page 39.

443 79 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 39.


Sanadin shaƙuwata da Nanah kenan ko in ce mafarin soyayyar mu, dan daga tutorial soyayyarmu ta samo asali, kunyarta da nutsuwarta yasa na kamu da son Nana anan na gano ƴar Kaduna ce.

Idan mun gama karatu ko wani abubuwan mu mu kan haɗu da Nanah mu yi namu karatun tare daga nan mu zarce hiran soyayya."

"Dan Allah kalmar nan ta isheni ka bani labari straight forward." Murshida ta faɗa tana katseshi ta ɓata rai.

Murmushi Bagus yayi yana mamakin ta ko mai na kishi ga wacce bata raye.
"Kina kishina ne?"

Kanta ta juyar gefe tana turo bakinta bata an kara taji sauƙar yatsa saman leɓɓenta an riƙe, da tsoro ta juya har lokacin yana riƙe da leɓɓen kamar za tayi kuka ta kasa magana.

"Ban miki warning ba."

"Ka yi." Ta iya faɗa mishi da kyar jikintane ya fara rawa ta fara jin wani tsoro na shigarta dan bata taɓa yarda wani namiji ya riƙe mata ko da hannunta ba sai shi lokaci ɗaya ya kai nashi hannun zuwa ga bakinta ya dille mata bakin, ɗazu kuma ya riƙe mata hannu yanzu kuma ya taɓa.

Sakin bakin yayi yana murmushi dan ganin duk jikinta ya fara rawa yace.
"Kin katse mana labarin."

"Kaci gaba." Ta faɗa ƙasa ƙasa.

Gyara zama yayi yana duba agogon hannunsa yaga uku da mintuna biyar gani yayi suna da isasshen lokaci, hakan yasa yaci gaba da faɗin.

"A cikin haka har muka ɗauki shekara uku muna tare duk da haka soyayya mu bata hanamu karatu ba, a haka muka kammala karatun mu ka fito da sakamako mai kyau, bayan gamawarmu muka harhaɗa komai namu muka dawo gida.
Anan na tarar da ƙanwata ƴar shekara biyu Raudah, dana tambayi yar waye aka ce min Mamma, sosai nayi mamaki da murnan hakan dan iya sanina tin haihuwata bata ƙara samun wani cikin ba amma ban nunawa kowa mamakina ba na boye hakan, na fara nunawa ƙanwata da muke uwa ɗaya uba ɗaya soyayya.

Bayan dawowana Abba ya nema min aiki a asibitin abokinsa da sai an kai an kawo ake zuwa, bayan fara zuwana aiki kullum muna waya da Nanah in da nake tabbatar mata da jadda da mata ina sonta kuma zan ma iyaye magana.

A cikin haka watanmu uku da dawowa na samu Mamma da maganar Nanah bata kawo komai a ranta ba ta sanar da Abba kowa yayi murna a gidan har Aunty Ani itama ta nuna farin cikinta.

A haka manya suka shiga maganata da Nanah, aka saka bikinmu wata biyar masu zuwa, Noor ta fi kowa murna yayanta zai yi aure tamkar sauran ƙawayenta, Sanjidah ma haka.

Bayan watanni abuwawa da yawa sun faru ciki har da ranar da bazan taɓa mantawa ba ranar da nake ƙiranta da ranar ƙaddara duk da ko wani bawa rayuwarsa AKWAI ƘADDARA, hakan nima ta zame mini.

Aurena da Nanah saura sati biyu na wayi gari da saƙonta da ya girgiza ni ya girgiza ahlina, hakuri take bani akan ta fasa aurena amma kuma tana jaddada min cewa tana sona son da bata taɓa ma kowa ba.
Na shiga ruɗani, bayan na sanar da ahlina a ranar na kama hanyar Kaduna, ina zuwa ban zarce ko ina ba sai gidansu da kyar Nanah ta fito.

Ina roƙarta ina mata magiya ta sanar dani dalili taki sai ma kuka da ta saka tana cewa ita kawai auren ne ta fasa, jin maganganunta nake tamkar tana watsa min ruwan zafi amma na bar abin a yarinta ya za'a yi biki saura sati biyu amma tace ta fasa, hakan yasa nayi zuciya na bar gurinta, in da nace sai dai tayi biki kam sai anyi tin da saura sati biyu, kuma tace tana sona aure ne kawai baza tayi ba, in anyi auren ai zata zauna.

Tin da na koma ban ƙirata ba duk akan nayi fushi burina kawai lokacin yayi a ɗaura mana aure in sauƙo mu yafi juna mu gina rayuwar aurenmu.
 
Dawowata da sati ɗaya na samu ƙiran mahaifin Nana ƙiran gaggawa har da mahaifina, tin da na samu labarin ƙiran zuciyata ta kasa nutsuwa, jikina duk yayi sanyi har ina cewa in dai akan maganar auren ne zance a ɗaga in kuma sun matsa kamar yadda Nanah ta ce ta fasa sai in hakura dan bana son tauye mata haƙƙinta.

Tin da muka doso hanyar gidansu na fara hango taron jama'a, bayan shigar mu muka tarar da abin da ya sani shiga tashin hankali, kin san mai na tarar?

Bagus ya tambaye Murshida muryarshi ta karaya, girgiza kanta tayi dan bata da karfin maganar, jikinta yayi sanyi da jin labarin ga zuciyarta da ke cike da tausayinsu su dukkansu biyun, idanunta kuwa cike suke da kwallan da take sharewa akai akai.

"Gawar Nanah na tarar Seyyidah."

"Ta rasu?" Ta tambayeshi cike da tashin hankali.

Kai ya ɗaga mata yana ci gaba da cewa.
"Nanah ta rasu ta barni ta barmu gaba ɗayanmu, ashe ita taji a jikinta ba zaman aure tsakanin mu shi yasa tace ta fasa auren, haka muka kai Nanah gidanta na gaskiya muka dawo, na zama tamkar ba ni ba.

Sai lokacin naji ashe dare ɗaya tayi jinya washegari ta rasu, ta rasu tana neman gafarana, ta tafi ta barni ina fushi da ita, nayi ta roƙar Allah ya mata rahma da gafara na kuma yafe mata, duk da ni na dau fushin na ɗaurawa kai na amma ta ɗaurawa kanta laifi.

Ranar sadakan bakwai washegari Mahaifin Nanah ya matsamini na koma gida saboda aikina kasancewar Abba washegari ya koma, haka na tattara na dawo da kewar Nanah.

Tin da na dawo na dukufa akan aikina ba garin Allah da zai waye rana ta faɗi ban tuna Nanah ba, haka har aka yi sadakar arba'in din Nanah anan na samu Mahaifin Nanah da ya ban auren ƙanwar Nanah mai suna Muhsina.

Bai yi wani dogon nazari ba kasancewar ya sanni ya ɗauki auren Muhsina ya bani, dana koma gida na sanar da iyayena, sun nuna sunji daɗin hakan amma duk da Mamma sai da tayi magana akan dana bari abu ya ɗan shekara, anan Abba yayi ta lallaɓa ta ta amince ya ƙira mahaifin Nanah ya masa godiya da kuma za'a zo a saka rana kasancewar itama yarinyar ta amince.

An saka ranar aurena da Muhsina wata takwas kafinnan rasuwar Nanah yayi shekara, mun shaku da Muhsina kasancewar halinsu ɗaya da Nanah da kuma kammannin da suke yasa na ɗauki soyayyar Nanah na ɗaura mata.

Ana cikin wannan yanayin har muka ci watanni bakwai, cikin wata ɗaya da zamu shiga na bikinmu na samu saƙon Muhsina, kin san mai saƙon ya kunsa?"

Bagus ya tsagaita yana duban Murshida da gaba ɗaya fuskarta ya jike da ruwan hawaye har idonta yayi ja dan kuka, kai ta girgiza masa tana sa bayan hannuwanta ta goge fuskarta.

"Saƙonta na tattare da barazana na cewa ta fasa aurena in kuma na matsa akan sai na aureta zata kashe kanta tamkar yadda take zargin yayarta Nanah ma kashe kanta tayi."

Keep liking.

Pharty Bb.

Nagarta Writers Association.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now