page 60.

515 78 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 60.


Washegari safiyar bata tashi da wuri ba sai wajen karfe goma, tana buɗe idanunta taga rana ya hasko ɗakin ras, gefenta ta kai dubanta taga shima baccin yake, da saurinta ta diro a saman gadon ta fita falo, abun mamaki ta tarar domin Khausar ta gyara ta share sai kamshin turaren wuta yake, cikin kitchen kuwa ta gama girkin tana wanke abubuwan da tayi amfani, ganin hakan yasa bayan sun gaisa ta koma ɗakin shima lokacin ya farka.

Wanka ta shiga kafin ta rufe ƙofar ya shiga ciki shima ya rufe kofar, ɓata rai tayi tana cewa.
"Wanka fa zanyi."

"Yi miki zanyi ai." Za tayi magana ya kunna shower ruwa ya fara sauƙa a jikinsu, dole bata so haka ta tsaya su kayi tare suka fito, shiryawa su kayi kafin su fita falon, break fast ɗin da Khausar ta dafa suka ci dukkansu a saman table ɗin, bayan sun gama tace masa Mama zata neme su Khausar ya kamata su tafi, cewa yayi su shirya zai sauƙesu gida daga nan zasu wuce gida akwai magana mai muhimmanci da za'a tattauna.

Bayan su Khausar sun shirya gaba ɗayansu suka fito suka rufe gidan suka fita, a hanya ya tsaya ya musu tsaraba duk da Murshida ta hanasa yace ba ruwanta, dole taja bakinta tayi shuru, bayan sun sauƙesu ya basu suka karɓa suna masa godiya kafin su wuce gida.

A harabar gidan yayi parking, bayan ya parker suke fito suka nufin hanyar falon, ba kowa cikin falon hakan yasa suka nufi ɗakin Aunty Ani, da fara'arta ta taresu, bayan sun gaisa ya sanar da ita akwai baƙi da zasu zo za a tattauna wata magana mai muhimmanci.
Da mamaki take dubansa za tayi magana ya fita, hakan yasa ta tambayi Murshida ko tasan wani abu akai, nan tace ba abinda ta sani.

Suna zaune haka har karfe biyu bayan sun gabatar da sallah ya shigo yace suzo, hijabinta Aunty Ani ta ɗauka Murshida kuma ta gyara zaman mayafinta suka fita, har falon Abban su ya tsaya yace Aunty Ani ta shiga akwai baƙin da zasu shigo yanzu zai jirasu, ba musu ta shiga, anan ta tarar Abba da Mamma sai Abubakar da bai jima da zuwa ba, guri ta samu ta zauna tana tambayarsu ko sun san wani abu akai, nan suke ce suma kawai ya nemi ganinsu ne basu san dalilin ba.

Bayan Aunty Ani ta shiga ya juya yana kallon Murshida yace.
"Zauna Beautiful." Kujeran dake ajiye a wajen ta zauna tana zama taji shigowar mutane, ƙarasawa Bagus yayi gurinsu ya shigo dasu, Abban Nanah da Muhsina da mijinta sai ƴarsu ƴar shekara biyu tana gudunta, bayan sun shiga yace Muhsina ta tsaya wajen Murshida.
Bayan Abbansu ya shiga da mijinta, Bagus ya gabatarwa Murshida Muhsina, da murmushi ta gaisheta itama Muhsina ta amsa tana murmushi har Murshida ta karɓi yarinyartan.
Suna cikin haka Abban Zainab da Ammah da kuma yayun Zainab suka shigo, bayan sun ƙarasa suka gaisa yace Abban Zainab ya shiga cikin falon da yayun Zainab ita ta zauna, da to suka bisa dan duk wanda yasan abinda yake shiryawa baya mamaki sai Murshida da da idanu take binsu.

Ana cikin haka Mustapha ya shiga jin muryarsa yasa Murshida tashi da saurinta ta ƙarasa wajen Bagus tana rukumkume sa, sanin hakan yasa ya riketa a jikinsa har Mustapha ya ƙaraso.
Bayan sun gaisa yace ya zauna anan yaja Murshida su kayi ɗakin su Noor, zaunarta yayi yace ta kwantar da hankalinta wannan ba Mustapha data sani bane, ba dan ta amince ba ta yarda ta zauna ya fita.

Yana isa wajen ya tarar yanda ya barsu, cewa yayi su zauna za suna jin duk abinda ake tattaunawa daga nan in lokacin da ya kamata suyi magana yayi sai su shiga, da to suka bisa ya shiga ciki da sallama mutanen gurin suka amsa masa.
Guri ya samu ya zauna kusa da Abubakar da yayun Zainab, duk da an gaisa sai da suka sake sabon gaisuwa, Abba, Mamma, Aunty Ani da idanu suke binsu dashi musamman Mamma da taga yayartan da mijinta.

Nutsuwa Bagus yayi ya buɗe bakinsa ya fara magana in da kowa ya maida hankalinsa ga abinda yake faɗa.

"Abba mahaifi gareni da bani da tamkarsa, ya riƙe ni ya soni tamkar ɗan cikinsa, bai taɓa nuna mini wani abun ba cewa bashi ya haifeni ba har ila yau, ban san da mai zan saka masa ba sai fatan Allah saka masa da gidan aljanna."
Bayan Bagus ya faɗi haka ya kalli Aunty Ani yana ci gaba da maganarsa.
"Aunty Ani, ko in ce mahaifiyata da Ƙaddararta yasa bata taɓa nunamin cewa ita ta mahaifini ba sai dan wasu dalilai da suka taso hakan ya bayyana."
Murmushi yayi mai ciwo da in ka duba fuskarsa zaka hango tsantsan baƙin ciki da dacin maganar da zai faɗa yace.
"Sai wacce ta ɗauke ni matsayin ɗa ta zame mini uwa ta nuna mini soyayya da gata tamkar yadda ko wani yaro yake bukatar hakan, sai dai ashe hakan duk a baki take bai kai zuciya ba, muguwace, azzaluma bak'ar macijiya"

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now