page 15.

624 102 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 15.

Wayar ta fara bincika rabonta dashi yafi sati Uku, wajen ƙira ta shiga missed call ne barkatai ba adadi, lambar da ta gani ana yawan ƙira take son kira amma tana tsammanin bama kudi a wayar, hakan yasa ta shiga duba asusun wayarta.

Kafin ya nuna mata aka sake ƙira, kamar karta ɗauka sai kuma ta danna tare kafawa a kunnenta tana sallama.

Daga can ɓangaren sa ajiyar zuciya ya sauƙe jin ta amsa ƙiran, amsawa yayi tare da furta sunan da ya daɗe da bata.

"Seyyidah."

Jim tayi na jin an ƙirata da sunan da ba mai ƙiranta dashi, da kyar ta samu ta furta.
"Na'am."

"Why ba kya ɗaukan ƙira na, ke har yanzu baki ɗauke ni matsayin dana ba kaina a wajenki ba wanda nake fatan gaba kaɗan ya wuce haka ?" Bagus ya faɗa daga can bangarensa da damuwa a tattare da shi.

Ta fa gane muryar da duk maganganun sa, mai kuma ya ƙira ya faɗa mata banda duk abinda suka mata, tin lokacin bai nemeta ba sai yanzu, ta dalilinsa komai ya faru.
Bata jin zata iya masa rashin kunya amma ta ɗaure ta furta.
"Mai kake bukata daga gareni da zaka saka damuwa a ranka in har ban ɗauka ba, duk abinda ya shafeku dana gidanku na barshi."

"Abinda nake buƙata in nazo zan fada miki, yanzu faɗamin mai yasa bakya picking c....."

Da sauri ta tareshi.
"Ka zo ina?"

"Gurinki mana i missed you." Ya bata amsar da bata son ji.

"Bana so bana so dan Allah." Ta ƙarasa maganarta haɗe da roƙo.

Murmusawa yayi jin duk ta rikice daga maganar zuwa, shi kuma baya jin zai fasa niyyarshi.
"Gurinki zan zo Seyyidah, kin san dai nasan gidanku, ko yaushe nayi niyar zuwa zan zo kawai dai bana son zuwa ba tare da izininki ba, So yanzu ki samin rana."

Rau rau tayi da idanu kamar yana gabanta ta.
"Dan Allah dan Allah ka bari bana son abin magana, mai kake tsammanin mutane zasu ɗauka."

Kafin ta rufe bakinta ya tari maganarta.
"Ko mai zasu ɗauka su ɗauka bazan fasa niyata ba."

"Niyar mai? Dan Allah mai kake buƙata? Mai kake so." Ta faɗa kamar tayi kuka.

Dariyarshi ya danne yace.
"In na zo za kiji komai har abinda baki tambaya ba."

Murshida kam kuka take son yi jin yaki jin maganarta ba dan tana jin kunyarsa ba da ta tsula mishi rashin mutumcin da take ma Mustapha, amma ya za tayi dashi.

"Kina jina Seyyidah."
Sai lokacin maganarshi ya fargar da ita.

"Uhm." Ta iya furtawa har muryarta ya karye.

"To ya muke ciki?" Ya faɗa da murmushi.

'Dagaske yake'
Zuciyarta ta bata amsa, numfashi ta sauƙe.
"Ka bari in nasa lokaci zan faɗa ma."

"Na baki lokaci, in kuma kika wuce to zaki ji sallama a gidanku." Yace da ita.

Kashe wayar tayi kafin ya ƙarasa maganar shi, hawaye taji sun biyo kumatunta, to mai yake shirin faruwa, mai zai faɗa mata, mai yake bukata daga gurinta.

Kwanciya tayi ta shiga tunani taji alamar shigowar saƙo ta jawo wayar ta buɗe.
'Please ki daina nisa da wayarki i will call you anytime."

Ƙaramin tsaki taja ta kashe wayar gaba ɗaya.

Bangaren Bagus kam dama ya ɗaukarwa kanshi alƙawarin ko mai zai faru sai ya jure dan samun nasara a wannan yaƙin.

Daren ranar sukuku ta kwana har Mama na lura da ita amma ta bar abun a gajiyar da suka yi na rabon katin biki.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now