote yy ƙasa

SABREENA SABEERWhere stories live. Discover now