page 45.

455 68 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 45

  Da dare su Abba da Abbaah suna falonsa suna mai da zance yana tambayarsa abubuwan da Bagus ke so da wanda baya so dan ya kula yaron har yanzu bai sake dashi ba.

Bagus, Abubakar, Izziddeen suna bangarensa sosai yaron ya shiga zuciyar Bagus ko dan ya taso bashi da ƙani ko yaya namiji.

Aunty Ani da matar Abbaah suna nata bangaren suna hira sama sama kasancewar ita ba hausa ta iya ba Aunty Ani kuma ta fara manta yaren Indonesiya.

...

"Kasan mai yasa muka zo neman ka?"
Abba ya tambayi Abbaah yayin da suke zaune a falonsa.

Kai ya girgiza masa yana cewa.
"Ah a fatan lafiya kamar yadda nake zaton haka."

"Lafiya kalau, Annisa tin bayan zuwanmu na karshe bata taba kawo min wani zance da ya shafi nan ba hakan yasa muka bar komai, yaron nan tin da ya taso bai taɓa tsammani bani na haifesa ba sai da ya tashi aure."

Da sauri Abbaah yace.
"Aure dai? Me ya faru?"

Murmushin taƙaici Abba yayi yace.
"Sau uku yana neman aure baya samu sai a wannan lokacin ya samu yanzu saura sati biyu iyayen yarinya suka ji bani bane asalin mahaifinsa dalilin da yasa muka zo nan dan ɗaukar ka zuwa Nigeria."

Murmushi Abbaah yayi yana cewa.
"In kuwa hakane ku kwantar da hankalinku dan aure tamkar an yi, za muje Nigeria in gabatar da kai na a garesu harda sauran dangi, gobe zan haɗa family meeting ko dan ya ga danginshi."

"Da kuwa ka masa abu mafi muhimmanci da soyuwa a garesa."

Anan Abba ya kwashe labarin komai a tattare da abin da yake shafi Bagus ya sanar dashi da kuma irin barazanar da matan da zai aure suke tsintar kan su a ciki.

Tausayin Bagus ne ya kama Abbaah duk shine ya jefasa cikin wannan halin.
"Wannan abin yana da alaƙa da maƙarƙashiya, tabbas da sa hannu." Ya faɗa bayan ya gama sauraron Abba.

"Haka kowa yake zargi amma mu dai yanzu burinmu ayi aure daga baya zamu fara bincike."

"Allah kaimu lokacin." Abbaah ya faɗa yana ɗaukar waya ya sanar da yan'uwansa gobe yana nemansu anan ya ƙira familyn Aunty Ani ma ya sanar dasu cewa gobe yana nemansu akwai magnaa mai muhimmanci.

....

Suna zaune suna taɓa hira sama sama Abubakar da Izziddeen ne ma yawancin suke hiran.

Yayi kewarta yayi kewar jin muryarta kwana uku yau, ga kwata kwata ya mance da sayan sabon layi hakan yasa ya ma Izziddeen magana ko zai samu.
"Brother ina zan samu sabon layi ina son ƙiran matata."

"Nima ina buƙatar hakan zan ƙira nawa matar da yarona, zaka ƙira budurwarka dai." Abubakar ya faɗa da sauri.

Harara Bagus ya watsawa Abubakar.
"Ina ruwanka ka samin ido wallahi."

"To ai gaskiya na faɗa."

"Sa ido dai, Izz ina buƙatar sabon layi."

Dariya Izziddeen yayi duk da wani sa'in suna jefa hausa yana fahimtar maganganun su, wayarsa ya ɗauka yana miƙawa Bagus.
"Kayi amfani dashi kafin gobe in nema maka."

Karɓa yayi yana godiya ya ɗauki nasa wayar ya kwafi lambarta.

"Lambarta ma baka riƙe ba lover boy."

"Ka fita ido na Abubakar."
Bagus ya faɗa tare da tashi ya bar gurin, balcony ya nufa yana ƙiranta.

Tana zaune tana zaman jiran ƙiranshi kamar kullum duk ta bi ta damu da rashin Ƙiransa har mama na mata faɗa tana cewa in taji shuru alherine ta kyautata zato.
Ringin biyu ta ɗauki wayar ganin lamba mai +628 tasa a ranta shine ta amsa tana sallama.

Jin sanyayyar muryarta ya sashi sauƙe ajiyar zuciya bayan ya amsa mata ya ce.
"I miss you i miss your voice."

Murmushi tayi tana cewa.
"Ya hanya?"

"Allahamdulillahi mun isa lafiya mun samu kowa lafiya, ya mutanen gida?"

"Lafiyansu kalau, yaushe zaku dawo?"

"Kin yi missing ɗi na?"

Shuru ta kasa basa amsa hakan ya sashi cewa.
"Kar ki damu zaki ganni kafin satin ɗaurin aure, may be zuwa nan da kwana uku mu taho."

"Allah dawo daku lafiya."

"Ameen zan ƙiraki zuwa gobe in na saya layi akwai hira da za muyi sosa wannan na brother na ne kinsan wai ina da ƙani."

"Dan Allah Dagaske?" Ta tambayeshi da mamaki.

"Yes har kama muna yi."

"Ikon Allah kenan."

"Hakane good night beautiful kar mu ƙarasar masa da kuɗi."

Ba dan sun so ba suka kashe wayar ya koma ya bawa Izziddeen wayarsa, a nan ya ce musu bari ya leƙa Aunty Ani akwai maganar da za suyi.

Part din da yake zaton anan take nan ya nufa yaci sa'a tana nan sallama yayi bayan sun basa izinin shiga ya shiga a nan ya faɗa mata yana son magana da ita suka fita suka samu guri.

Shuru yayi ya rasa ta ina zai fara mata tambayar da yake son mata, lura da hakan yasa tace.
"Na san akwai magana a tattare da kai faɗamin menene?"

Kansa ƙasa ya furzar da iska mai zafi yace.
"Aunty ina da tambayoyin da sun shige mini duhu, duniyata a juye take ke kaɗai zaki iya fassaramin ko samar min amsa ki taimaka ki faɗa min."

"Kana son sanin menene dangantakata da kai."

"Eh iya sanina Mamma itace mahaifiyata amma ina ganin abun na neman juyawa zuwa wani abu."

Tabbas ya kamata ya sani amma tana tsoron abinda zai faru? Shin zai karɓe ta? Ko zai ɗaura mata laifi?.

"Ki sanar dani Aunty." Maganar Bagus ya fargar da ita.

Kanta ta sunkuyar ƙasa da kyar baƙinta ya furta.
"Mamma ba ita ce mahaifiyarka ba, ina nufin ba ita ta haifeka ba."

"What! Me ki ke nufi? Mai yasa sai ni? Wacece kuma mahaifyar tawa? Mai yasa kuka rabani dasu? Wannan wace irin Ƙaddara ce ke faruwa da ni?"

Duk dimbin tambayoyi da yake yi tana ji har ya ƙarasa yasa hannuwansa duka biyu ya dafe kansa da yaji yana neman fara ciwo.

Hannunta ta ɗaura saman nashi tana cewa.
"AKWAI ƘADDARA a rayuwar ko wani bawa taka ƙaddarar kenan ta kasance ɓoyayye, ka daina faɗan haka dan Allah shi ya jarabceka da wannan Ƙaddarar duk da ni na jawo ma."

Sai lokacin yayi ƙoƙarin ɗago idanunsa da suka kaɗa ya kalleta yana cewa.
"Bangane ke kika jawo ba? Ki sanar dani me ki ka sani."

Numfashi ta sauƙe tana cewa.
"Bagus Azeez ni ce na jawo ma komai saboda ni ce mahaifiyarka ba Mamma ba."

Pharty Bb

Nagarta Writers Association.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now