page 51.

551 83 8
                                    

AKWAI ƘADDARA 51.

  Bayan ya gama cin abincin sa ya kwashi plates din ya kitchen, ɗakinsa ya shiga yayi brush kafin ya kashe wutar falon da komai na kayan wuta ya fito ya nufi ɗakinta, duhu ya gani hakan yasa yayi amfani da hasken wayarsa ya haska, can ya hangota duƙunƙune cikin bargo, bakin gadonta ya ƙarasa ya zauna addu'ar bacci yayi ya shafa ya shafa mata ya gyara kwanciyarsa ya shige cikin bargon, matsawa yayi kusa da ita, kwanciyarta ya gyara mata ya sata cikin jikinsa yana hamdala a ransa daya basa ita.

Mutsu-mutsu take ya ƙara matseta yana mata raɗa a kunne.
"Shishh yi baccinki ba abin da zan miki."

Dif ta dakata kamar wanda aka yi ruwa aka ɗauke, kunyar maganarsa yasa ta ƙara runtse idanunta kamar yana ganinta.
A haka bacci ya ɗaukesu cikin jin daɗi, musamman Bagus dan ya cire tsammani da ganin wannan ranar.

Da asubabi bayan ya farka yayi alwala ya tasheta sai da ta shiga toilet kafin ya tafi masallacin da ya ji ana ƙiran sallah, tana fitowa bayan ta gabatar da sallah ta koma saman gado, da ya dawo shima kwanciyar yayi bacci ya ɗaukesu.

Karfe goma yaji ana knocking, tashi yayi ya zareta jikinsa a hankali yana fita, kofar ya buɗe sai da suka tsorotasa ƴan gidansu ne Noor, Sanjidah dasu Izziddeen, Fadhlan.

Sanjidah ya kawai rankwashi kai yana mita, yana shirin kaiwa Noor, Fadhlan ya shiga tsakaninsu.
"Kana taɓa min mata zan rama."

Baƙi ya buɗe cike da mamaki yana kallonsa ya kalli Noor da ta rufe fuskarta dan kunya bai ce komai ba ya matsa suka shiga cikin falon kallonsa ya mayar kan Izziddeen da yaga bashi da walwala, shine ƙarshen shiga ya riƙo hannunsa.
"Lafiyar ka kuwa brother?"

"Lafiya amma akwai maganar da za muyi anjima."

Da to ya bisa suna ƙarasawa cikin falon idonsa ya kai kan Sanjidah dake ƙoƙarin shiga ɗakin Murshida da sauri yace.
"Ke Sanjh ina zaki je?"

Juyowa tayi tana kallon yayantan tace.
"Aunty zan ƙira tazo su gaisa."

"Ni na saki? Dawo nan." Ya faɗa yana ƙarasa wajenta da saurinta ta bar gurin, ya shiga ɗakin, yadda ya barta haka ya dawo ya sameta, ƙarasawa bakin gadonta yayi ya zauna kusa da kanta, hannunsa ya ɗaura saman fuskarta ya ƙira sunanta
"Seyyidah tashi."

Jin muryarsa yasa ta buɗe idanunta tana tashi da sauri sai lokacin ta ga hasken rana da bata ma san garin ya waye haka ba.

"Munyi baƙi fa su Izziddeen ne da Sanjh sun zo gaishe ki."

Kamar za tayi kuka ta dubi jikinta tace.
"Gashi ko wanka ban yi ba."

"Kiyi sauri ki shiga ki fito."

Sauƙa tayi tana faɗawa toilet, saman gadon ya gyara yana fita ya wuce ɗakinsa dan shiryawa shima.
Bayan ta gama ta kasa fitowa tsoronta kar dai yana nan, kofar ta buɗe kaɗan ta leƙa nan ta gani baya cikin ɗakin, da sauri ta fito ta sawa kofar lock ta fara shiryawa, riga da skirt ta saka na less ja da baki ɗinkin ya zauna a jikinta mai ta shafa ta fesa turare tana fita.

Anan ta tarar shima ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya, guri ta samu ta zauna suka fara gaisawa, ƴan matan ba ruwansu nan ta saki jikinta da su suka yi ta hira ta tashi dan nema musu abin da za susa a baƙinsu.
Kitchen ta nufa ta tsaya dan bata san mai zata basu ba, fridge ta buɗe ko zata samu abu, da mamakinta ta samu ruwa katan katan da kayan lemo, diɓa tayi ta kai musu ta zuba musu ba laifi sun sha suka ci gaba da hiransu karshe ma ɗakinta suka shige suka bar mazan a falo.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now