page 43.

489 74 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 43 .

Rasa in da zata fara shiga ya sata tambayar office din sa bayan an nuna mata ta isa gurin taga a kulle, malamar asibiti ta tambaya ta kwatanta mata in da zata samesa, godiya ta mata tana nufan wajen.

Da sallama ta tura kofar ɗakin yana kwance dan har lokacin kansa bai bar masa ciwo ba, magani yasha ya kwanta ko zai samu bacci, Aunty Ani ta tafi gida wanka.

Jin muryarta ya sashi buɗe idanunsa ya zubawa kofar ido yana amsawa, ciki ta ƙarasa tana neman gurin zama ya mata nuni da ta ƙaraso kusa da shi.
"Ƙaraso nan."

Girgiza kanta tayi tana zama saman kujeran da ta gani tace.
"Nan ma ya isa."

"Please Seyyidah i need you beside me."

Ba yanda ta iya banda ta aika abin da yake so,farin ciki take son bashi a rayuwarsa, tashi tayi ta nufi in da yake gyara kwanciyar sa yayi ya matsa ya nuna mata kusa dashi ta zauna a tsorace.
"Ina kwana ya jikin?" Tace a ɗan tsorace.

Bai amsa ba sai hannunsa daya ɗaura saman nata hannun da yake saman cinyarta, hannunta ya rik'o cikin nasa ya damƙe yanda ba zata iya janyewa ba, a tsorace ta fara ƙoƙarin kwacewa duk dabararta ƙasa.

"Ka bari mana dan Allah." Ta faɗa masa kamar za tayi kuka.

Bai kulata ba ya canza maganar ta hanyar faɗin.
"Kinji abin da ya faru."

Kai ta ɗaga masa har lokacin tana ƙoƙarin zare hannunta cikin nasa jikinta har ya soma rawa dan yadda zuciyarta ke bugawa tamkar ba nata ba.

Murmushi yayi duk yana lura da ita hakan yasa yace.
"Kin amince da maganarsu Baba, Abba ba shine mahaifina sannan sai an samu Mahaifina a ɗaura aurenmu."

Tausayinshi ne ya kamata dan yadda ya ƙarasa maganar ya ƙara karya zuciyar ta.
"Bani da zaɓin da ya wuce haka." Ta faɗa masa.

"Zaki iya jirana na je na dawo." Taji ya tambaye ta.

Ɗaga masa kai tayi tana cewa.
"Zan jiraka ko nan da shekaru nawa ne."

Hannunta ya ƙara matsewa cikin nasa yana tashi zaune, fuskarta yake kallo ba wani kwalliya sosai hakan yana ƙara mata kyau, shima yafi son hakan.
"Kin yi kyau." Ya faɗa mata idonsa na yawo a fuskarta.

Murmushi tayi tana ƙoƙarin juyar da kanta yasa hannunsa ɗaya ya juyo dashi, damƙe idanunta tayi bata son haɗa ido dashi gaba ɗaya kunyarsa take ji, ko shi ya manta da ba auren a tsakanin su da zai dinga ƙoƙarin taɓa ta.

Bakinta ta turo har lokacin idanunta rufe tace.
"Ka bari mana in wani ya shigo fa "

Bakin yabi da kallo lips glow din ya zauna a bakin, yadda ta tura bakin shi ya sashi kai yatsun hannunsa saman leɓɓenta, sauƙar hannunsa saman leɓɓenta shi ya sata buɗe ido tana ƙoƙarin janyewa aka bankaɗo kofar ɗakin.

A tsorace ta juya taga Noor ce, hannunta tayi ƙoƙarin janyewa ya saketa ta matsa a gurin kunyar Noor taji ya kamata kamar ta nutse.

Nu nawa Noor tayi tamkar bata gani ba ta ƙarasa gurinta tana gaisheta, kasa amsawa tayi ta gaisheta ta amsa tana murmushi dan ta kula kunya ne ya kamata.

Gurin Bagus ta ƙarasa tana zama gefensa.
"Yaya ina kwana, ya jiki? Ashe ba kaji daɗi ba aka ɓoye min."

Tsaki yaja yana dungurin kanta.
"Ban san yaushe za kiyi hankali ba Noori? Allah shiryaki ƙira Dr Nura ya zo ya sallameni."

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now