page thirty

190 13 2
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

~Khadeejaht Hydar~ ~Young-Novelist~

~The experienced~ ~writer of~ 👇

~IHSAN~
~UQUBAR UWAR MIJINA~
~WATARANA SAI LABARI~
~PRINCE AIRAN AND MAIMOON~
~KANKI KIKA CUTA~
~DUNIYAR MU A YAU~

~And Now with the most enjoyable one~ 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

Vote my novels and follow me on wattpad.
https://www.wattpad.com/user/YoungNovelist4
Or @YoungNovelist4

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

TWEETER
@Young Novelist II

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ga link din novel din SABREENA SABEER.
https://my.w.tt/PnGPV1PO2bb

Facebook page,like pls.
https://www.facebook.com/Khadeejaht-Hydar-Hausa-Novels-YoungNovelist-101121485268631/

PAGE THIRTY🖊️

@YOUNGNOVELIST4
Dont forget follow and vote plss👏🏻👏🏻

Masu voting sauran novels ɗina a wattpad ina godiya Allah yabar ƙauna😍💞👏🏻❤️.

ALHAMDULILLAH Yau Allah ya nunamana zanci gaba da rubuta wannan labarin mai ratsa rai da tausayi.

Barkanmu da azumi barkanmu da sallah harda bayan sallah fans,ina miƙa saƙon gaiduwata ga waenda suka dunga nemana akan nacigaba da novel ɗinnan,harma waenda basu tambayaba,kusani kuna raina,kuma yau nacika muku alƙawarinku ga SABREENA SABEER NAN zanci gaba da rubutashi,YOUNG NOVELS BILLYN HAMMA TAKUCE🖊️,kuci gaba dabin alƙalamin Khadeejaht Hydar..

Da sassafe su Sabeer suka wuce asibiti babu wanda yasani ,don lokacin da suka fitama Abuu yana karyawa,asibitin wani abokinsa private suka nufa,batare da tunanin komai ba suka mai bayanin abinda ke damunsu,Dr Hisham yakalli Sabeer yace"Oga Allah ya inganta ya sauƙeku lfya,da mamaki Sabeer da Aysha suke kallonsu,Sabeer yace"Hisham bafa wasa nazo nayiba Allah zan saɓa ma,cikin murmushi yace"Allah fa dagaske nake kun kusa zama Mom and Dad,da sauri Aysha ta tashi tafita waje cikin kunya sosai,shikuwa Sabeer gyara zama yayi cikin tsananin murna yace"Hisham.dan Allah fa,masha Allah,Alhamdulillah Ala ni'imatuka alayya,haka ya dinga jerama Allah ƙirari,Hisham na tayashi,tashi yayi ya rungume Hisham yace"Hisham tukwuicinka daban yake ngd sosai ,zamu dawo insha Allah,daga haka ya fice yana mai ƙara godema Allah.

A mota ya tadda Aysha ta haɗa kai da sitiyara tana hawaye ,da sauri ya ɗagata ya ɗaura kan cinyarsa gabansa na faɗuwa"kardai Aysha cikin sane bataso,tabb da akwai rigima,don shi babu abinda yaji yakeso a duniya bayan mamarsa ,Hanan da Aysha sai cikin nan,daƙyer ya buɗe bakins"Aysha meyafaru kike kuka?wani abunne?,ko cikin ne bakyaso,da sauri ta gƴaɗa masa kai tana mai kwantar da kanta kan ƙirjinsa,"to meyasa bakyason gudan jininmu kyautar Allah?tace"wlh su Ammee zasusan inada ciki tun ban tareba,dama tunjiya naga anata kallona,ashe cikin suka gani,nidai dan Allah kasa acire in muka koma gidanmu sai in haifi wani,wlh za'ace banda kunya taƙarasa zancen tana bubbuga ƙafarta,da murmushi Sabeer yakalleta yace"shikenan karki damu gobe ko jibi zamuzo sai acireshi ai farincikinki shine nawa my Eesha,don yasan inba haka yayi ba me rabasu sai Allah,yasan yarinta da kunya ke damunta,inbanda abun Aysha waye zaiga cikin wata ɗaya,cikin murna tace"Nagode sosai Bbnmu ngd,"welcome matar muje gida kar su Anti Zaitoon suzo nemanmu,sunyi ɗan tafiya taga mai saida abarba da Banana,a hankali ta saci kallon gun tana haɗiye miyau,duk Sabeer na kallonta,tsayawa yayi ya fito daga motar ya tsallaka,abarba da banana da duk fruit ɗin dayagani agun ya saya dayawa akasa a babbar leda ya ɗauka bayan yabada kuɗin,akan cinyarta ya ajiye yace"gashi kiyita sha kafin acire wanda yasamaki kwaɗayin,ki basa yasha kafin a kashesa yadda mahaifiyarsa ta kuɗirta,bata kallesaba ta ɓige da ɗaukar banana tafara sha,kafin sukai gida ta shanye bunche ɗaya na banana apples uku,shidai baice mata komai ba har suka isa gidan.

Suna isa ita tafara fita da ledar kayan fruit ɗin a hannunta,shima fitowa yayi suka jera suna tafiya dayake mutanen gidan babu wanda yafito,kagansu abun sha'awa,har sun kusa mashigar parlour sukayi kiciɓis da Anti Zaitoon da Anti Hameeda sunfito da alama ɓangaren su Sabeer zasu,galala suka tsaya kallonsu Aysha kam kunya ya gama kamata ta koma bayansa ta laɓe,Anti Hameeda tace"Auta ku daga ina haka da sassafen nan,bai amsaba illa hannun Aysha daya kama yace"kije ki kwanta ki huta kinji,kisa Hanan ta ɓare maki abarbar kisha saiki kwanta,gƴaɗa masa kai tayi kanta a ƙasa ta wuce sum sum kamar muna fuka,Anti Zaitoon da mamaki tace"Auta daga ina kuke haka?kardai yarinyar mutane ka ɗauka kuka kwana wani waje?,cikin basarwa yace"kudai wlh anyi Aunties masu sa ido to nida matata banda haƙƙin fita da'ita ai ko a hotel muka kwana halal ɗina ce daga haka yabarsu tsaye yana murmushinsa yayi wucewarsa don yasan ya rufe bakin maganar,Anti Hameeda tace"ni wlh ganima nake anya ba ciki ne da'itaba,don ni Sabeer yanzu tsoro yakebani,Anti Zaitoon tace"ciki kuma na yaushe ai kina ganinta kinga mai jaririn ciki amma Allah ya shirya Sabeer maimakon yabari akaita,uhmm XEEYERT APPLE kinji sufa🙈🤥🤥.

Yana shiga ya tadda Hanan na ɓare abarbar bata gamaba amma Aysha sai ɗaukar wacce aka yanka take tanasha,a ƙofa ya tsaya yana kallonta ko ƙiftawa babu,kamar ance ta ɗaga kanta tagansa tsaye yana kallonsu,tashi tayi da sauri takarasa gunsa tana ƙwaɓe fuska,cikin kula yace"meyafaru?tace"ba Hanan bace taƙiyin sauri ba,Hanan ta ɗago tace"kajitafa yanzun nafito nasamu ta shanye duka kayan marmarin saura kaɗan ko ragemin batayiba donma kinsamu ina ɓare maki,Sabeer yace"lalle Hanan yakamata na ɗaukar maki mataki amma kafin nan kigama ɓarewa tukun kibata,Ammee wacce tafito yanzun tace"ah waza ama hukunci badai autar mata naba zaku taɓa,Aysha komawa tayi ta zauna tana mai sadda kanta ƙasa don sosai tanajin kunyar Ammee,Hanan tace"Ammee ki kallifa duk ta shanye komai abarbarna tunkafin agama ɓarewa takusa shanyeta,kallon Aysha tayi takalli Sabeer wanda shima sai yanzu yaƙaraso ya zauna kusa da Hanan,shida Aysha sun sata a tsakiya,Ammee tace"to ke Hanan ai saiki barmata tunda ke ba ma'abociyar shan kayan fruit bace,Sabeer yace"ai inbatayi haka ba baza'a san sunanta Auta ba,ana haka saiga su Anti Hameeda sun dawo,harda Anti Feena ,ko kallon inda suke baiyiba ya maza,zama sukayi,Ammee takalli Sabeer tace"Sabeer kaji su sisters ɗinka sunce Insha Allahu gobe zasu gudanar da shagalin aurenka shine nace suzo su faɗamaka ni ba ruwana,cikin murmushi yace"haba Ammee harsai sun tambayeni wlh ni ko yau sukeso ayi za'ayi,cikin jin daɗin irin haɗin kan Ƴaƴanta tace"Masha Allah,Allah yamuku albarka ya ƙara haɗa kanku,ameen suka amsa duka,Anti Feena tace"Ammee komai mun shirya.gobe da safe misalin ƙarfe tara za'aje dinner sai azahar muyi walima,Ammee tace"shikenan amma bakuma sanar da jama'a ba,babu wanda yasake magana aka hau fira ana dariya,Anti Zaitoon ce takalli Hanan tace"Hanan kitada Aysha taje ta kwanta tun da muka shigo naga tafara bacci,kallon Aysha wacce tagama nisa a bacci Sabeer yayi ya saki murmushi,tadata Hanan tayi takaita ɗaki tadawo.

"Ke zakiyi tafiya bayan kinsan sabon sati za'ayi shagalin auren Sabeer,cikin murmushi Fadeela tace"haba Laɗeefa taya kike tunanin zan manta hakan,kwana biyu kacal zanje nadawo dagacan nasake hutawa,kema kinsan bazan br zumar sairayin nan ya wuce niba.

Alhamdulillah nadawo,iya vote,comment da share ɗinku iya typing ɗinku.

Ƴan wattpad ina jiran sabbin votes da comment.

Autar💃🖊️
YoungNovelist
Billyn Hamma.

SABREENA SABEERWhere stories live. Discover now