page 64.

540 76 16
                                    

AKWAI ƘADDARA 64.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Haka gidan yake cika da baƙi ƴan uwa da dangi har makotanta sun shigo mata barka.

Ranar suna yarinya taci suna Nanah kamar yadda asalin mai sunarta take.
Baban Nanah da mahaifiyarta sunyi mamaki abinda basu taɓa tsammanin ba, har gida suka zo suka ga takwarar ƴarsun suka saka mata albarka tare da gudunmawa na akwati cike da kaya banda na uwa da uba da suka haɗa.

Murshida da farko kin karɓa tayi dan cewa tayi ita ta matane dan son da take mata duk da bata taɓa ganinta ba.
Dakyar ta amsa, haka Aunty Ani ma tayi nata kayan, Mama ma haka sai da tayi nata kayan goyon, daga ƴan Indonesiya da Nijar ma ta samu kyautattuka, ranar Murshida taga gata, ƴan uwanta ma mata kowacce sai da tayi ƙoƙarin bata wani abu, Batul ce tsaye kan komai ita da Rufaida.

Anci ansha anyi taro lafiya an watse lafiya in ka kalli ahlin ba zaka ce wani abun ya taɓa faruwa dasu ba.

Bayan an gama taro washegari an gama gyara mata gidanta da komai aka haɗa mata kayanta dana Nanah suka tafi gida wanka, duk da Bagus ya nuna baya son hakan amma abu da al'adar kaka da kakanni yasa ya barta.

Tun da ta koma take samun kulawa ita da Nanah daga ɓangare da dama, kullum sai yazo haka Sanjidah da Aunty Ani suna zuwa bayan kwana biyu, a haka suka cinye sati uku.

Saura sati biyu ta gama wanka ta samu ƙiran Batul cewa an fara cika DE(Direct Entry), tayi murna sosai ta ƙirasa yana office ya gama aiki yana shirin fita ya samu ƙiranta.

Bayan ya ɗauka ta sanar dashi cewa.
"Kasan wani abu?"

"Ah a sai kin faɗa." Ya amsa mata bayan ya buɗe motarsa ya shiga.

"An fara cika DE." Tace cike da murna.

"DE? Menene haka ban fahimceki ba?"

"DE Direct Entry mana zuwa University, ina son cikawa, ina da burin karatu tun ba yanzu ba Allah bai yi ba."

Shuru yayi na sakwanni har sai da tace.
"Kana jina?"

"Eh ina jinki, amma yanzu ina hanya inna koma gida ko in nazo za muyi magana."

"To shikenan Allah kaimu."

Ameen yace yan kashe wayar ya kunna motar yana barin harabar asibitin.

Suna gama wayar ta tashi ta hargitsa ɗakin Mama neman credentials nata, bayan ta samu ta gyara mata dan faɗa Mama ta mata da tazo ta samu haka.

Ranar haka har dare tana zaman jiran ƙiransa da zuwa amma shuru har tayi bacci, washegari ma shuru data ƙirasa bai ɗauka ba sai kuma ta damu lafiya, saƙo ta tura masa cewa mai yasa bai ɗauka ba, ganin sauƙon ya sashi aika mata da saƙonsa cewa yana lafiya aikine yasha gabansa, bayan ta karanta ta masa fatan alheri ta bari sai nan da kwana biyu kuma zata ƙirasa.

Haka ta cinye sati tana jiran ya mata magana shuru, ganin ta bar maganar ya sashi cigaba da ƙiranta, ganin bashi da niyar mata maganar ya sata masa magana ranar yazo da dare suna ɗakin da Baba ya gina dan baƙi, yana zaune da Nanah a hannunsa yana mata wasa, yarinya tayi bulbul abinta kamanninsa da ita sai bayyana yake.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now