page 27.

477 85 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 27.

Kansa ya sunkuyar ƙasa.
"Aunty na rasa dalilin hakan amma yanzu zan sameta in faɗa mata."

"Yafi kam dan taji labari kuma ta nuna bata ji dad'i ba."

"Shikenan bari in je sai da safe." Ya faɗa yana tashi.

"Allah tashemu lafiya."

Bayan ya fita ya nufi ɗakin Mamma, da sallama ya shiga ta amsa ba yabo ba fallasa, ganin yanayinta yasa gaba ɗaya jikinshi yin sanyi.
Bakin gadonta ya samu ya zauna.
"Mamma."

Ido ta ɗaga ta kalleshi bata amsa ba, nashi idanun ya sauƙe ƙasa.
"Mamma na miki laifi ko? Nasan na bata miki rai amma banda kalaman da zan iya ƙare kaina dashi ba sai dai in ce miki kiyi hakuri."

"Iya abinda zaka faɗa kawai."
Kai ya ɗaga mata da damuwa a fuskar shi, ganin yanayinsa gaba ɗaya ya canza ya sata faɗin.
"Nayi mamakin har abu yayi nisa amma ina matsayin mahaifiyarka ka iya ɓoyemin."

Bai ce komai ba dan yasan ya tafka laifi, faɗa ta shiga yi masa ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, sosai ta masa faɗa, ya kuma amsa laifin shi ya bata hakuri har ta sauƙo.

Sai lokacin ta mishi tambayar da ya rasa bata amsa har sai da ta maimaita a ɗan tsawace.
"Ina tambayar ka wacece yarinyar? Yar gidan waye ce?

Shuru yayi ƙasa ƙasa yace.
"Anan unguwar suke layi biyu tsakaninmu."

"Ba unguwar su na tambaya ba waye mahaifinta anan unguwar ɗin."

"Mamma kiyi hakuri da zabin da nayi ba laifina bane zuciyatace ta zaɓa mini ita Seyyidah Murshida ce."

Cike da mamakin da bata taɓa shigaba take dubanshi har tana gyara zamanta ta kasa yarda da abinda kunnuwanta su kaji.
"Dakata wace Murshida, ba dai wacce na sani ba."

Kai ya ɗaya mata zai yi magana yaji sallamar Abbansu a ya shigo, shuru yayi har Abbansu ya shigo, Bagus ya zame daga zaman da yake ya durƙusa saman ƙafafuwanshi ya gaishesa, bayan Abba ya amsa yace mishi yaje ya huta.

Tashi yayi jiki a sanyaye ya fita, bayan fitarshi Abba ya samu guri ya zauna yana kallon Mamma da duk ta haɗa rai.
"Kin bani mamaki Maryam, dan yaro ya miki laifi haka zaki sashi gaba da faɗa maimakon ki mishi nasiha."

"Alhaji raina ne ya ɓaci."

"Duk da hakan." Ya tari maganarta da sauri.

"Shikenan ya wuce." Tace tana yin shuru da baƙinta zuciyarta na watsa mata maganganu iri iri.

....

Ɓangaren Baba washegarin ranar yaje ya samu babban yayansu da shi ɗaya ya rage musu da mai bi mishi mace ya sanar dasu abinda ake ciki.
A nan Malam Umaru yace jibi da yardar Allah zai zo shi ayi magana da iyayen yaron su zo, shi kuma Baba ya ma limamin unguwar su da makota su zo.

Da hukuncin da Malam Umaru ya yanke Baba ya dawo ya ƙira Mama ya sanar mata ta faɗawa Murshida.
Bayan Mama ta faɗawa Murshida ta sanar da Bagus ta tura mishi sakon ta waya, tana turawa ta kashe wayar dan tasan yanzu sai ya ƙirata yayi ta sata kunya.

Yana zaune yaga shigowar saƙonta, buɗewa yayi ya karanta yafi sau goma, bai yarda ba da farko dan gani yake tamkar zolayarshi take, wai yau shine ake maganar aurenshi, abinda ya daɗe da cire rai.

Wayarta ya ƙira yaji a kashe anan ya tabbatar da gaskiyar abin, wato ta kashene dan kar ya ƙira.

Da daren ranar ya sanar da Abbansu, nan Abba ya nuna mishi sun yi magana da yan'uwansa, sannan inshaAllah zai ƙara sanar da yan'uwansa akan zuwan wanda zai kama ranar Lahadi.

Godiya ya mishi yana tashi, daren ranar kwana yayi yana sallah yana kai kukanshi wajen Allah da rokar samun nasara a wannan lokacin.

Washegari ranar asabar bai tashi da wuri ba, ranace ta kasance weekend (hutun ƙarshen mako), banda baccin da yake yi a weekend yau harda baccin da yake ramawa na daren jiya da bai samu yayi ba.

Sai wajen sha biyu da mintuna ya farka, wanka yayi ya shirya cikin kaya marasa nauyi kafin ya fita babban falon gidan, duk ahlin suna falo banda Abba daya fita sanar da yan'uwansa maganar sa su kayi jiya da Bagus.

Bayan ya gaishe da iyayenshi ƙannensa suka gaidashi.
Sanjidah yasa ta haɗa mishi sabon breakfast ta kawo mishi, bayan yaci ya bar falon ganin falon ya zama tamkar wajen makoki, kowa yayi shuru, Mamma na fishi dashi akan abinda ya faru, Aunty Ani kuma bata son saka baƙinta ace zaƙewar yayi yawa.

Nufan kofar baya yayi wajen ƙarƙashin bishiyar da yake zama dan ɗauke kewa, kujera ya jawo ya zauna yana tariyo mishi yanayin da suka gudunar shi da ita a wajen.

Murmushi yayi yana godewa Allah daya jefota cikin rayuwarshi, wayarshi ya ɗauka ya sake kiranta yayi Sa'a ta shiga.

Kasancewar yau weekend bayan su Khausar sun dawo daga islamiyya ta ɗauki wayar ta kunna ko Murshida bata sani ba.

Lokacin da ƙiran ya shigo taga bata san mai sunan ba yasa ta tashi ta shiga ɗaki ta bawa Murshida, karɓa tayi tana amsawa.

"Assalamu alaikum." Ta faɗa daga ɓangaren ta.

"Walaikis salam, mai yasa kika kashe mini waya jiya."
Bayan ya amsa sallamar ya jefa mata tambaya.

"Umm ina wuni?" Ta faɗa dan kawar sa wancan zancen da bata san amsarshi ba.

"Wayo ko?" Ya faɗa dan ya gane nufinta.

Murmushi tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta tamkar yana gabanta tace. "Ah a."

"Lafiya lau nake na sanar da Abba saƙonki amma kafin nan zan so na haɗu dake akwai maganar da za muyi."

Cike da mamaki tace.
"Magana kuma?"

"Yes mai muhimmanci ne."

"Amma ai da ka bari zuwa wani lokaci."

Sarai ya gane nufinta ta bari har iyaye suyi magana a bashi izinin kafin nan, ba zai jira ba, magana ce data shafi farin cikinta da Sadauƙar wa, ba zai tauye mata haƙƙin ta ba, hakan yasa yace mata.
"No Seyyidah maganace mai muhimmanci ki bani dama duka duka ba zai wuce cikin mintuna goma ba zamu gama, in zan samu mu haɗu yau."

"Amma kuma.."

"Please Seyyidah."

Shuru tayi tana mamakin kuma mai Ai faɗa mata, ko dai zai sanar da ita maganar da yace zai faɗa mata in lokacin yayi? Kenan lokacin yayi?

Keep liking..

Pharty Bb.

Nagarta Writers Association

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now