Page Two

663 37 4
                                    

🌹🌹🌹🌹🌹🌹
             🍃🍃🍃 🍃
SABREENA SABEER
              🍃🍃🍃🍃
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

Story and written by

Khadeejaht Hydar Young-Novelist

The experienced writer of 👇

IHSAN
UQUBAR UWAR MIJINA
WATARANA SAI LABARI
PRINCE AIRAN AND MAIMOON
KANKI KIKA CUTA
DUNIYAR MU A YAU

And Now with the most enjoyable one 👇

SABREENA SABEER
(Love,fight,saga,sacrifice).

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/

Ban yarda wata ko wani ba su juya min littafi ba.

Ga masu son samun wannan littafin updated ba tare da neman jira ba a duk lokacin da nayi post to a neme shi a wattpad ,kuyi follow sannan ku danna vote  akan kowane pages na littafin SABREENA SABEER.

Follow and vote on

WATTPAD
YoungNovelist4

Blog:
https://khadeejahthydaryoungnovelist.blogspot.com/?m=1

INSTAGRAM
Khadeejaht-hydar -youngnovelist

TWEETER
@Young Novelist II

FACEBOOK
Khadeejaht Hydar YoungNovelist

BAKANDAMIYA
Khadeejaht Young-Novelist Hydar

GMAIL
NanaKhadeejamusa@gmail.com

Ban yarda wani ko wata ba ya juya min littafi ba.

Novel is free just need ur support dearies,visit me on wattpad to read more of my stories.

Page Two

Sai da suka kaita ɗakin da babu komai sai tabarmu wanda in zaka shiga ɗakin ma sai ka tsuguna kamar de bukka irin ta fulani tukun suka sheƙa mata ruwa ,firgigit ta tashi tare da fasa wata uwar ƙara ta ce "Dan Allah kayi haƙuri na tuba ka yafe min buɗe idonta tayi amma bata ga kowa ba sai duhu dake cikin ɗakin,rushewa tayi da kuka tana nadamar zuwa kasuwa a wancan ranar,tashi tayi ta fita daga ɗakin tayi tsakar gidan tana kuka sosai,fitowa yayi daga bukkarsa a fusace ya ce "ke wace irin mahaukaciya ce zaki dinga min ihu a gida ko kina buƙatar wasu marukan ne, yayi kanta saurin tsugunawa tayi tana kuka da masa magiya akan ba zata sake ba,a ransa ya ce "saina horaki ta yadda nan gaba ma ba zaki ma wani rashin kunya ba kallonta yayi a karon farko daya kalli mace don ra'ayin kansa,Sabreena doguwa ce sosai amma sam bata da jiki sai shape don ko a makaranta mai ƙirar coca-cola suke ce mata ,bata da haske sosai amma akwai manyan idanu ga gashin idonta dogaye kamar wacce ta ƙara sai gashin gira kamar zai haɗe,tana da madaidaitan laɓɓa wanda ƙasansa yake pink sama kuma baƙi wanda ya sake ƙarama fuskarta kyau sai gashin ta wanda yake har waist ɗinta ga baƙi amma bai da cika, ita sam bata son kitso ko kaɗan ga gaban goshin ta ma gashine a kwance lub-lub sai sajenta mai kyau a taƙaice de Sabreena akwai komai saidai abinda ya ɓatata akwai rashin kunya da tsiwa kasancewarta ƴa ɗaya tilo agun iyayenta, wanda suke da rufin asiri dai-dai gwargwado wanda hakan ne yasa tabar ƙauyensu karatu suke zuwa na cikin gari,Malam Mustapha kanurine na usuli wanda asalinsa ɗan habasha ne amma yaƙi ya dawo dasu Nigeria a jahar adamawa da matarsa mai suna Kulthum Hausawa suce(Kaltuma) wacce ta kasance Balarabiyar Habasha, Malam Mustapha ya ɗauki son duniya ya ɗaurama Sabreena wanda asalin sunanta(Khairat)komai takeso bata yake a kullum mahaifiyarya takan zaunar da'ita tamata faɗa amma taƙi saurara tabi huɗubar mahaifinta,ɗauke kansa yayi daga kanta yace"ki dainamin kuka bake wai mara kunya ba kidinga mawa mutane rashin kunya gaki fitsararriya ko zaki gane kuranki tashi maza ki share gidannan tas kar naga ko tsinke saboda ni mazaunina ba dauɗa kice kikazo  min da'ita ,cikin kuka ta tashi ta ɗau tsinstiyar daya jefomata tafara share gidan hijabinta nabinta,ɗagowa tayi taga bayanan ta cire hijabin ta gyarashi tasaka a baibai don kar yayi dauɗa taci gaba da sharar,tana gamawa ta zauna tana haki da kuka,haka ta zauna babu kowa a gun ga gidan a garkame babu hanyar fita,wani sabon kuka ta kece dashi jikinta na ɗaukar zafi,dai-dai lokacin yafito yace"zonan cikin ɗaga murya jiki na rawa taje ta tsuguna agabansa tace"dan Allah Manga kayi haƙuri bazan sakeba wlh sharrin shaiɗanne,ko kallon kirki bai mataba yace"tashi kije ki dafamin abinci akwai komai ga itace nan ki hura,cikin matsanaicin kuka tace"wlh ban'iy girkiba banayi a gida,da mamaki yace"baki iya girkiba yau kam zaki kowa,saima shekarunki nawa baki iya girkiba cikin sheshsheƙa yace" sha takwas yace"kuma baki iya girkiba maza tashi kije akoyamiki don daga yau ke zakina mana girki kinga gidannan mu ashirin ne,haka ya tasa ƙeyarta suka nufi madafar.

Malam har yanzufa yarinyar nan bata zoba wlh nadamu kaga fa har magriba ta kusa Allah yasadai lafiya,yace"wlh kam bari inje gidansu Hafsa na dubota kafin ya rufe  baki saiga Hafsa tayi sallama tagaidasu tare da cewa"Sabreena kifito mu tafi keda bakya latti mekika tsaya yi Mama kode bata jin daɗine,cikin fargaba Mama da Baba har suna rige-rigen mata tambaya sukace"kamar ya batare kukaje makaranta ba yau?cikin rashin fahimta tace"Mama aini banje makranta ba yau ,cikin rawar murya Baba yace"munga ƙarfe biyar  kuke dawowa munma zata wani aikinne ya tsayar daku amma damukaga har magriba ta kusa yasa mukace bara muje mu tambayeki shine ma kikazo kika samemu,Mama kuwa sai nanata "Innalillahi wa'inna ilaihir-raji'un take to ina Sabreena ta nufa nan fa suka fita akafara gayawa mutanen gari cewar ba'aga Sabreena nan hankalin kowa yatashi aka bazama nemanta,har makarantarsu anje kuma an tabbatarmusu taje tayi karatu kuma tare da'ita aka kulle makaranta,inda suke hawa mota sukaje,Ado wanda yake ɗakkosu yace"ah Hafsa yau bakuzo makarantaba mwyafarune?,cikin sarewa tace"wlh banajin daɗine amma Sabreena tazo ,yace"ai kuwa yau ba mota ta tahau ba don bangantaba,cikin zubda kwollah tace"ta tashi daga makaranta amma bata koma gida ba yanzu haka nemanta ake,nan yahau salati yace"tabɗijam to yanzu ko'ina taje amma Sabreena bata yawo Allah yasa dai lfya,amin Baba ya amsa sannan suka koma cikin gari zuciyar kowa aka raye,musamman Baba wanda hankalinsa in yayi dubu ya tashi.

Amma Malam baka ganin muje dajin Manga ko zamuga ko gawartane tunda kaga shi Manga ba ruwansa da mugunta inbade laifi aka masaba taƙarasa zancen tana kuka sosai,Baba wanda idonsa yayi jaa cikin rawar murya yace"bana tunanin zatabi hanyar ita kaɗai gobe zamuje cikin gari mukai rahoto gun ƴan sanda da taimakon Allah dana maigari saimuje atayamu nemanta yaƙarasa zancen da rauni cikin muryarsa.

MAYO-BELWA(Adamawa state)

Wani ƙaton gidane wanda in akacemaka akwai mutum bahaushe a gidan zaka ƙaryata zakayi zaron turawa ne ke rayuwa a gidan,gidane babba wanda ɓangare huɗu ne acikin gidan kowanne da suna a maƙale a jikin building ɗin ɓangaren amma ɗaya acikinsu yafi girma sosai,a ƙofar gun an rubuta Mr and Mrs Hydar da alama ɓangaren iyayen gidanne,sai wani an rubuta Sabeer's palace  ɗaya kuma an rubuta visitors place sai ɗaya kuma wanda babu komai rubuce a gun,baban ɓangaren nashiga wanda ƙofarma parlourn ma abun kallone shiga nayi don bama idona abinci,babban parlour ne wanda aka narka dukiya akanta sai furnitures da'aka zuba masu tsada cofee colour,jikin bangon kua duka walpaper ne(sabon abinda ake mannawa a bango kanar paint mai design amma shi takarda ne,,sai wani ƙaton hoto mutane huɗune ajiki wannan matar da yarinyar sai wani guy wanda shima yana kama dasu amma yafisu kyau kamar wani mace sai wani mutum wanda dagani kaga mahaifinsune sunyi kyau cikin kaya iri ɗaya duka suna dariya,komai dai masha Allah,wata dattijiwa ce zaune mai kimanin shekaru 50 hamsin sai wata ƴar budurwa mai kimanin shekaru 18 sha takwas tana zaune agefenta kamarsu  harta ɓaci don kamar an tsaga kara sai dai kawai matar ra nunama yarinyar shekaru,fararene sol dasu ga hanci da idanu ga bakinsu ƙanana pink shar ga gashi gar gadon baya,a hankali tace"Ammi wai yaushe Yaya zai daina fushi yadawo gidanmune wlh am missing him wlh zanmaki kuka,cikin takaici tace"Sabeer bansan meyake damun saba sam nakasa gane wane irin mutum ne shi,Abbu wanda yake sauƙowa yace"yatafi ni damuwa tama bamusan inda yajeba yau kimanin shekara ɗaya kenan  bamu sake jin ɗuriyar saba ga wannan yarinyar Aisha ta tada hankalinta ta ƙwallafa rai akansa amma yabarta ni sam nakasa gane me Sabeer ke nufi, nadamu sosai da rashinsa nasan shima duk inda yake yana kewarmu amma taurin rai da zurfin cikinsa ya hanasa zuwa mude fatanmu yana cikin ƙoshin lfya yaƙara sa zancen damuwa akan fuskarsa don yana tsananin son Sabeer don yaro ne mai shiga rai.

ME YA SAKA SABEER YABAR GIDA.

AI'NA YASAMU SUNAN MANGA.

MIYE ALAƘAR SHI DA AISHA WACCE ABBU YA AMBAYA.

Zaku samu amsarkune idan kukaci gaba da bibiyata a shafukana na .

Wattpad da kuma Blog, ɗina wanda ku duba a sama akwai yadda zaku shigesu,karku manta comment ɗinku da sharhi dashi kaɗai zaku biyani don Novel ɗina kyauta ne,ku danna vote sannan kuyi read a wattpad saina jiku Ngd sosai masoya.

Vote pls and follow

SABREENA SABEERWhere stories live. Discover now