page 23.

519 85 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 23.

Wayarta ta fara nema da rabonta dashi tin jiya, iya binciken ta bata samu ba hakan yasa ta hakura ta gama aikinta, wanka ta fita tayi ta koma ɗaki ta sa kaya.

Ɗakin su Batul tayi sallama baƙin kofa, Iya Rammace ta amsa mata tana cewa.
"Waye haka?"

Ƙaramin tsaki ta ja ciki ciki.
"Ni ce Batul nake nema."

"Bacci take." Ta bata amsa, bata jira ta gama maganar ba ta fara ƙoƙarin barin gurin ta koma ɗakinsu.
Wayarta na gurin Batul tabbas, ko jiya ya roƙeta da barin wayarta kusa da ita.

Da fata taji anyi ta juya, Batul na tsaye tana murza idanuwanta dan bacci.
"Lafiya kike nema na?"

Dariya tayi ganin yadda take duk a birkice.
"Wayata nake nema, yana gurinki?"

"Amma wallahi kin gama dani akan waya zaki tada ni, ki biyoni ki karɓa yana ɗakinmu."

Bayan Batul ta bi har ɗakinsu ta karɓi mata wayarta da tin jiya yake gurinta bayan dawowarsu daga gidan Aunty Sameera.

Karɓa tayi ta koma ɗakinsu, kunna wayar tayi ta lalibo lambar shi da ko saving ba tayi ba ta danna ƙira, tsaki tayi jin ma'aikaciyar kamfani ta sanar mata ba kuɗi ya sata kashe wayar tana jifa dashi.

Karar wayar ya sata kallo gurin ta tashi ta ɗauka, kallon lambar tayi har zata ɗauka ta tuna maganar Mama, hakan ya sata fasa ɗauka ta ajiye wayar tana bi da kallo har ya tsinke.

.
Wayar ya ciro daga kunnensa yana bi da kallo tin daren jiya yake kyira a kashe yanzu da ya gwada ya samu ya shiga amma ba'a ɗauka ba.
Hakan bai dameshi dan yasan ɗaukar wayarta sai Sa'a dan ya saba da hakan.

"Mai yake faruwa?" Yaji maganarta daga tsakar kanshi ya juya yana kallon mai maganar tana zama saman kujeran office din.

"Lafiya lau Dr, ya hidima da jama'a?"

"Allahamdulillahi ka tashi ne?" Dr Aishah ta tambayeshi.

"Ah a wani abu ne?"

"Shikenan kawai." Ta faɗa tana tashi tsaye.

"Ki faɗa min mana ko zan taimaka miki." Ya faɗa dan tsayarta .

Murmushi tayi tana cewa.
"Shikenan Dr na ɗauka ka tashine ka sauƙe ni a gida motata ta samu matsala jiya a hanyata ta komawa gida."

Tashi yayi daga kan kujeran da yake zaune.
"Muje kawai dama na gama aikin Abubakar nake jira."

"Ba matsala." ta faɗa mishi.

Kai ya ɗaga mata yana lalibo lambar Abubakar ya kira ya faɗa mishi ya wuce sai gobe, bayan sunyi sallama ya kulle office din suka fita.

Bayan ya sauƙeta a gida ya wuce gidansu, duk ahlin suna falo sunyi mamakin ganinshi yanzu a wannan lokacin amma basu mishi magana ba.

Bayan ya zauna suna taɓa hira wasu hankalinsu na ga tv.

"Ya labarin ƴata." Juyawa yayi ya kalli Aunty Ani.

"Lafiyanta lau, yau kwata kwata ban samu wayarta ba." Ya faɗa yana shafan kansa.

"Lafiya kuwa." Ta nemi ƙarin bayani.

"Ina tsammanin hakan dan bata cika ajiye wayar kusa da ita ba."

Murmushinta tayi halin Murshida sai ita.
"Ok ka gaisheta in kunyi waya."

"Za taji." Ya faɗa yana tashi ɗakinsa ya nufa dan ɗauro alwalar azahar.

Bayan gabatar da sallah a hanya ya sake gwada kiranta, nan ma ringin yake ba'a ɗauka ba.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now