page twenty nine

185 13 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
             🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
              🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

~Khadeejaht Hydar~ ~Young-Novelist~

~The experienced~ ~writer of~ 👇

~IHSAN~
~UQUBAR UWAR MIJINA~
~WATARANA SAI LABARI~
~PRINCE AIRAN AND MAIMOON~
~KANKI KIKA CUTA~
~DUNIYAR MU A YAU~

~And Now with the most enjoyable one~ 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

Vote my novels and follow me on wattpad.
https://www.wattpad.com/user/YoungNovelist4
Or @YoungNovelist4

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote  akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

TWEETER
@Young Novelist II

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ga link din  novel din SABREENA SABEER.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb

Facebook page,like pls.
https://www.facebook.com/Khadeejaht-Hydar-Hausa-Novels-YoungNovelist-101121485268631/

PAGE TWENY NINE🖊️
   @YOUNGNOVELIST4
Dont forget follow and vote plss👏🏻👏🏻

Masu voting sauran novels ɗina a wattpad ina godiya Allah yabar ƙauna😍💞👏🏻❤️.

   Sai bayan magrib kowacce ta nufi gidanta bayan sun gama saka Aysha kunya,Mama ma ɗakinta ta nufa Hanna tabita tana cewa"Ammee dan Allah kibani wayar naƙira Abee yazomin dashi,Aysha kam ɗakinsu ta nufa dai dai Sabeer yashigo parlourn,bata ji ko ganin saba amma shi akan idonsa Hanan da Mama suka ƙarasa shiga don haka yayi wuf yabi bayanta,da sallama ya shiga lokacin tana ƙoƙarin cire rigarta don ta riga dama tacire zanin ta ɗaura towel,saurin sake rigar tayi tana mai juyowa,kallonta yakeyi bako ƙiftawa itakam hijab ɗinta take ƙoƙarin ɗauka amma ya rigata tare da saurin riƙe hannunta,janyota jikinsa yayi ya rungumeta tsam atare suka sauƙe ajiyar zuciya,cikin sanyin dayake samun kansa da zazzaɓin dake damunsa kullum dare yakai bakinsa kunnenta a hankali yace"i missed u rabona danaji ɗuminki tun jiya da daddare kafin muzo,lumshe idanuwanta tayi tace"Uhmm jin yafara koƙarin kissing ɗinta,kan gadon ya nufa da'ita ya kwantar ta tare da mata rumfa yaci gaba da kissing ɗinta,jin Hanan na sallama ne yasa Aysha fara zamewa a hankali tace"Hanan na sallama,komawa gefe yayi ya juya mata baya,tana tashi tasa Hijab tayi hanyar banɗaki don bazata iya kallon Hanan ba,Hanan kuwa jin shiru yasa ta turo ƙofar ta shiga don tasan su kaɗaine a ɗakin wataƙil Ayshan na wankane,turus tayi ganinshi a zaune bakin gadon ya zuba mata ido,cikin murmushi tace"Bb ashe kana ciki shine baka amsa sallamataba ina Aysha,yace"kefa surutunki yayi yawa Aysha na wanka meyafaru?tace"babu komai kwanciya zanyi yace"shikenan inta fito kice takaimin abincin a bq(boys quarters daga haka ya fita,yanasan su kwana tare amma ɓangarensa bazaiyiba badon rashin guri ba a'a matarsa cikin mazane baiso sai isa ya zaɓi ɗakunan dake gefe kusa da nasu Ammee,koda ta fito Hanan ta kalleta tace"Sis Bb yace ki kaimasa abincinsa,"to Aysha ta amsa,kayan bacci baƙake tasa,rigar iya tsakiyar cinya sai wando wanda yafi rigar tsayi da kaɗan yama farar fatarta kyau,turaren humra ta shafa a kowane saƙo da lungu na jikinta Hanan takalleta tace"duk wannan shirin na Bb ne lalle Bb yana shanawa wlh,duka Aysha takaimata cikin dariya tace"kya sani da sa ido daga haka tafita tana cewa"Madam karki rufe ƙofa zan dawo dan Allah,da to Hanan tabita don tasan Sabeer bazai taɓa bari tadawo ba.
Da sallama tashigo ɗakin yana kwance acikin blanket yana rawar sanyi,da sauri taƙaraso ɗakin tahau gadon tare da yaye blanket ɗin cikin rawar  murya da jiki ta taɓa wiyansa tace"meyasameka?bakada lafiyane dama?ko in ƙira  Ammee?girgiza mata kai yayi yace"zai tafi zo ki rufemin jikina,blanket ɗin taja ta rufe masa jiki ta zauna tana taɓa wiyansa tace"ko zakaci abinci sai kasha magani,hannunta yakama yana kallonta kwanciya tayi a gefensa,sake matsowa yayi kamar zai shige jikinta,bakinta yafara laluba ganin yanayinsa yasa ta matso tare da haɗa bakinsu waje ɗaya,harshenta yakamo yafara laluɓar ƴar matarsa saida yagaji da wasansa ya rungumeta sanyin jikinta na sassauta ɗumin jikinsa,tashi tayi zata maida rigarta ya riƙe yace"sleep wife,komawa tayi ta kwanta ya ɗaurata ajikinsa yana shafa kanta.

    
    "Hafsa yanzu wai yanaga kamar kina ƙara jiki ne kuma kinyi haske?,murmushi Hafsa tayi tace"ko tanbayata ya jiki bakiyiba wanda shine ya hanani zuwa gun gaisuwa,murmushi Sabreena tayi tace"ah sorry Babe ya jikin to kodai nasamu takwarana?murmushi Hafsa tayi tace"nima dai bansaniba ,Sabreena tace"uhnmm komai abinki aishi ba'a ɓoyesa,haka dai sukayita fira Hafsa naƙara kwantar mata da hankali ba'ita tabar gidan ba sai bayan isha'i don ba yanzu zata koma ba saita haihu cikinta yanzuwa wata shidda amma baida girma sai isa take saka ƙaton hijab Sabreena ma bata kulaba saida sukazo yin sallah tagani yafito rass dashi taita mata tsiya,koda ta rakota ƙofar ɗaki  saida tace"to Mama Hafsee akularmin da ɗana dakyau ki kuma gaida babansa.

     "Faɗeela albishirinki cewar Laɗeefa,cikin fesar da hayaƙin tabar bakinta tace"goro,ya akayine? Laɗeefa,tace"nazo miki da wani babban labari mai girman gaske,Fadeela tace"inajinki,gyara zama Laɗeefa tayi tace"to sati mai zuwa za'a gudanar da shagalin auren Sabeer da Aysha,cikin zabura Fadeela tace"wane Sabeer ɗin wacce Aysha kuma?"calm down Babe zauna muyi mgna,zama tayi Laɗeefa tace"ashedai ƴar mai gadin nan ya aura kuma tun satin can suka dawo,cikin zafin rai Fadeela tace"to wacece damuka gani da Sir Ahmad rannan?wannan matar Sir Ahmad ce mai rasuwa kawai dai sunyi kama ne,Fadeela tace"zat gane ruwa ba sa'an kwando bane da zataso har ta auri Sabeer ɗina,wlh saina halakata.

   Da safe daya tashi ras yayi kamar ba shine ya kwana da zazzaɓi ba,saida ya ɗauro alwala yazo yafara tashinta,buɗe idanuwanta dasuka mata nauyi tayi ta zubasu akansa,shima kallonta yake,a ransa yana mamakin meke sata nauyin bacci  haka yace"zanje masallaci sai na dawo,adawo lfya tamasa ta tashi tawuce banɗaki tana mai addu'a,tana gama sallah tafara azkar ko gamawa batayiba tayi bacci akan salla myar,ƙarfe bakwai ya shigo ɗakin,murmushi ne ya suɓucemata ganin yadda ta dunƙule gu ɗaya ga carbi a hannunta alamun dai ba ason ranta baccin ya ɗauketa ba,ɗagata yayi cak ya ɗaurata kan gaɗo tare da cire mata hijab ɗinta,buɗe idanuwanta tayi a hankali tace"Ina kwana,"lfya ya amsa yana mai ja mata bargon yana kallon fuskarta,cikin so da ƙaunarsa tace"ya jikin naka?kwanciya yayi tare da ɗaurata kan jikinsa yace"gashi nan babu abindake damuna dama kullum saida daddare yake damuna safiya nayi kuma zai barni,hannunta ta ɗaura a kansa tana shafawa cikin baccin dayafara ɗaukarta tace"nikuma kaga kullum sai indinga bacci kuma da bahaka nakeyiba,kallonta yasakeyi yace"my Eesha ke baccin kawai kika lura kinayi gaba ɗayankima kin canza,kinyi haske kinyi ƙiba kodai bakida lfya ne?tace"uhm uhm lfyata ƙalau amma ai kaima naga kana ramewa kaine bakada lfya,hannunta yakama yace"kallon tsoro kikamin kiyi baccinki anjuma saimuje asibiti adubamu,bata sake maganaba sai bacci,shikuwa ƙara rungumeta yayi ajikinsa yanajin ƙaunarta na barazanar ɗauke numfashinsa.

     "Daddy dan Allah kasa su Daniel su kashemin matar Sabeer wlh ni har yanzu ina sonsa,ba zato taji sauƙar mari guda biyu masu lfya akan fuskarta karo na farko da Abbanta yasa mata hannu,bai sake magana ba yabar mata parlourn,kuka ta rushe dashi tana ihu,Laɗeefa ta riƙeta tace"haba Fadeela kar soyayya yasa ki zauce ki nutsu mu nemi mafita inma so kike akasheta saiki bari muyi kayanmu a sirrince ai kema kinsan munada masu mana aiki kawai kibani lokaci muyi aikin dabaza a zargemu ba,Fadeela tace"shikenan Laɗeefa so nake ayi ta ta ƙare kowama ya rasa wlh ko ta mutu ko na mutu koshi Sabeer ɗin ya mutu,tunda ya ƙunta tamin akan ta wlh shima sai ya ɗanɗani ɗaci da raɗaɗi a rayuwarsa,ni Fadeela Falalu saina ƙunta tawa rayuwar Sabeer inhar be aure niba.

Vote
Comment
Share

Autar✍️💃
YoungNovelist
Billyn Hamma

SABREENA SABEERUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum