page 63.

543 72 2
                                    

AKWAI ƘADDARA 63.

Pharty Bb
Wattpad phartybb.

A haka rayuwa taci gaba da tafiya har aka shiga satin bikin Noor da Fadhlan, wasu sun zo daga Indonesiya wasu sun zauna dan jiran amarya, ƴan Niger sun zo hatta dangin Mamma sun zo dan nuna kara, Mamma taso zuwa Abba ya hanata sai da tayi ta roƙarsa kafin ya barta, a ranar da tazo ta samu Aunty Ani tayi ta rokarta yafiyarta, ganin yadda duk ta koma ga kuma karamci da taimako data mata ya sata yafe mata tace ta nemi yafiyar Bagus da Murshida da su Muhsina.

Ranar farko su kayi kamu washegari ɗaurin aure, bayan ɗaurin aure maza su kayi reception, washegari aka yi walima aka yi wa'azi sai bayan kwana biyu aka fara shirin kai amarya, tasha kuka tamkar ranta sai fita dan kusan suma ta musu tace ita ta fasa auren sai da Abba yayi mata faɗa sosai Bagus yayi ta lallashinta kafin ta yarda ta daina kuka.

Sanjidah, Raudah, Bagus sai mutum takwas ƴan Niger suka kaita, aka bar Aunty Ani da Murshida da cikinta haihuwa ko yau ko gobe dan ta shiga wata tara.

Tin da suka rakasu airport suka dawo take jin ciwon baya, da suka dawo ta lallaɓa tayi wanka ta kwanta ko abinci bata samu daman ci ba, bacci mai daɗi ya fara ɗaukarta taji wani azababben ciwon marar da ya sata dira daga kan gadon ta tsaya, wayarta ta ɗauka taga biyar na yamma, bakin gado ta zauna jin ya lafa, haka ya dinga mata bayan mintuna goma goma har magriba tayi in da wani azababben ciwo ya riƙeta ta kasa ko tashi sai cije baki take tana damƙe hannuwanta.

Ganin magriba har ta gota bata ji motsinta ba ya sata dubawa ko lafiya ta nufi ɗakinta ta tura ƙofar tana leƙawa, ganin halin da take ciki ya sata ƙarasawa wajenta da sauri tana tambayarta.
"Lafiya Murshida? Mai yake damunki? Kina cikin wannan halin baki sanar dani ba."

"Aunty ciwon marane ke damuna amma zuwa anjima zai bari dan yana zuwa yana dawowa."

"Naƙuda ko ciwon mara, tashi muje asibiti." Aunty Ani ta faɗa tana tashinta suka fita.

Dakyar ta sauƙa downstairs ta zaunarta saman kujera ta koma ta ɗauki hijab dinta da ƙaramin kits da suka haɗa kayan buƙata ta sauƙo ta ɗagata suka fita, Murtala ta kwala ƙira ya ɗauko motarta ta sakata ciki kafin suka fita.

Basu tsaya ko ina ba sai asibiti dai-dai lokacin Dr Aisha ta tashi tana shirin tafiya, ganinsu ya sata dawowa ta taimaka musu zuwa part din ƴan labour, ganin Dr Aisha yasa aka karɓe ta da sauri zuwa labour room, bayan shigarsu Dr da zata karɓi haihuwar ta sanar da Aunty Ani haihuwace amma karta damu zata haihu lafiya.

Bata yadda da hakan ba dan tasan haihuwa dai haihuwace duk zafinta ɗaya ne dan ma ta lura yarinyar akwai dauriya, bata zauna ba ta fita ta saka Murtala ya kaita gidansu Murshida ta sanar da Mama.
Bayan Mama ta sanar da Baba suka tafi har da Khausar da Laila.

Suna isa zamansu da kusan awa ɗaya Dr ta fito daga ɗakin ta sanar dasu ta haihu lafiya ana gyarata ita da baby zuwa mintuna kaɗan za'a fito da ita a kaita ɗakin hutu zuwa gobe in an duba lafiyarta dana baby za'a sallamesu.

Murna da hamdala suka dinga yi tare da mata godiya, cikin mintuna talatin aka gangaro da ita zuwa ɗakin hutu, ita ɗaya a ɗakin sai gadon baby, ciki suka shiga suka zauna tana bacci hakan yasa suka ɗauki babyn suna kallo tare da yin addu'a.

..

Tin da suka isa ya huta yake ƙiran wayarta bata ɗauka ba hakan yasa ya kira Aunty Ani itama bata ɗauka ba, Abba ya ƙira yana tambayarsa, bai san komai ba saboda yana gidan Mamma da yanzu ba laifi yana sake mata, duk da tayi nadama amma hakan bai saka ya yarda da ita ba, hankalinsa ya kwantar masa yace zuwa safe zai duba ya gani ko lafiya, da haka su kayi sallama.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now