page 59.

521 123 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 59.

Da safe karfe bakwai ya tashi dan shiryawa, jin motsinsa shi ya farkar da ita a anan ya sanar da ita Kaduna zai tafi hakan ya sa ta shiga kitchen ta hau haɗa masa break fast, ya gama shirinsa dai-dai ta gama haɗa masa, bayan yaci ta rakasa gar bakin motarsa in da yace ta je gida ta kwana in ba zata ta iya kwana ba, ko ta ɗauko Khausar ta tayata kwana dan sai gobe zai dawo, taji daɗi sosai ko ba komai tayi kewarsu, addu'a ta mishi kafin yaja motarsa ya fita ta koma.
Ya fita ya biya gidan Abubakar da ya damesa da ƙira akan ya shirya, yana isa suka ɗauki hanya.

Tana komawa cikin gidan tattarewa tayi ta share tayi goge gogenta har ɗakunan su sai da ta gyara musu duk da ba wani dattine dashi ba, wanka tayi ta saka kayanta kala biyu a jaka kafin ta fito falon tayi breakfast, agogon ta kalla taga sha ɗaya da mintuna, jakanta ta ɗauka ta kashe komai na wuta ta kulle falon ta fita ta kulle gidan gaba ɗaya ta nufi bakin titi dan neman abun hawa, bata wani jima ba ta samu ta shiga tana faɗa masa in da zai kaita, har kofar gidansu ya kaita ta sallamesa ta fito ta shiga gidan da sallamarta.

Kowa yayi mamakin ganinta sai binta suke da ido, gaishesu tayi badan ta saba hakan ba sai dan neman haɗin kan su, wanda yaji zai iya amsawa ya amsa wanda ba zasu iya ba ya juyar da kansa, kanta ta girgiza tana mamakin halin ƴan gidansu ba zasu taɓa canza hali ba, ɗakinsu ta shiga ta samu Mama zaune da tin shigowarta ta kasa fita tana jinta.
Da gudu ta faɗa jikinta tana cewa.
"Mama nayi kewarki?"

"Ɗaga ni wawiya kawai, bakya hankali wallahi shi ma yanzu haka kike masa?" Mama ta faɗa tana tureta daga jikinta.

Baki ta tura tana cewa.
"Mama ai shi..." Sai kuma tayi shuru ta kasa ƙarasa maganar da tasan in ta faɗa sai Mama ta zageta, canza salon maganar tayi tana cewa.
"Mama ina Laila? Khausar fa."

"Sun tafi makaranta ai, mai ya kawo ki ma tukunna?"

"Mama dan nazo gidanmu shine nayi laifi? Tafiya yayi yace in zo in kwana ko in ɗauki Khausar muje ta tayani kwana ni kuma nafi son gidanmu shine nazo miki, kwana zan yi muna hira dake." Tace tana murmushi.

Ɓata rai Mama tayi tace.
"Dawa? Ai ko sai dai ki ɗauki Khausar ku tafi dan ba'a ɗakina ba, ke ko kunyar idon mutane bakya ji, satinki biyu fa in ma kin kai."

Marairaicewa tayi ta koma yanayin tausayi tace.
"Mama shi ya faɗa fa."

"Ni ma ni na faɗa, zan barki ki jira Khausar ta dawo tin da kinzo amma ba dan haka ba da korarki zan yi."

"Amma Mama.."

"Ya isa." Mama ta faɗa tana tashi ta fita a ɗakin, za tayi magana taji ƙarar wayarta cikin jaka, hannu ta saka ta ɗauka, ganin shine ya sata murmushi sai kuma tayi yanayin kuka ta ɗauka muryarta na rawa kamar zata saka masa kuka.

"Matar!" Ya faɗa ta nashi bangaren.

"Umm." Tace tana ƙoƙarin matso hawayen ƙarya.
Jin muryarta a raunane ya sashi tambayarta.
"Lafiya Matar? Waya taɓa min ke? Ko kinyi missing ɗina ne?"

"Ba Mama bace tace sai na koma na kwana ni kuma tsoro nake ji gashi baka nan." Ta ƙarashe maganar tana turo bakinta.

Yanda ta ƙarasa maganar ya sashi canza salon maganar dan har tsakar kansa yaji wani abu yace.
"Matar kar kisa na fasa abinda ya kaini na dawo kawai dan in gyara bakin nan."

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now