page 24.

467 77 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 24.

Tin kafin ta gama maganarta yaji duniyar na juya mishi, ba dan ya dafa hannunsa da motarsa ba da ya faɗi ƙasa dan yadda yaji ƙafafuwanshi sun kasa ɗaukarshi, lumshe idanunsa yayi ya buɗe ya zuba mata su.

Tana gama faɗar maganarta ta saka hannu ta goge hawayenta da suka zubo a kumatunta ta ɗago tana kallonsa.

"Ko zaki faɗamin dalilinki na faɗar haka." Da kyar bakinshi ya buɗe ya iya furta mata hakan.

Girgiza kanta tayi ƙasa, bai ƙara cewa komai ba ya buɗe motarsa ya shiga yana barin gurin, da kallo ta bishi har ya bacewa ganinta kafin tana jan kafufunta ta koma gida.

Da taimakon Allah ya isa gida, ko faka motar bai yi mai kyau ba ya kashe ya fita ya shiga falo, duk iyayensa na zaune bai bi takansu ba ya wuce ɗakinshi ya kulle kanshi, saman gado ya zube yana maida numfashi.

Mai yasa sai shi? Laifin mai ya aikata da hakan ke faruwa dashi? Ta yaya zai fara warware wannan abin? Ta ina zai fara binciken hakan? Mai yasa sai lokacin da yake tsaka da cimma burinshi sai komai ya tarwatse?.

Ɗinbim tambayoyin da suka cika masa kai da har suna neman sashi ciwon kai, tashi yayi daga kwancen da yake ya ɗaga hannunshi sama.
"Ya Allah gani nan bawanka ina neman afuwarka da gafarar ka abisa laifi ko wani kuskure dana aikatama ban sani ba ka yafemin, Allah kai ka jarabceni da jarabtarka, ban fi ƙarfin jarabawa ba Allah ka sassautamin ka kawamin agaji cikin lamurana."

Bayan ya gama addu'ar ya shafa yana kwanciya, idanuwanshi ya rufe kamar mai bacci wanda a zahiri tunani ya faɗa.

.....

Tana komawa cikin gida, ɗakinsu ta wuce a yadda ta bar Mama haka ta dawo ta sameta, hijabinta take cirewa taji Mama tace.
"In kin gama kizo muyi magana."

To tace bayan ta gama cirewa ta linke ta maida ta dawo kusa da Mama ta zauna.
"Gani Mama."

Kallonta take kamar ba zata yi magana tace.
"Kinyi kuka ko?"

Tambayar da Mama ta mata shi ya ƙara sawa taji zuciyarta ya karaya, idonta ya cika da hawaye.

Ganin bata da niyar bata amsa ya sata fuskantar ƴartan sosai dan so take suyi maganar da zai amfane ta.
"Murshida kina sonshi ko?"

Kanta ta ɗaga ta kalli Mama kafin ta sunkuyar ƙasa, in har ta mata karya bata sonshi ta san ƙarya ne kawai.

Murmushi Mama tayi ta fara mata magana cikin nutsuwa.
"Murshida kenan, bazan hana abinda Allah ya haɗa ba, Allah ne ya haɗaku, na so na rabaku ganin ke da shi ɗin ba ku dace ba amma in nayi hakan na tauye muku hakkin da ina tsoron Allah ya kamani dashi, zan tayaku da addu'a Allah ya zaɓa muku alherinsa, sannan bana son wannan tsaye tsayen a kofar gida gudun magana, fatan kin fahimce ni."

Murshida tin da Mama ta fara maganarta take kallonta har ta kai karshe bata ce komai ba.

"Da ke fa nake." Taji Mama ta faɗa tana zungurin kanta.

Murmushi tayi tana mai da kanta ƙasa a kunyace tace.
"Naji Mamana nagode sosai da kika fahimce ni."

"Ba dole na fahimce ki ba, soyayya na nuƙurƙusar yarinyata tana neman hallakarmin ke." Faɗin Mama da murmushi ganin ƴartan ta murmusa wanda rabonta da ganin hakan tin jiya.

Kunya taji ya kamata ta sunkuyar kanta ƙasa tana cewa.
"Mama..!" Sai kuma tayi shuru.

"Faɗi maganarki." Mama tace ganin baƙin Murshida akwai magana.

A hankali ta faɗawa Mama dalilin zuwansa na yau da kuma abinda tace masa. Shuru Mama tayi tana mamakin Murshida da har zata hakura da nata farin cikin dan farin cikinta.
"Ki ƙirashi kice masa kin amince amma za'a ma babanki magana tukunna, ya baki lokaci."

"Shikenan Mama." Ta faɗa tana tashi a gurin, murmushi Mama tayi ta bita da kallo, ko da wasa aka ce mata Bagus zai so Murshida ko ita zata soshi ba zata yarda ba, ikon Allah kenan.

Wunin ranar a ɗaki ya wuni dan ko iyayenshi ba suga gilmawarshi ba, sosai Aunty Ani ta shiga damuwa hakan.

Ba abinda ke ɗagashi daga kwancen daga sallah sai sallah, wani azababben ciwon kai ke damunshi dalilin damuwar da yake ciki.

...

Da dare suna zaune suna cin abincin ita da kannenta, kaɗan taci ta tsame hannunta tana duban Khausar tace.
"Khausar ina wayata da muka haɗa kuɗi dake muka saya."

Dariya tayi jin maganar Yayartan tasan da gayya tayi maganar.
"Yana saman akwatina."

"Allah kin isheni yarinyar nan, kin bi kin sawa mutum waya a gaba, Ni nama kwace abuna."

Khausar dai ba tace komai ba dan jin bambamin yayartan.

Bayan ta ɗauki wayar ta kunna, lambar shi ta lalibo sai lokacin taji tana son yin saving amma ta rasa sunan da zata sa masa, hakan yasa tasa farkon sunanshi da babban baƙi B.

Bayan tayi ta shiga gurin tura sako ta tura mishi sakon 'Na Amince.'

Shine kawai abinda ta rubuta ta tura misa tana sauraron amsarshi.

Yana kwance bayan ya gabatar da sallar isha'a yaji alamar shigowar saƙo wayarshi, kamar bai zai ɗauka ba ya lallaba ya jawo wayar ya kunna.

Tashi yayi sosai yana karanta saƙon yafi sau biyar kafin ya fita gurin ya danna mata ƙira.

Dama ta tsammani ci ganin ƙiranshi a lokacin hakan yasa bata bar gurin ba, wayar ta kurawa ido tana ganin yana ƙara har ya kusa yankewa a hankali ta amsa ta kafa a kunnenta tare da sallama.

Bai iya amsawa ba ya watsa mata tambaya.
"Dagaske kike Seyyidah." Burinshi tace eh.

Kai ta ɗaga tana cewa. "Eh." Kamar yana gabanta.

"Allahamdulillahi ya Allah Nagode maka, Nagode miki Seyyidah Murshida, hakika yau naji kalma daddaɗa da na daɗe ina fatan ji, Allah baki farin ciki kamar yadda kika sani."

"Ameen, baka amsa min sallamata ba."

"Walaikis Salam Malama Seyyidah Murshida."

Dariya tayi jin yadda ya wani har haɗa sunan kafin tace.
"Amma hanzari ba gudu ba."

Shuru yayi yana sauraronta kafin yace."Ina jinki."

"Mama tace abi komai a hankali, bayan hakama saboda gaggawa aikin shaiɗan ne, za'a ma baba magana sai ya bada lokaci sai in faɗa ma."

Gaskiya ta faɗa kam fan haka yace.
"Hakane gaskiyarki Mama, zan faɗawa Abba yasan da maganar ne zuwa lokacin."

"To shikenan, sai anjima."

"Korata kike?" Ya tambayeta yana kwantar da murya.

Shuru tayi kamar ba ita ta gama zuba zance yanzu ba.
"Tambayarki nake, ni na ƙira ai ni ya kamata na kashe ko? Kin san ma menene?"

Girgiza kanta tayi tace."Uhm uhm."

"Da gobe sai dai kizo asibiti gaisuwa."

A tsorace tace. "Subhanallahi Waye ba lafiya?"

A shagwaɓe yace. "Ni mana kin haddasamin ciwon kai, yanzu ma sai nasha magani may be ma jinina ya hau."

"Allah sawwaƙe kasha magani ka kwanta zai bari."

"Ameen Beautiful."

Kashe wayar su kayi a tare kowannen su na sauƙe ajiyar zuciya.

Sallah ya tashi yayi raka biyu ya godewa Allah, kafin yasha magani ya kwanta cike da farin ciki, ya daɗe yana burin wannan ranar tin bayan abinda ya faru ya cire tsammani da ganin wannan ranar.

Pharty Bb.

Nagarta Writers Association.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now