page 21.

557 130 3
                                    

AKWAI ƘADDARA 21.

"Wannan tamkar ba Seyyidah Murshidan dana sani ba, wacce na sani ina hango rashin tsora da jarumta a tattare da ita, menene ya faru?"
Maganar da Bagus yake faɗa mata kenan dan shi mamakin canjawarta yake.

Tabbas hakan take amma ta rasa dalilin da tin lokacin da yazo mata da buƙatar neman soyayyarta taji ta canza a kanshi, duk lokacin da ta ji muryar shi takan nemi maganar baƙinta ta rasa, balle yau da suka kasance tare su biyu.

"Bayan na saurari amsata da nake ta muradin ji, nasan akwai dimbin tambayoyi da za su biyo baya daga gurinki, hakane?
Bagus ya ƙarasa maganar da neman amsarta.

Sai lokacin tayi ƙoƙarin ɗaga kanta tace. "Eh."

"Ta ina zamu fara?" Ya tambaye ta ganin ta fara buɗe baki ta amsa mishi.

"Duk ta inda kaga dama." Ta bashi amsa dan buƙace take da ta saurari abubuwan da take son ji.

Nustuwa yayi ya fara magana.
"Bari ni in fara, Allah ne ya Ƙaddarar haɗuwarmu har naji ke ɗin wata a bace tattare dani, hakan yasa na ɗauki matsayin ƙanwa na baki, to ban san kin wuce hakan ba sai da idanuwa suka rasa ganinki kunnuwana suka rasa jin muryarki, anan na tabbatar dagaske kin samu gurbi cikin zuciyata, ban kuma yarda da hakan ba sai da Aunty Ani tazo min da maganarki na yarda, a ranar da ta min maganar kwanan nayi ina addu'a da neman zabin Allah inda washegari na yarda da zuciyata ke din take so, shi yasa na tattara na zo miki da bukatata wanda ban san ta ina zaki ɗauki maganar ba, fatan kin samo min amsa."

Ya  ƙarasa maganar yana jiran amsa, ɗago ido tayi ta kalleshi tana kawarwa gefe, murmushi yayi yace.
"Idanuwanki sun bani amsa, menene tambayarki game dani wanda kike so ki sani kuma?"

Ranar da take jira yazo, amma ta rasa ta ina zata fara, ta ina zata soma ma bata sani ba kwata kwata.

"Ke nake saurara Seyyidah Murshida." Ya faɗi hakan dan ganin tayi shuru kuma yasan dole akwai tambayoyi tattare da ita.

"Ban san ta ina zan fara ba." Ta faɗa da sanyin murya.

"Ki fara ko ta ina." Ya bata amsa dan baya son ta kwari kanta ko kaɗan  a kanshi.

"Ka san aikine ya kai ni gidanku kuma ban san komai tattare da ahlin ba, ina son sanin hakan."

"Kina son sanin ni waye?" Ya tambaye ta.

Kai ta ɗaga mishi da sauri, shurun kusan mintuna uku yayi har yasa ta kallesa ko maganarta ya ɓata mishi rai.

Murmushi ta gani kwance saman fuskarshi, baya rabuwa dashi in ba yana tare da damuwa ba.

"Sunana Bagus Azeez kamar yadda na taso naji ana faɗamin, ɗa na fari ga Alhaji Mudassir Timber da Hajiya Maryam, Noor, Sanjidah y'ay'an Aunty Ani ne, ni da Raudah ya'yan Mammane, Mahaifina sanar sai da kataki yake shi yasa ake ce masa Alhaji Mudassir Timber, wadda Allah ya bukasa masa yake fita kasashe da yawa, Nayi karatuna daga primary har degree na anan ƙasarmu Nigeria duk da mahaifina yaso nayi a wata ƙasar Mamma ta nuna bata so, hakan yasa ina gama degree ya turani karo karatu akan abinda na karanta fannin ido."

Jin yayi shuru ta dubeshi za tayi magana ya rigata.
"Na gaji."

Murmushi tayi tace.
"Kasha ruwa."

Kallon inda aka jera mishi ruwan yayi ya dawo da kallonshi gareta.
"Bana shan kayan gwangwani ko na kwalba, na fi son matata ta min da hannunta nasha na ji dad'i nasa mata albarka ita ma taji daɗi."

Kanta ƙasa ba tace komai ba ta kawar da maganar ta hanyar faɗin.
"Dangin ku fa?"

"Na wajen Mamma suna garin Kaduna, dangin Abba kuma suna Nijar, dangin Aunty Ani ne ban taɓa gani ba ban kuma san in da suke ba, bama haɗuwa da kowa in ba biki ko wani taro ba."

Gingina kanta tayi alamar ta gamsu, amma har yanzu akwai tambayar da yake cikin ranta ta rasa ta ina zata mishi ita

"Na san akwai sauran tambayoyi tattare dake amma kina shakkar tambaya ko?"

Ta ya a kayi ya san hakan?
Da sauri ta ɗaga kanta ta kalleshi ta daga masa kai.

"Na taɓa miki maganar da yake tattare da tambayar da zaki min ki na bukatar amsa ko? Ya tambaye ta.

Kai ta ɗaga mishi da sauri, murmushi yayi mata.
"Zan baki amsoshin tambayoyin ki amma ba yanzu ba sai lokaci yayi ni da kaina zan baki amsarsu a dai-dai lokacin da kike buƙatarsu, dan haka kar ki damu kanki ni dai fatana a riƙeni amana."

Murmusawa tayi kanta ƙasa tana wasa da zoben hannunta da Bagus ya bata.

"Za'a riƙeni?" Ya tambaye da zolaya.

Hannu tasa taja gyalenta ta rufe fuskarta tana murmushi.

Murmushinta kaɗai ya bashi amsar da yake bukata na samun gurbi cikin zuciyarta, hannunsa ya kai kan agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa biyar da arba'in.

"Kinga lokaci yaja, sai wani lokaci zan dawo?"
Bayan ya faɗa yana tashi, ba tace komai ba ta tashi tabi bayanshi yana fita.

"Ƙiramin sister muyi sallama dan ba ƙaramin taimako ta mini ba."

Juyawa tayi ta shiga falon ta shaidawa Batul ta zo suyi sallama, hijabi ta saka ta fito su kayi sallama ta koma.

A bakin get ta tsaya tace masa."Sai anjima."

Juyawa yayi da mamaki yana kallonta ."Anan zaki tsaya."

Kai ta daga mishi alamar. "Eh"

"Ok please wayarki, kina ajiyewa kusa da ke."

"Zan ƙoƙarta inshaAllah."

Sallama ya mata ya fita ta koma ciki, falon gidan ta shiga ta samu Batul na zuba kayan wata leda a saman kujera, duka ta ɗaka mata a baya tana zama.

"Kin shammace ni sister."

Batul gurin ta sosa ta kai mata duka ta kauce tana dariya.
"Zan rama, dan ma na miki taimako, kuma kin san dai na girmeki amma zaki iya ɗaukan hannu ki dake ni."

"Wannan kuma kayi tayi."
Murshida ta faɗa tana gyara gyalen kanta tana ci gaba da faɗin."Wai wannan kayan fa na sayarwa ne Aunty Sameera"

"Ban sani ba." Batul ta faɗa tana ɗaukan turare biyu data gani an rubuta sister, sauran kuma agogone na mata mai kyau da turaruka uku da suke da shegen kamshi ko ba'a faɗa ba tasan na wa yake nufi, kwasa tayi ta zubawa Murshida kan cinyarta tana cewa.
"In kunyi waya ki min godiya."

Please keep liking, your like will give me more courage 🤗

  Idan bakwa liking sai in ga kamar bakwa jin daɗin littafin, littafin na da tsawo yanzu mu kayi somin taɓi.

Zan buɗe group a whtspp ga masu buƙatar shiga ciki kyauta ne.

Pharty Bb.
Nagarta Writers Association.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now