page 28.

481 90 4
                                    

AKWAI ƘADDARA 28.

  "Shikenan zan maka magana zuwa anjima." Ta samu kanta da faɗan hakan dan ji tayi tana buƙatar jin menene zai faɗa mata.


"Ok sai naga kiranki."

Bayan sunyi sallama ta shiga tunanin yadda zata nemi hanyar haɗuwa da shi, banda Batul ba wanda zai taimaka mata da wannan aikin, tashi tayi ta fita ta nufi hanyar ɗakinsu, sallama tayi ba kowa ɗakin hakan yasa ta shiga ciki, rana ta farko da wayonta ta shiga ɗakinsu.

Bacci ta hangota tana yi ta lallaɓa ta ɗaka mata duka a baya, a firgice ta tashi tana neman gudawa.

Dariyar mugunta Murshida ta saka har tana neman faɗuwa, ganin Murshida yasa Batul ɓata rai tana sosa gurin.
"Ban yafe ba muguwa." Ta faɗa mata.

"Kar ki yafe ɗin." Ta faɗa tana sakin wani dariyar.

"Menene kuma zaki tasheni ina bacci na."

"Taimako na zo nema gurin ƴar'uwata." Murshida ta faɗa tana yin yanayin tausayi.

"Menene?"

Anan Murshida ta faɗawa Batul abinda ke tafe da ita da ta taimaka mata suje gidan Aunty Sameera ta mata magana za tayi bako.

Tsaki Batul tayi tana kwanciya.
"Wato sai buƙatar ki ya tashi zaki nemeni, bazan je ba ai kema kina da kafa kije ki sameta."

Ganin da gaske Batul take ya sata faɗin."Kar kimin haka sister ke kaɗai gareni wa zai taimaka min in ba ke ba."

"Ke kam kin cika daɗin baki, da roƙo kika fara da kin samu kuɗi."

"Naji koma mainene ki faɗa na amince."

Tashi Batul tayi tana mita haka Murshida ta tsuke baƙinta tayi shuru a zuciyarta tana cewa zata ramane.

Hijab nata tasa ta fita suka nufi gidan Aunty Sameera, sun ci Sa'a sun tararta tana nan, anan kuma suka fara inda indar sanar mata, dariya tayi tana cewa.
"Na fa gane nufinku baza a zo a gaisheni ba sai buƙatarku ta taso."

Cike da kunya suka kasa magana dukkansu dan tana da gaskiya.

"Shikenan tinda kun ki magana zan fita yanzu, da karfe uku zan dawo wacce take da baƙon in na dawo sai tazo dan bazan iya barin mace dana miji su kebe a gidana ba bana nan."

"Toh shikenan." Batul ta faɗa suna tashi, dan gaskiyarta ne ko su rashin son keɓewar su biyun yasa gwara su nemi gida.

Suna isa gida ɗakin su Murshida suka shiga anan Batul tasa Murshida a gaba akan ta sanar mata me yake faruwa tsakaninta da Bagus.

Ganin yanzu ba abinda zata ɓoye mata yasa ta sanar da ita komai har da zuwan iyayensa gobe.
Sosai Batul ta mata murnar hakan.

"Amma sister ina son karatu mai zurfi ban shirya aure yanzu ba."

Bata rai Batul tayi tana cewa.
"To uwar yan boko shi auren yana hana karatune? Ke rufin asirin mace ɗakin mijinta, kiyi aurenki in yaso kici gaba da karatunki a gidanki in mijinki ya yarda."

"Allah yasa ya amince."

"Ameen." Fadin Batul suna ci gaba da hiransu da tattaunawa akan bikin su Batul da ya rage saura sati biyu.

Har ƙarfe biyu suna zaune a ɗakin anan su kaci abinci su kayi sallah Mama ta dawo Batul ta musu sallama ta basu guri.

Bayan tama Mama sannu da zuwa take tambayarta.
"Mama ina su Khausar?"

"Ke da na barki dasu ko sun tafi gidansu Asma'u."

"Zai iya yiwa." Murshida ta fadi hakan tana son faɗawa Mama cewa Bagus zai zo anjima akwai maganar da zai faɗa mata.

"Mama!" Ta ƙira sunanta kuma tayi shuru.

"Na'am ya akayi?"

Dakyar ta iya cewa. " Mama dama wai... Amm cewa yayi anjima zai zo akwai maganarta da zai faɗamin mai muhimmanci."

"Da da yake zuwa ku ke haɗuwa da sani na."

Girgiza kanta tayi tana yin ƙasa dashi.

"To Allah kawoshi lafiya." Mama ta faɗa, anan su Khausar suka dawo tare da robar ice cream a hannunsu.

"Waya baku?" Mama ta tambayesu.

"Uncle Mustapha."
Laila ta faɗa tana miƙawa Murshida, girgiza kai tayi tana cewa.
"Bana sha." Tace tana tashi ta hau saman gado.

Da kallo Mama ta bita dashi tana mamakin ƙiyayyar da take ma Mustapha banda abunta ma ta kusa rabuwa dashi, tausayinshi ma ya kamata.

Wayarta Murshida ta ɗauka ta tura mishi saƙo, lokacin da saƙon ya shigo wayarshi yana tare da iyayenshi da tin da ya zauna maganar fatar baki bata haɗasu ba, hatta yaran sun fara ganewa da akwai abinda ke faruwa a gidan, bayan ya karanta ya tura mata saƙon inshaAllah yana tafe zuwa lokacin.

Karfe uku da mintuna goma ya sameshi a layin unguwar su, ya ƙira wayarta.
"Gani nazo."

"Ka shigo cikin gidan Aunty Sameera."

"Wayece haka?"

"Gidan nan dai." Ta faɗa dan bata san ta ya zata kwatanta ba.

"Ok gani nan shigowa." Ya faɗa yana yanke wayar, a ƙofar gidan yayi parking motarshi ya fito ya shiga cikin gidan tare da sallama, yaron Aunty Sameera ne ya amsa mishi yaro ɗan shekara takwas.

Ƙarasawa gurinshi yayi. "Kai ne mijin Aunty Murshida."

Murmushi yayi da jin sunan da yaron ya bashi sosai sunan ya karɓu a cikin zuciyarsa.

Kai ya ɗaga masa yana cewa.
"Eh ni ne ita ta faɗama?."

"Ah a cewa tayi in kai ka can falon."

"To muje." Bagus ya faɗa yana kama hannun yaron har cikin falon baƙi kafin ya fita da gudu ya sanarwa Murshida ta fito.

Da sallama ta shiga cikin falon da ta gani yayi mata kaɗan ji take tamkar ta koma take ji.

Amsa mata sallamar yayi yana cewa.
"Bismillah shigo mana ko dai kunyarce?"

Bata yarda ta haɗa idanu dashi ba ta shiga tana neman gurin zama da sauri dan wani muguwar kunyarshi ne ya kamata.

"Ni kam wannan kunyar da ban san shi ba ya fara ishana."
Ta tsinkayi muryar Bagus na faɗa mata.

Kanta ta ƙara sunkuyarwa baƙinta na rawa tace.
"Ya aiki ya su Aunty Ani."

"Duk lafiya lau, ya mutanen gida?"

Kai ta juya mishi alamar Lafiya lau.

"Sai kuma ki ka ji na nemi muyi magana mai muhimmanci kafin iyaye su shiga maganarmu."

"Eh." Ta faɗa mishi tana ɗago idanuwanta ta kalleshi idonshi cikin nata hakan yasa ta sadda kanta ƙasa.

Murmushi yayi yana cewa.
"Idanuwan nan da ake min rowar ganinsu wataran zan kallesu har na gaji."

Ba tace komai ba ta murmusa cike da kunya.

"Maganace mai muhimmanci Seyyidah tsakani na dake, bana son rushe miki farin ciki a rayuwarki ina son ki samu farin ciki tamkar kowa shin zaki amince da ni a duk yanayin da kika tsinci soyayyarmu?".

Keep liking.

fateenaguary

Ummuh_

Thank you for the liking ❤️

Pharty Bb.

Nagarta Writers Association.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now