page 57.

436 91 2
                                    

AKWAI ƘADDARA 57.

Baki ya buɗe yace.
"Zan faɗa maka iya abinda na sani amma kamin alƙawari ba zaku ce da sa hannuna a cikin komai ba sannan zaku taimaka mini na bar garin dan an min kashedin kar na faɗa in har nayi ƙoƙarin faɗa zan iya rasa raina.

"Na amince sannan zanyi ƙoƙarin taimaka maka dan samun tsiratar da ranka, faɗa min."

Shuru yayi yana zubawa Abubakar ido har sai da ya ɗaga masa kai alamar gaskiya ya yarda dashi kafin ya buɗe bakinsa ya fara magana.
"Ina son Murshida tin ranar da na zo unguwarsu gaban yayana da zama, na ganta na fara sonta, duk in da zanbi na nuna mata hakan abun bai yu ba dan bata taɓa so na ba, tasha faɗa mini ta sha nuna mini amma hakan bai sa na hakura ba har rana ɗaya na ji labarin aurenta da ɗan gidan Alhaji Mudassir, na ji kishi sosai hakan yasa na dinga mata barazana, a cikin haka na haɗu da wata mata ko in ce Hajiyar da ko sunanta ban sani ba tace in taimaketa ta taimake ni na samu auren Murshida, in da ta nemi na bata lambarta, idona rufe yake da buƙatar aurenta hakan yasa na bata tin lokacin bamu ƙara haɗuwa ba sai waya da muke yi, amma ni tun lokacin dana tabbatar an ɗaura auren Murshida na hakura da ita na san ta mini nisa."

Shuru yayi bayan ya gama maganar yana sauraran abin da Abubakar zai ce, ganin ya gama ya sa Abubakar cewa.
"Ka tabbatar da abinda ka faɗamin gaskiyane?"

"Eh hakane komai."

Numfashi Abubakar ya sauƙe yana cewa.
"Shikenan ina zuwa." Ya tashi yana fita a ɗakin, ɗakin da Bagus yake ya shiga ya zauna yana cewa.
"Kaji komai ba, nasan kana da tambayoyi muje ka masa."

Kai ya ɗaga masa yana tashi suka fita, bayan Abubakar ya shiga shima Bagus ya shiga yana bin Mustapha da kallo, matashin Saurayi da ya bata wayonsa a idonsu, Abubakar ne ya fara magana.
"Mustapha ga mijin Murshida nan, yaji duk abinda muke tattaunawa akai yaji ya amince da bukatar ka sannan zai maka tambaya."

Da kallo Abubakar yake bin Bagus dashi dole Murshida taƙisa in har tana da irin wannan, kallon da yake masa yasa Bagus cewa.
"Simcard naka kawai zaka bani tun da kace kana da lambar matar."

"Bayan na ƙirata mun yi magana jiya ɗazu da safe na karya akan zan saya sabo gudun kar ta nemeni."

Iska mai zafi ya furzar jin abin da yace simcard nashi kaɗai zai basu daman cigaba da bincike amma yasan mai za suyi, zasu so sanin wacece wanna matar, duban Mustapha yayi yace.
"Dole kayi welcome back ko dan cigaba da binciken mu in kuma ka nuna ah a zamu cire hannun mu cikin lamarin ka da matar kuma za muci gaba da binciken mu har sai mun gano gaskiya, sai ka zaɓa ranka ko taimakon mu."

Da sauri Mustapha ya tari numfashinsa yana rufe bakinsa yace.
"Na amince zan yi wallahi, ni dai kar ku bar ni da ita dan ina hango rashin tsoron Allah a tattare da ita "

"Shikenan sai gobe." Ya faɗa yana fita Abubakar ya bi bayansa a falon suka tsaya Bagus yace.
"Gobe a haɗasa dasu Abbaty sai su rakasa, na kula yafi tsoron matar akan mu."

"Hakane amma wannan ko wayece zamu ganota da izinin Allah, zan aiko Abbaty da abincinsa anjima"

"Nagode abokina." Bagus ya faɗa.

A nan su kayi sallama kowa ya nufi gidansa Bagus na ma Abubakar gorin yaƙi zuwa gidansa, dariya yayi yace yana jira su gama cin amarci zai kawo Madam ɗin sa da boy ɗinshi.

Daya isa gida sai da yayi knocking ta leƙa ta buɗe masa, tana ganinsa ta maƙalƙalesa tana masa sannu da zuwa, zama yayi saman kujera yana bin kwalliyarta da kallo yace.
"Kinyi kyau fa matar."

"Nagode mijin." Tace tana ƙoƙarin tashi ya riƙeta.
"Tsaya in biya kwalliyar mana."
Tsayuwa tayi ya haɗa bakinsu guri guda ya fara ya ba kwalliyar tana tayasa.
Bayan sun nutsu ya shiga ya watsa ruwa da taimakonta suka fito suka ci abinci kafin su zauna hira a falo.

...

Washegari sai da Abubakar ya tabbatar ya turasu Abbaty kafin ya wuce office, bayan sun bincika jakansa suka samu national ID card ɗin Mustapha suka tafi dashi aka musu Welcome back din sim ɗin sa, bayan sun gama suka dawo dashi, shi nan ɗin ma yafi masa kwanciyar hankali sai kaɗaici, yana samun ci da sha.

Da suka tashi daga office nan suka taho bayan sun karɓa sim ɗin a wajen Abbaty suka duba lafiyar shi in da suke ce masa ko zai koma gida yace yafi son nan dan tsiratar da ransa sai kaɗaici yasan zuwa wani lokaci ne.

Bayan fitarsu Abubakar ya miƙa masa sim card ɗin.
"Dole a samu mai bincike, masani a harkar computer ya bincika mana sim ɗin duka biyu na Murshida da wannan na Mustapha da waccan layin da ake turo sakon ko za'a samu lambartan saboda kasan dai in anyi welcome back numbers suna ɓata."

"Hakane zuwa gobe zan samu Noori ta mini wannan aikin aikintane."

"To shikenan Allah kaimu Allah yasa mu samu wani abun."

"Ameen Ya Allah, ka gaishe da my boy."

"Zai ji zai kawo maka wuni." Abubakar ya faɗa yana murmushi ya shiga motarsa, shima Bagus murmushin yayi yana shiga motarsa suka bar gidan.

..

Kafin ya wuce office washegari ya ƙira Noor ya faɗa mata zai zo hakan yasa yana fita gida ya wuce ya samu iyayensa suka gaisa kafin su keɓe da Noor ya mata bayani yana miƙa mata simcard ɗin dukka biyu da lambar da za ta masa bincike a kai, karɓa tayi kafin ya wuce office.

Wuni tayi kulle a ɗakin karatunsu da laptop gabanta tana bincike akan simcard ɗin, ta wahala sosai kafin ta samu wani bayani, har saida ta da haɗa da ƙiran lecturer nasu ya mata wasu bayanai.

Da ya baro office Abubakar ne ya wuce duba Mustapha duk da ya bar su Abbaty su kula dashi su bashi abinci sannan su zauna dashi dan ɗebe masa kewa, daya dubasu ya wuce gidansa.

Bayan ya isa gida ya ƙira Noor a waya yace su haɗu a ɗakin karatunsu, anan ta samesa yace mata ta samu wani bayani.
Dogon numfashi ta sauƙe bayan ta zauna tace.
"Yaya abin da wahala kasancewar wannan sim ɗin sabone komai ya goge misali su numbers din ciki ba lalle a gano suwa suke kira ba, wannan kuma sim ɗin na ƙasa, ba  zamu iya bincike ba sai in har yana aiki, amma na saita komai da idan har an kunna zai nuna mana location ɗin da yake."

Keep liking and commenting ❤️

Wattpadian ghosts readers ina ganinku😂🙄 a cigaba da kallo ba liking ba comments 🥺🤪

Pharty Bb
Nagarta Writers Association

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now