page 50.

563 77 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 50.

Hannunta ya kama yana binta da kallon tayi masa kyau sosai, simple makeup ne a fuskarta, da bai saba ganinta da kwalliya ba sai yaga ta canza masa gaba ɗaya.

Izziddeen ne ya leƙa yace su fito, fitowa su kayi yana riƙe da hannunta suka nufi filin gurin gefe da gefensu mutane ne a zaune suna masu tafi wasu na ɗaukarsu a hoto, a tsakiyar gurin da aka tanadarwa amarya da ango zasu zauna suka nufa ya zaunarta ya zauna gefenta.

Anan suka fara gabatar da shagali in da dangin ango zasu bawa amarya kyautattukan da suka tana da mata haka dangin amarya ma zasu bada kyauta a ango, amma kasancewar dangin amarya ba tasu al'adar bane kuma basu san da hakan ba yasa suka ce su bari su zasu bawa amarya.

Manyane suka taso suka fara bada tasu kyautar, kowa in ya bada sai an ɗaga an gani, daga manya sai samari da ƴan mata hatta ƙananan ƴara sun bada nasu, kyauta kam amarya sai da ta rasa ina zata saka su aka fara jirgewa a gefe, hakan da suka yi Bagus yaji daɗin sa sun nuna masa shi ɗin jininsu ne.

Bayan bada kyauta aka fara ɗaukar hotuna, bayan an gama musu aka ɗauki amarya da ango sunsha kyau ko ina yana maƙale da ita duk kunya ya isheta, daga nan aka fara ciye ciye, an sha anci anyi taro lafiya aka fara watsewa wajen karfe sha ɗaya, abin gwanin sha'awa ba kiɗe-kiɗe ba rawe rawe duk da wani kiɗa yana tashi a hankali ba wanda yayi gigin zuwa yin rawa dan ba hanya abu ga manya.

Yana ganin ana fara tafiya ya riƙo hannun matarsa suka fita, binsa kawai take, wajen motar da suka zo yayi da ita bayan ya buɗe mata ta shiga ya zagaya ya shiga ya tada motar suna ƙoƙarin barin gurin yaji tace.
"Khausar fa da Izziddeen."

Bai kulata yaci gaba da tuƙinsa sai da suka fita a gurin hankalinsa naga hanya yace.
"Na ma Izziddeen magana ya tabbatar ya dawo da ita gida."

Ba tayi magana ba ta mai da hankalinta a titi a zahiri kuma zuciyarta ne yaci gaba da bugawa dan tunawa da abin da ya mata jiya.

Katse shurun nasun yayi ta hanyar faɗin.
"Kinga al'adar su ko? Ya burge ni ya burge ki?"

"Eh ba wani rawe rawa da kiɗe-ƙide."

"Abin da ya fi burgeni ma."

A haka yana janta da hira dan ganin ta saki jikinta ya dinga yi har tazo ta sake tana bashi amsa, a haka suka isa kofar gidansu ya faka motar tana ƙoƙarin fita yace.
"Tsaya mana."

Ba musu ta dakata tana gani ya cire tissue ya saka hannu ya ɗago fuskarta, a hankali ya fara goge mata kwalliyar fuskarta, da ido take bin sa dashi yanda yake gogewa yana kashe mata jiki gaba ɗaya, tas ya goge fuskarta ya bar jambakin leɓɓenta.

Buɗe gilashin motar yayi ya jefar yana juyawa ya kalleta.
"Kin fi kyau haka, bana son kwalliyar nan nafi son ganin matata da natural beauty nata."

"Nima bana so Batul ta matsamin aka yi duk ya takura mini, ni jambakin ma ya isheni."
Ta faɗa masa tana ƙoƙarin ɗaukar tissue ta goge ya riƙo hannunta.

"Wannan aikina ne, bari kiga."
Ba tayi aune ba ya haɗa bakinsu guri ɗaya, tas ya shanye jambakin kafin ya sake mata bakinta yana kara janta jikinsa.
"Ji naje kamar in wuce dake a biyo ki da kayanki gobe."

Bata iya bashi amsa ba sai ƙoƙarin raba jikinsu take tace.
"Ka buɗe min na fita za'a neme ni."

Fita yayi ya zagaya ya buɗe mata kofar tana saka ƙafafuwanta zata sauƙar ya tsungunna kan kafafunsa ya kama kafarta, takalman ƙafarta masu tudu ya cire mata yana kama yatsun kafarta yana ja yana matsawa a hankali.

AKWAI ƘADDARAजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें