page 6

664 119 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 6.

"Aunty Ani."
Zuciyarshi ta bashi amsa, tabbas in Mamma zata ɓoye masa abu Aunty Ani ba zata iya ɓoye masa ba, yana jinta a zuciyarsa tamkar ita ɗin wani sashine na sa.

Da dimbin tambayoyi ta iso gidansu bayan ta gama aikinta, da shigarta gidan ta tarar Ameer na jibgar kanwarta Laila, matan gidan kowa na kofar ɗakinsu na kallo ba mai yunkurin hanawa, bata kula su ba ta wuce ɗakinsu ta tarar Mama bata nan sai Khausar dake ta kuka ganin ana dukan ƙanwarta, hijab nata ta cire kafin ta fito a ɗakin in da ta barsu nan ta fito ta samesu, tana zuwa ta ɗagashi daga kanta kafin ta bashi marin da ya sashi fasa ihu a gigice ya nufi mahaifiyarsa.

Hannun ƙanwarta ta ja ta kaita bakin randarsu ta wanke mata fuska suka koma ɗaki, tana ji Babar Yara na ta bambami ko a ƙwalar rigarta yau ƴan faɗan basa kanta yanzu ma ganin za'a cutar kanwarta ya sata rabawa.

Suna shiga tayi ta lallashin ƙanwarta tare da zungurin kan Khausar.

"Matsoraciya kina kallo za'a cutar kanwarki."

Hawaye ta ta share "Ni wallahi Aunty Murshi tsoro nake ji, kinga fa ranar yanda suka tararwa Musaddik."

"Ai duk wanda ya tarar muku In na dawo sai na karyasa, nan gaba in bana nan ko Mama kuje gidansu Asma'u kuyi wasa, kunji?

"To za muje."
Suka faɗa tare, a hankali suke hira suna bata labarin makaranta tana dariya har Mama ta dawo daga unguwar da take ta sameshi.

Da dare suna zaune Murshida ta kalli Mama.
"Mama ya maganar makarantana."

"Murshida mu bar maganar nan kinsan halin mahaifinku bazai taɓa amincewa ba."

"To yanzu Mama haka zan zauna ba karatu." Ta faɗa tana turo baki.

"Allah haɗaki da wanda zai dillemin bakin nan, kiyi aure kawai irin yanda ƴan uwanki za suyi, sati mai zuwa za'a kawo goron tambayar Fauziyya da Aneesa, an kawo na Batul yafi wata uku sanin kan kine, ke bawa yaronnan dama, wai haka zaki zauna min in saki a gaba ina kallo."

Bakinta ta gyara tana cewa.
"Ni Mama daga tambaya, yaronnan bana son shi, su kuma su suka ga zasu iya yanzu, nima ina zaune Allah zai kawo min mijina ko a ƙasar Sin yake."

"Kece Sin ɗin, ai Ni dai na faɗa miki ki cire rai a karatu, in kinyi aure mijinki ya yarda toh, in ko yaƙi ki rungumi na annabawa."

"inshaAllah zai yarda Mama."

"Toh Ameen."

---

Juye juye yake a saman gadonshi bacci ya ƙauracewa idanuwansa kamar ko wani lokaci.
Zuciyarsa fal tunani da yanda zai bullowa lamuransa, shekarunsa talatin da bakwai, yana bukatar yaga nashi ahlin yau ya ƙira gida da iyali mallakinsa kamar kowa, amma abubuwan da bai san ta ina suka faru ba, kuma suka faruwa, wanda kuma za suci gaba da faruwa in har zai ɗago zance abinda ya wuce.
Daren ranar da kyar bacci ya ɗaukesa.

Washegari bayan yayi sallar asuba ya koma bacci kasancewar ranar Lahadi ne ba aiki, bai farka ba sai wajajen sha biyu kasancewar daren jiya bai yi bacci ba, wanka ya faɗa yayi shirinsa cikin kayan shan iska ya fito.
A in da yake tsamanin samun su nan ya tararsu falon Ƙasa, Mamma, Aunty Ani, Zaituna, Noor, Raudah zaune gurinsu ya ƙarasa ya gaishesu kafin kannenta su gaishsa.

"Yarona break fa." Faɗin Mamma.

"A kawomin nan." Ya faɗa hankalin sa na ga Aunty Ani ganin yadda take kallonsa, damuwa ta gani tattare da Bagus, ganin zai fahimci irin kallon da take masa ya sata kawar da idanunta a kanshi tana masa addu'ar samun maslaha a rayuwarsa.

"Noor jeki ɗauko masa." Yaji Mamma ta faɗa da ya sashi kawar da idonsa.

"Mamma sai dai a dafa wani, yayi sanyi zuwa yanzu tin safe fa." Noor ta faɗa.

Da damuwa Mamma tace. "Yanzu kam Baba Saude ta tafi, ki sa ko Murshida ta ɗaura masa."

"Mamma a barshi in babu karku wahalar da kanku." Bagus ya faɗa dan ji damuwarsa tafi yunwar cikinsa yawa.

"To haka zaka zauna da yunwa, tashi Noor jeki faɗa mata, ina kuma za kiyi masa toh."
Tashi Noor tayi ta nufi kitchen.
Cikin mintuna talatin ta soya masa dankali ta haɗa masa da tea ta kawo masa, kaɗan yaci dan baya jin cin abinci.
Hira suke jefa jefa a haka har azahar ya riskesu suka fara ƙoƙarin tashi dan gabatar da sallah. Kaf suka watse.

Wunin ranar basu Murshida da Bagus basu haɗu ba, kuma bai samu keɓewa da Aunty Ani ba.

Washegari ya kama ranar Litinin karfe takwas ya wuce gurin aiki ko breakfast bai yi ba, ƙiran emergency aka mishi, bayan fitowar sa ya aika takeaway.

Wuraren karfe uku ya baro asibiti ya shigo unguwarsu a masallaci ya tsaya yayi Sallah kafin ya ƙaraso gidan, mahaifinsa ya fara tararwa cikin falon ya dawo daga ƙasar daya tafi kwana biyu.
Anan ya zauna suka sha hira har wajajen biyar kafin ya wuce ɗakinsa, ruwa ya watsa ya ɗauro alwala ganin shida ta kusa.

Fitowar sa yayi dai-dai da barinta ta falon, bayanta ya bi jiya da yau kwata kwata bai sata a idon shi ba, motarshi ya shiga ya danna horn mai gadi ya buɗe masa.
A hankali yake tuƙawa har ya iso gefenta, tun dosowar motar gurinta take jin ƙararshi har tsayuwar sa hakan ya sata dakatawa da tafiyarta dan ganin mai tsayuwar.
'Tabbas motarshi ce' Ta faɗa a ranta, gilashin motar ya sauƙe wanda ya sa suka haɗa idanuwa tayi saurin ɗauke nata.

"Shigo na cika alkawarina." Ya faɗa yana leko da kanshi ta bangarenta.

Da mamaki ta kallesa tana ɗauke idonta.
"Wani irin alƙawari kuma?" Ta nemi ƙarin bayani.

"Shigo zan faɗa miki, kinga magriba ta kusa ina son zuwa masallaci."

"Kaje kawai dan ni ban san alƙawarin da ka ke magana a kai ba."

"Allah zan haɗaki da Mamma in baki shigo ba."
Ya faɗa yana lalibo lambar ta cikin wayarsa. Ba tayi tsammani ba taji yace. "Mamma."

Ta d'ayan bangaren ta amsa masa da "Yarona."
Kasancewar wayar a handsfree ya saka taji abinda ta faɗa.

Da azama ta buɗe murfin motar ta shiga ganin hakan yace wa Mamma.
"Na tafi masallaci sai na dawo."

"Shikenan a dawo lafiya."

Kit ya kashe wayar yana ba motar giya, kallonta yayi yanda ta zumburo baki sai abin ya bashi dariya.

Murmusawa yayi hakan ko ya ƙara kular da Murshida.

"Ina za mu bi." Ya tambayeta.

Da hannu ta dinga nuna masa har bayan layin gidansu tace ya isa, bayan ya faka motar ta buɗe.

"Nagode sai gobe." Ta faɗa.

Kanshi ya ɗaga yana cewa. "Gyara bakin kar yayi tsini irin wannan turowan."

Juyawa tayi tana tana ƙara turo shi, ashe ya kula da ita, dariyar yayi sai kuma yaji abin wani iri, motarshi ya ja yana barin gurin.

Please don't forget to like..

Pharty Bb
Wattpad phartybb
Okada phartybb
WordPress www.phartybb.wordpress.com
#comment
#like
#phartybb
#onelove

NWA.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now