page 11

619 88 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 11.

"Mai na faɗa maka? Ya ya mu kayi da kai?"
Mamma ta faɗa bayan zamanta kan kujeran ɗaya daga cikin ɗakinsa.

Tashi yayi daga kwance da yake, tun bayan da yayi sallah ya shigo suka yi hira da iyayensu wajejen ƙarfe tara ya musu sai da safe ya shigo ɗakinsa ya kwanta dan samun isasshen bacci kasancewar tashin ƙarfe biyar za suyi, yana shiga ta biyo bayanshi.

"Mamma mai kika gani?" Ya tambayeta.

"Mai na faɗa ma, wato ka nuna min yanzu baka jin maganata?"

Cikin sanyin murya Bagus yace."Allah baki hakuri Mamma, Amma ni iya sanina ban miki wani laifin ba."

"Amma ɗazu mai na gani da idona, tare da na naga kun fito a kitchen Kuma da zata fita ka bi bayanta."

"Wa kenan?" Bagus ya faɗa dan shi yama manta da anyi hakan.

"Wannan yarinyar mana Murshida." Faɗin Mamma na yatsine fuskarta.

Murmushi yayi yana gyara zaman shi tare da rik'o hannunta cikin na shi.
"Mamma ki daina tunanin wani abun ni da ita, yarinyar nan na ɗauketa matsayin su Noor ne na bata, ganin ƙanwata nake mata."

Ajiyar zuciya ta sauƙe tana tashi sai yanzu hankalinta ya kwanta, dan tasan in har Bagus ya faɗa abu to iya gaskiyar sa ya fada, shi mutum ne da baya ɓoye abu a rayuwarshi.

Sallama ta misha ya mata sai da safe kafin ya koma ya kwanta.

Bayan sunyi sallar asubabi, biyar cib Abubakar yazo ɗaukarsa tare da ƙaninsa da zai dawo da motar in ya sauƙesu, bayan yama iyayensa sallama tun sallar asuba, yasa bai tashi kowa ba suka nufa airport, ƙarfe biyar jirgin su ya ɗaga zuwa Lagos daga nan Legas ya ɗaga zuwa birnin Kuala Lumpur Malaysia.

Ƙarfe takwas da mintuna ta isa gidan, ba wanda ya farka, Baba Saude ta gama girki, itama ta fara aikinta cikin nutsuwa, sai wajen karfe goma suka tashi, kaf suka haɗu a dining table ban dashi, anan ta tabbatar ya tafi.
Duk da ba wani sabon su kayi ba amma ta ga gurbinsa da baya nan, da yamma haka da tazo komawa gida ta dinga tuna hiransu na jiya.

Ƙarfe sha biyu na rana a Malaysia suka isa wanda yayi dai-dai da karfe goma na safe a Nijeriya, bayan sun isa sun huta a masauki su ya ƙirawo gida da sabon simcard din da suka saya, ya shaida musu sun isa lafiya.

Tin da suka isa ya mai da hankalinsa ga abinda yaje yi, aiki suke sosai baya samun zama sai dare. Kullum yamma ko dare yana ƙiran ƴan gida su gaisa.

Ƙarfe Biyar Na Yamma dai-dai da karfe sha ɗaya na dare a kasar. Waya suke da Aunty Ani, Raudah tana ta zuba mishi surutu.

"Aunty na tafi."
Ya tsinkayi muryarta ta cikin wayar da suke yi, sosai yake buƙatar sake jin muryarta wanda shi kansa ya rasa dalili.

"Little sister ba aunty wayar."
Miƙa mata tayi ta karɓa bayan ta sallama Murshida.

"Aunty ki bata wayan in ba damuwa, ko har ta tafi."

"Waye kanan." Aunty Ani ta tambayeshi.

"Wannan yarinyar." Dan bsya jin zai iya furta sunanta.

"Ai Murshida, ta tafi." Ta bashi amsa.

"Shi kenan dama zamu gaisa ne."

"Bari in turo maka lambar wayarta kwanaki ta ƙirani nayi saving."

A dake kar ta mishi wani fahimtar kuma
"Shikenan ki barshi kawai." Ya faɗa mata.

Bata mishi magana ba ta kashe wayar tana laluban lambar ta, ta tura masa.

Ƙarar shigowar saƙo shi ya sashi buɗe idonsa ya buɗe yana bin numbern da kallo kamar ita zai gani ta ciki.

Ya share sama da mintuna goma yana shawara da zuciyar sa ya ƙira ko ya bari, wata zuciyar ta bashi shawarar ƙira kawai.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now