page 25.

501 82 1
                                    

AKWAI ƘADDARA 25.

Cikin farin ciki da annashuwa ya wayi garin ranar wanda ya daɗe bai kasance cikinta ba, hamdala ga Allah yayi ta jerawa a ranar.

Da safe bayan ya gaishe da Aunty Ani ya sanar mata yanda su kayi da Murshida, sosai tayi farin cikin jin hakan har ta fishi murna a nata ganin, anan yake faɗa mata ta sanarwa Babansu in ya dawo shima zai ƙara faɗa mishi.

Da addu'ar samun nasara ta bishi dashi, sosai yake jin daɗin addu'arta a ko da yaushe, ɗakin Mamma ya leƙa ya gaisheta yana faɗa mata in ya dawo akwai maganar da za suyi, da To ta bishi dashi kafin ya mata sallama yana fita.

A office ma bayan ya gama duba marasa lafiya, ya samu Abubakar a office nashi, bayan sun gaisa yake faɗa mishi abinda yake wakana.

Da murmushi a saman fuskar Abubakar yace.
"Kai kuma haka ake abu wuta wuta?"

"To kuma mai zan jira yarinya ta Amince." Bagus ya faɗa yana hararan Abubakar.

"Ku ɗanci soyayya mana."

Tsuke fuska Bagus yayi.
"Kasan dai ni ba yaro bane, bani da wannan time ɗin."

"Ka dai takurawa yarinya."

Murmushi Bagus yayi ysna shafa gefen fuskarshi.
"Ina so tana so mai ya rage."

Dariya Abubakar yayi cike da farin ciki ganin abokinsa na farin ciki da wannan zaɓin nasa.
"Hakane kam Allah tabbatar mana da alheri."

"Ameeen." Bagus yace yana tashi, bayan ya mishi sallama ya koma nashi ofishin.

Ɓangaren Murshida kam tin lokacin da su kayi da Mama zata fara sanar da Babanta akan maganarshi maganar bai ƙara haɗasu ba, ita kunyar Mama ma take ji.

Karfe uku ya tattara ya leƙa ofishin Abubakar ya mishi sallama ya wuce gida.

A masallaci ya tsaya yayi Sallah kafin ya wuce gida, bayan ya isa yasa Sanjidah ta kawo mishi abinci yaci ya watsa ruwa ya zauna kallo dan rage zama.

Karfe takwas da mintuna yayi sallama a kofar falon mahaifinshi, bayan ya amsa ya bashi izinin shiga ciki, shiga yayi yana samun guri ya zauna ya rasa ta ina zai fara mishi maganar data kawoshi, bai san yaya zai ɗauka ba? Yana tsoron kar yaƙi amincewa.

Da ido yake bin yaronshin, ajiye kofin hannunshi yayi yayi masa magana.
"Lafiya yaron Mamman? Bakin ka akwai Magana daga gani."
Duk da Aunty Ani ta mishi magana akan Bagus yafi son ya ji ta bakinshi.

Ƙara sunkuyar da kanshi Bagus yayi.
"Baba dama..." Ji yayi ya ƙasa ƙarasa maganar shi ya rufe baƙinshi.

"Dama mai? Wai kunyata kake ji? Ka faɗamin me ke tafe da kai?"

Tattaro jarumtar sa yayi yace.
"Abba dama yarinya da nake fatan ɗaura alaƙar da zai zame mana alheri ni da ita na samu."

Murmushi Baba yayi jin yadda gaba ɗaya ya kasa sakewa ya fito mishi baro baro, kunyar yaronshin na burgeshi.
"Fatan dagaske ta amince da hakan?"

Kai ya ɗaga misa yana cewa.
"Da yardarta ma na sanar maka, ina son a nemamin izinin fara zuwa wajenta."

"MashAllah Allah ya sanya albarka, dama jira nake naji ta bakinka Auntynku ta faɗamin komai, kayi magana da yarinyar sai muje mu gana da magabatan ta."

"inshaAllah Abba dama munyi magana da ita za tayi magana da magabatan ta in sun bamu lokaci sai aje."

"Wato ma kun gama komai." Abba ya faɗa da murmushi cike da zolaya.

Murmushin kunya Bagus yayi yana sosa ƙeyarsa bai ce komai ba.

"Ƴar wayece, ina nufin wacece ita."
Yaji maganar Abba ya daki dodon kunnensa, anzo gabar da yake tsoron faɗawa Abba wacece ita ɗin tin yanzu, bai shirya yanzu ba, yafi so sai ranar da za suje yaji komai.
Amma yaya zai yi? Dole ya faɗa mishi gaskiya.

"Abba Seyyidah Murshida ce."
Ya faɗa cikin dakewar murya.

Shuru Abba yayi yana tunanin ina ya san sunan, da ma mallakiyar sunan, jin Abba yayi shuru yasa shi dago ido ya kai dubansa gurin shi wanda yayi dai-dai da faɗin Abba na cewa.
"Murshida yarinyar wajen mai aikin da take yi kwanakin baya."

"Eh Abba." Ya iya faɗa yana maida kansa ƙasa.

Sosai Abba ya shiga cikin mamakin wannan al'amari, lalacewar har ya kai ya nemi auren yar mai aikinsu, duk dan gudun abinda zai faru ko gudun sake faruwar da yayi a baya.
Amma ikon Allah ya wuce komai, mai yuwa itace matarshi ko rabonshi shi yasa duk lokacin auren bai yi su sai yanzu, fatanshi kar lokaci ya sake maimaita kanshi.

Dogon numfashi ya sauƙe yana karantar yanayin yaronshin kafin ya furta.
"Bazan hana abinda Allah ya halarta ba tsakanin ku, Allah sanya alheri da albarka a duk abinda kake nema ko kake niyan aikatawa."

Matsawa Bagus yayi kusa da mahaifinshi da sauri jin maganganunsa.
"Abba nagode sosai Allah kara nisan kwana، nagode sosai."

"Ameen summa Ameen, Wato sai yanzu zaka matso kusa dani dan na amince."

Kunya yaji yana tashi ya fita da sauri, da kallon tausayi yabi bayanshi yana mishi fatan samun nasara a wannan lokacin.

Ɗaukar kofin yayi yaga baƙin shayin da yake sha yayi sanyi, hakan yasa ya ƙira Mamma ya sanar mata dan kawo mishi wani duk da ta sanar dashi zata dawo, dan duk ran girki bangaren mai gidan matan suke kwana.

Ba'a fi mintu biyar ba ta dawo cikin shirin bacci, sai zuba kamshi take marar misali, nuni ya mata da kofin gabanshi.
"Ɗan ki yasa shayine yin sanyi."

Na hannunta ta miƙa mishi tana ɗauke dayan tace.
"Ya shigone?" Bayan ta ajiye kofin a saman Center table dake gefe a ajiye ta dawo ta zauna.

Ɗaga kai yayi bayan ya hadiye wanda ya kurɓa yace.
"Yanzu yazo min da wata magana mai ban mamaki, ban sani ba ko ya sanar dake."

Da mamaki ta jero tambayoyi marar adadi.
"Wane irin magana? Lafiya dai ko? Mai ya faru? Bai sanar dani komai ba?"

"Aure yake nema."
Abba ya faɗa mata kai tsaye dan bai san ta ina zai fara amsa mata tambayoyinta ba.

"Aure! Aure dana sani?"
Ta fada a razane kuma tattare da mamaki.

"Kinyi mamaki ko? Nima nayi hakan, fatanmu Allah tabbatar da alheri dan nayi farin cikin jin hakan sosai."

"Baya tsoron abinda zai je ya dawo ko faruwar abinda ya wuce."

Girgiza kai Abba yayi da sauri yana tarar maganarta.
"Mu mishi fatan alheri kawai."

"Hakane, Allah tabbatar da alheri."
Ta faɗa a sanyaye.

"Ameeen ya Allah."
Faɗin Abba yana kawo mata wani hirar akan Noor da ita ma tana da manemi sai a haɗa bikin, amma gashi shuru shekara kusan ashirin da shida, da farko mazan sun fara zuwa sai kuma suka daina ya zamana daga sun zo basa jimawa suke rabuwa, yanzu kuma sun yanke ma shuru kamar anyi ruwa an ɗauke.
Ko Sanjidah ma ta isa aure shekararta ta goma sha tara balle Noor.

Nuna mishi tayi Allah yana sane dasu zai kawo nusu mazajensu har gida, suci gaba da addu'a.

Pharty Bb.
Nagarta Writers Association.

AKWAI ƘADDARAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt