page 61.

568 77 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 61.

Abba, Aunty Ani, Amman Zainab sun fi kowa shiga cikin tashin hankali game da maganganunsa, wai ana zata wuta a makera ta tashi a masaƙa, basu taɓa tsammanin faruwar haka daga wajenta ba.

Jin Mustapha ya gama bayaninsa yasa Bagus kallon Muhsina yana cewa.
"Muhsina ki faɗi iya abinda kika sani lokacin da aka saka ranar aurena mai dame kika fuskanta da har ya saka ki fasa auren."

Babanta take kallo sai kuma ta juya ta kalli mijinta ya ɗaga mata kai alamar ta faɗa gaskiya kar taji tsora, kai ta sunkuyar ƙasa tana cewa.
"Na fuskanci barazanar na rasa rayuwata kamar yadda Yayata Nanah ta fuskanta, dalilin haka yasa ko su Abba ban sanar dasu ba na tura maka saƙon na fasa daga baya Abba ya tambayeni dalili amma na ɓoye nace kawai na fasa ne."

"Ƙarya take Abban su, wallahi sharri suke mini, taya zaka yarda da irin wannan abun Alhaji, ni ce Maryam.."

"Shut up..!" Abba ya daka mata tsawar da sai da ya hargitsa ƴan hanginta, hatta Aunty Ani sai da ta tsorata da tsawan taja baya.

Kallonsa Bagus ya maida kan Zainab da take a tsorace yace.
"Zainab sauran ke."

Hawayen da take ɓoyewa ta fara cikin muryar kuka tana girgiza kanta tace.
"Ni ba abin da na sani."

"Please Zainab.."  Ya faɗa ganin tana neman ɓoye shaidarta, babban yayan Zainab ne ya taresa yana cewa.
"Zee kalle ni."
Kanta ta ɗago tana kallonsa ya watsa mata hararan da ya tsoratata yace.
"Za kiyi magana ko sai na ɓata miki rai."

Girgiza kanta tayi tace.
"Tsoro nake ji."

"Kar kiji tsoron kowa kiji tsoron Allah."

Shuru tayi kowa ya zuba kunne yana sauraronta tace.
"Tun da aka yi maganar aurenmu dashi na fara fuskantar barazana, har gida ta zo ta same ni tana mini tace kuma kar in yarda in sanar da kowa in ba haka ba zata iya kashe ni."

Kowa falon salati yake yi in ka duba Abba da ya gama sauraron Zainab ya maida hankalinshi ga bayanin jikin split ɗin ya gama ya juya yana kallon Mamma idanunsa cike da tashin hankali, itama kallonsa take ta kasa magana shikenan asirinta ya tonu.

"Ki faɗa min gaskiya hakane Maryam?" Abba ya tambaye Mamma da tana kallonsa sai gumi take haɗawa.

Ba yanda ta iya duk da ba tayi tsammanin haka za'a tarketa ba, hakan yasa ta ɗaure tace.
"Kayi hakuri Abbansu sharrin shaiɗan ne.."

"Sharrin shaiɗan Maryam, mai Annisa ta miki ko yaron nan da har zaki bi ta wannan hanyar dan hanasa farin ciki da jin daɗin rayuwa, eh."
Ya ƙarasa maganar da tsawa da ya sata buɗe baki da sauri tace.
"Ta kwace mini gida, ta cika gidan da yara ya kake so in yi?"

Kafin ta ƙarasa ya kwasheta da marin da ya jawo hankalin yan ɗakin gurinsu, cikin zafin rai da ɓacin rai Abba yace.
"Son abin duniya ya rufe miki idanu har kika aikata hakan ko? mai kike shirin faɗa mini, ko kuma ƙiyayya ce ta saki haka."

Shuru tayi tana riƙe da kumatunta zuciyarta na zafi tana cewa.
"Kayi hakuri Abbansu wallahi na faɗa maka sharrin shaiɗan ne."

"Tashi ki bar mini guri Maryam i hate you, today i regret for marrying you, get out." Ya faɗa da karfin da ya sata tashi tabar gurin.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now