page twenty eight

203 11 0
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
             🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
              🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

~Khadeejaht Hydar~ ~Young-Novelist~

~The experienced~ ~writer of~ 👇

~IHSAN~
~UQUBAR UWAR MIJINA~
~WATARANA SAI LABARI~
~PRINCE AIRAN AND MAIMOON~
~KANKI KIKA CUTA~
~DUNIYAR MU A YAU~

~And Now with the most enjoyable one~ 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

Vote my novels and follow me on wattpad.
https://www.wattpad.com/user/YoungNovelist4
Or @YoungNovelist4

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote  akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

TWEETER
@Young Novelist II

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ga link din  novel din SABREENA SABEER.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb

Facebook page,like pls.
https://www.facebook.com/Khadeejaht-Hydar-Hausa-Novels-YoungNovelist-101121485268631/

Sorry for d late Update fans,tnx for missing d Novel.

PAGE TWENY EIGHT🖊️
    
    Visit me on wattpad Fam,Vote nd Follow 😍
@YoungNovelist4

  
    Ganin halin da tashigane yasa Abba da Inna suka koma da'ita gida don gaba ɗaya takoma kamar mutum mutuni,kowa yakoma tausayamata Hajiyar Ahmad ma dole take ɓoye damuwarta don Sabreena.

   Yauma tasha wahala agunsa don saida tayi kuka amma bakamar ranar farko ba,a hankali ta ɗaga idonta tana kallonsa idonsune ya sarƙe dana juna don shima kallonta yake a hankali ta sauƙe kanta ƙasa tare da lumshe idanuwanta,a hankali ya zareta daga jikinsa ya rungumeta da kyau a hankali yakai bakinsa kan kunnenta yace" U are sweet my Eesha,rufe fuskarta tayi da tafin hannunta kunya kamar ta nutse,hannunta yake ƙoƙarin janyewa yana magana,"wai Eesha kunyata kike har yanzu,kodan dole mutum yaji kunya kullum shi kuka da raki daga an taɓashi,saurin buɗe idanuwanta tayi a hankali tace" dama nasan hakan zakace ai sbd bakai bane,bakasan yadda nakejibane aida baka faɗi hakan ba taƙarasa zancen tana ƙwaɓe fuska a shagwaɓe,saurin gimtse dariyarsa yayi yace"noo Hubby am joking wlh ai nasan ke jaruma ce,tnx alot,turo bakinta tayi tana gunguni ba zato taji ya capki bakinta yana tsotsa,saurin turesa tayi tana jan bargon jikinta tace"ka kyaleni Allah ni gabana sai faɗuwa yake kuma ...bata ƙarasa maganar ba wayarsa tafara ruri,hannu yasa ya ɗauki wayar ɗaya hannun kuma ya riƙe Aysha yana madata jikinsa,ganin waya zaiyi yasa ta tsayawa ,yana amsa ƙiran yasa a handsfree yace"Alhaji Lukumanu har kun huta a gida kenan fatan kun kai Hanna da Ahmad gida don naga yanayinsa sai a hankali?cikin sanyi Lukman yace"Sabeer sai dai haƙuri Ahmad babu Allah ya karɓi abunsa Ahmad yayi hatsri,nan yafaɗa masa mai yafaru cikin tashin hankali Sabeer yace"Haba Lukman wai wane Ahmad ɗin nifa Ahmad ɗin dakuka tafi dashi fa nake magana,Shareef ya karɓi wayar yace"Sabeer shi Ahmad ɗin daka sani shine ya rasu,Sabeer sai kaga yadda Hajiyarsa ta kasa zaune ta ɗimauce,inkum kaga matars sai kayi hawaye babu wanda batasa kuka ba sai suma taketayi a jere,innalillahi kawai Sabeer yake jerawa Aysha kam kuka take sosai don ta ƙara tuna Hafeez haka shim Sabeer saida ya tuna Hafeez sbd shima kusan irin hakanne,katse ƙiran yayi yafar shafa kanta yana bata baki,ganin tayi shiru yasa ya ɗauketa donyin wanka,suna fitowa suk shirya sai taga yafara haɗa kayansu,ya juyo gunta yace"jekici abinci kizo insha Allahu yanzu zamu bi jirgi zuwa Nja,dama yunwa takeji don haka taje taci abincin koda ta dawo har yagama haɗa komai nasu tsaf ya kimtsa,handbag ɗinta ta ɗauka shikuma yaja babbar akwatinsu suka rufe gidan suka shiga mot sai airport.
Suƙa lfya SABEER AYSHA 🤪🤪🤪.
   Zaune take ta haɗa kai da gwuiwa tana hawaye,Inna data daɗe a tsaye ta ƙaraso ta zauna kusa da'ita tace"Haba Auta ta meke damunki haka kikazo nan kika barni da kewa?ɗagowa tayi takalli Inna a hankali tace"Inna Ya Ahmad Inna shinakeso ya dawo,cikin tausasawa Inna tace"kintaɓa ganin wanda ya rasu ya dawo?,kai ta girgiza saikuma ta fashe da kuka,rarrashinta Inna tayi bayan tayi shiru Inna tace"kinga yanzu kina takaba kamata yayi ki daina saka damuwa a ranki kina yawaita nafulfuli da istigfari kina nemawa Ahmad rahama agun Allah kinji ko kinason Allah yana azabtar dashi akan kukanki?saurin girgiza kai tayi,Inna tace"yauwa ƴar albarka maza ɗauki abincinki kici in dafa maki shayin zakisha,"eh Inna zansha taƙarasa zancen tana mai kai hannunta cikin kwanon don kar Inna tasa damuwa a ranta,amma itakam damuwarta yayi yawa rashin Ahmad ya taɓa ranta.

    "ke yanzu Fadeela akan wani Sabeer ɗin banza zaki dami kanki dallah ki manta dashi shi yayi asarar gara an aura masa kwaila kuma kema kince ba Aysha ya auraba kenan auren dole yayi kinga...yimin shiru Laɗeefa don ubanki ni zakicema na ƙyale Sabeer to wlh koma wacece ya aura sainaci ubanta kuma na rabata da ranta,ganin kamar kwayar datasha yafara aiki yasa Laɗeefa saurin fara bata haƙuri don batason su rabu kodan kuɗin datake samu aguta,dakyer tashawo kanta akan zata bincika yaushe zasu dawo.

   A cikin jirgi kuwa kukan da Aysha tayi na rasuwar Ahmad yasa tayi sanyi,suna zaune aka kawo ma Sabeer tea da kwai don baisa komai acikin saba,kallon Aysha data tohse hanci yayi yace"ya akayine?tace"bakomai kawai wari nakeji,baisake magana ba yagama cin abincin yasake kallon yadda ta lafe a kafaɗarsa tana bacci hankali kwance.

  
  "Sabreena ki tsaya karkiyi nisa dani kinga Aysha tanason tafiya tabarni don Allah ki tsaya ki yafemin,kuka take  bil hakki da gaskiya tace"bazan zauna dakai ba tunda na rasa Ahmad sau nawa na nuna ina sonka kaƙi ni ba ruwana dakai kaje kazauna da ita,kaje nace!taƙarasa zancen cikin karaji da kuka,Sabreena!Sabreena!!da sauri tafarka daga baccin la'asar ɗin daya ɗauketa,cikin mutuwar jiki tace"Inna sannu wlh baccine ya ɗaukeni,Inna tace"ai baccin bayan la'asar ba kyau maza tashi kije kiyi alwala.magriba ta kusa,tashi tayi ta nufi ƙofa tana tunanin mafarkin datayi.

   Suna isa suka tadda motar gida yana jiransu,tundaga nesa Hanan ta hangesu ta tafi a guje tana Oyoyo bb Oyoyo my Eesha,suma cikin murmushi suka tarbeta sai kace ba shekaranjiya bane suka rabu,driver ne ya ƙarɓi kayansu yasa a booth Hanan ta zauna a gaba kusa da driver su Sabeer kuma suka shige baya,suna isa gida tundaga gate sukaga canji suna shiga gidan suka tadda su Lukman da duk wani makusan tansu suna jiran tarbarsu wanda sun ɗauke party ɗin da'aka tanadarmusu na samun sauƙi da murnar aure saboda rasuwar Ahmad,kowa fuskarsa murna cw na dawowar Sabeer Aysha kam sai sunne kai take ganin kowa na mata wani kallo,da gudu taje tafaɗa jikin Umminta tana dariya itama murmushin  tayi ƙasa ƙasa  tace"kingirma fa yanzun,addu'a akayi sannan kowa yakama gabansa Aysha  ma gun Umminta ta nufa, su Bappa kam kamar sa zuba ruwa a ƙasa susha don murna MANGAn su ya dawo,ɓangarensu ya nufa komai tsaf dashi wanka yayi yaci abinci   saikuma suka ɗunguma suka fito zuwa gunsu Ammee,parlourn maƙil yake da ƴan uwa da abokan arziki anata hira suma zama sukayi anayi dasu anjuma kuma saiga su Lukman nan falo ya kicime bakajin komai sai muryoyinsu da dariya,shikam gogan ido yake bazawa ko zaiga Aysha amma babu alamarta,don haka yama  Hanan ido da ina Aysha,itama da ido tamasa magana akan tanagun Umminta.

    Mama wlh nayi kewarku,cikin murmushi Abuu yace"muma hak Auta ta dafatan ba matsala ko?,tace"eh Abuu babu,"to bazakije ku gaisa dasu Ammin nakuba kinzo kin jibge anan saikace da ba'acan kike ba cewar Umminta,cikin turo baki tace"ni Allah Mama kunya nakeji bazan iya zuwa ba,cikin dabara Ummi tace"kije anjuma saiki dawo banajima kince zakuje gaisuwar Ahmad ba kije ku shirya,fitowa tayi ta nufi cikin gidan cikin kayan data sauya daga doguwar riga zuwa riga da skirt dasuka mata cas tasa Hijab babba,da sallama ta shigo parlourn,ganin mutane kowa ya juyo yana kallonta yasa taji wata sabuwar kunya ya lulluɓeta harta kasa ƙarasowa,wata Antinsu Sabeer mai suna Zaitoon tace"ah matar Autar Ammee ki ƙaraso mana muda muketa jiran muga natar Autar mu kya tsaya anan,kowa dariya yasa banda Sabeer daya haɗe rai shi ala dole kar ace masa auta agaban yara,yace"Anti Zaitoon ainafi ƙarfin auta kema kinsani,tace"toh Anti Sabeer tunda munma aure ko,cikin haɗe rai yakalli Aysha wacce take murmushi shima sai murmushin yakamasa yamata alamun data zauna,zama tayi kusa da Hanan tashiga gaida Amme da sauran mutanen gun,ansawa sukayi cikin sonta suna ta tsokanarta,Anti Feena tace"kaifa Sabeer jinya tama rana tunda anma amarya,sake kwashe da dariya sukayi gaba ɗaya,Amee tace"kubarmin auta na ya huta,zo nan Autana zuwa yayi ya ɗaura kansa saman cinyarta ta sake kama hannun Aysha ta ɗaurata kanta akan ɗaya cinyar tata,kowa yasa dariya Anti Zaitoon tace"ah lalle Auta da matarsa,Anti Feena tace"wai Sis Hameeda yaushe zamuyi bikin ɗan gata ɗan autanmune don saimunyi na ƙere sa'a,wacce aka ƙira da Sis Hameeda tace"ai angama tsara komai next week Insha Allah kunga ai lokacin kowa yasamu chance,duka suka amince da haka shikam nasa ido ne don dama sunyi alƙawarin aurensa ko biyar ɗinsa bazai cire ba.

Tomf Fans NADAWO

MU HAƊU A BIKI NEXT PAGE.

NGD DA NUNA ƘAUNA AGARENI NAJINA SHIRU,XEEYERT APPLE ONE LOVE.

SHARE
COMMENT
VOTE ON WATTPAD🤞🥰

AUTAR💃💃🖊️🖊️🖊️
Billyn Hamma🤍

SABREENA SABEERWhere stories live. Discover now