page 18.

523 92 2
                                    

AKWAI ƘADDARA 18.

Sallamar da taji daga muryar da ba tayi tsammanin ba shi ya dawo da ita hankalinta ta kai kallonta gefen da aka yi, zuciyarta daya bugu har ji tayi ya kusa faso kirjinta.

Idonshi a kanta fuskarsa ɗauke da murmushin da ya zame masa jiki.
Ƴan matan sai kallon kallon suke tsakaninsu na son ganin wacece taja hankalinshi har ya tsaya ya kasa kuma furta komai.

"Bawan Allah lafiya ka tare mana hanya kuma ka ƙi cewa komai."
Sai lokacin yayi ƙoƙarin mai da hankalinshi ga inda yaji maganar tana fitowa, Rufaida ne tayi karfin hali furta hakan.

"Tambaya nake?" Ya furta hakan yana mai da hankali ga kallon Murshida da ta kafeshi da idanu.

"Allah yasa mun sani dan sauri muke."

Bai juya ya kalli mai tambayar ba ya bada amsa.
"Wata nake nema sunanta Sey.."

Girgiza kanta take a hankali tattare da alamar roko dashi kaɗai ya kula da hakan.

"Shikenan nagode."
Ya faɗi hakan yana komawa cikin motarshi, wani ajiyar zuciya ta sauƙe tana fara tafiya ganin sunyi gaba.

"Hi beautiful."
Ya faɗa yayin da ta zo wucewa taji ya faɗa, a tsorace ta juya ta kalleshi fatanta Allah yasa sauran basu ji ba.

Gira ya ɗaga mata tare da sakar mata murmushi, bata iya bashi amsa ba da sauri ta juya ta bi bayan ƴan uwanta.

Suna isa gida ana ƙiran magriba kowa alwala yayi ya wuce ɗakinsu banda Murshida da tin dawowarta ta shige ɗakinsu kasancewar tana hutu.

Magriba ta gota kaɗan taji wayarta dake ajiya saman mirror ya fara ruri, ba kowa ɗakin tin dawowarta har Mama, tashi tayi ta ɗauka tana bin lambar da kallo, lambar ta haddaceta a ƙwaƙwalwarta, kamar ba zata ɗauka ba har ta kusa yankewa ta ɗauka tana kafawa a kunnenta tare da sallama.

"Har na tsorata na ɗauka ba zaki ɗauka ba." Maganar sa biyo bayan sallamar da ya amsa mata.

Shuru tayi hakan yasa yaci gaba da maganar shi.
"Na tsorata ki ɗazu ko? Na sani am sorry."

Ajiyar zuciya ta sauƙe tana neman gurin zama.
"Ni ka daina bani hakuri."

"To ba ni nayi laifin ba."

"Ni dai ka bari." Murshida ta faɗa a shagwaɓe tana turo baƙinta.

"Please stop it." Ya faɗa ƙasa ƙasa, dan har tsikar jikinsa sai da ya tashi, sigar da tayi amfani dashi tayi maganar, ba zai iya jura ba, bashi da wannan ƙarfin.

"Zan ƙira ki." Ya iya faɗa yana kashe wayar, dafe kanshi yayi da hannunsa kafin yayi baya yana kwanciya saman kujera.

Wayartan ta bi da kallo tana mamakin abinda ya sashi kashewa, taɓe baki tayi, amma fa tana son magana dashi.

Tana wannan halin Mama ta shigo dasu Khausar da Laila, tashi tayi ta isa gurinsu.
"Mama lafiya, ina kuka je."

Bayan Mama ta cire mayafinta ta ajiye.
"Munje asibiti ne."

"Waye ba lafiya." Ta faɗa tana duba ƙannenta dan tsammanin ta ɗayansu ne ba lafiya.

"Kanin Asma'u Nuradden ɗazu suka kaishi, an basu gado shine muka je dubasu."

"Allah bashi lafiya."

"Ameen kema ya kamata gobe ki je ki gaishesu."

"Haba Mama, na mishi addu'a ai."

"Kin san dai yadda muke da mamar Asma'u ko, ko ba komai hakkin makotaka, kuma umarni na baki."

"Zanje Allah kaimu goben." Murshida ta faɗa tana barin ɗakin, ita fa ba zuwan bane bata so, tabbas sai ta haɗu da Mustapha.

Tana fita wajen ta haɗu da Batul da take ƙoƙarin shiga, hannun Murshida taja su kayi waje a zauren gidan suka tsaya ta san ba yadda mutum zai ji su kuma duk mai shiga zata hangoshi haka mai fita ma zata ganshi.

Bayan ta tabbatar hakan ta juya tana kallon Murshida hasken kwan fitilar wajen shi ya bata daman ganin fuskarta da kyau.
"Dai na kallona da manyan idanuwanki."

Kyafta idanunta tayi tana tsuke fuska.
"Ai irin naki ne, lafiya ma tukunna zaki wani jawoni kamar kaya."

"Daɗina dake baki da hakuri, magana za muyi ta ƴan'uwa tsakanninmu."

"Mainene ina jinki."

"Soyayya ku ke ko?"

Manyan idanuntan ta zaro har tana tsorata Batul dasu, ji tayi kafarta ya kasa ɗaukarta, shikenan ashe duk sun gane maganarshi, waya sani yanzu ma kowa ya sani a gidan.

Karfin halin buɗe baki tayi tace.
"Da wa?"

Harara Batul ta mata tana rik'o hannunta.
"Kinsan wanda nake nufi, wanda ya tsayarmu ɗazu, kallon da kuke bin juna dashi shi ya tabbatar mini da akwai abu tsakaninku, ba zan tambayeki ko takura miki ki faɗamin waye shi ba, saboda hakan shishshige ne kuma baki yarda dani ba, wanda hakan ya samo asaline daga tashin gidanmu da kanmu a rabe ya taso sai ta zama dole abu ke haɗamu, amma ni hakan ba'a son rai na bane, fatana mu dai na ƴan ubanci mu haɗa kanmu tamkar yadda sauran gida a duniyarnan suke yi, maganar yaron nan kuma ina miki murna sosai Allah tabbatar da alheri."

"Ba fa abinda kike nufi bane." Murshida ta faɗa cikin sanyin murya.

Murmushi Batul tayi.
"Faɗamin manene Seyyidah Murshida, ai ni ina jin yace Sey.. na gano balle tunda ya tsayarmu idonshi a kanki."

Girgiza kai Murshida tayi idonta cike da hawaye.
"Yanzu shikenan kowa ya sani."

"Ban san wannan ba amma tabbas da su Fauziyya sun sani da jaridar gobe na safe dake za'a buga." Batul ta faɗa tana dariya.

Murmusawa Murshida tayi dan bata da karfin dariyar.

"Kina sonshi kema?"
Tambayar da Batul ta mata ya daki zuciyarta da dodon kunnenta.

Hawayenta da suka zuba ta share.
"Ban sani ba Sister, zuciyata takan bugawa a duk lokacin dana ganshi ko naji muryar shi tin farkon haɗuwarmu, na rasa amsar, jiran amsata yake."

"Ki buɗe zuciyarki ki bata dama ta zaɓi abinda take so, in kuma ba haka ga mu bawa Mustapha, sannan ki yawaita addu'a."

Sai lokacin tayi murmushi ta ɗan ji sanyi a ranta da ta faɗawa Batul matsalarta.
"Sai dai wata Murshida bani ba." Ta faɗa dan ta tsani jin mai suna Mustapha.

Alamun takowar mutum Batul taji ya sata yin shuru daga amsar da zata bata.
Yayansu Kabeeru ne ya shiga hakan ya sa su barin gurin, bayan sun isa filin gudan kowa ya wuce ɗakinsu.

"Ina kika je?" Mama ta tambayeta.

"Wanka nayi"
Ta faɗa haka tana gyara gurin da zata kwanta, bayan ta watsa ruwa ta gyara jikinta ta shigo ɗakin. Mama ba tace komai ba taci gaba da abinda take yi.

Bata daɗe ba bacci ya ɗauketa.

Washegari karfe Goma da mintuna Mama ta matsa mata ta shirya dan zuwa gaishe da Nuradden a asibiti, wanka tayi ta shirya cikin bakin jallabiya ta yane kanta da maroon din gyale mai dan girma ba tayi wani kwalliya ba banda hoda da man baki da tasa, tana fita ta ɗauki kunun da Mama ta dama tin safe a cikin cooler ta fita.

Adaidaita ta hau tana fada mishi asibitin da zai kaita suka kama hanya, bayan ya tsaya a bakin asibitin ta biyashi kuɗinshi ta shiga ciki, da kallo take bin asibitin kamar ta taɓa zuwa.

Keep liking!!

fateenaguary thanks for the liking! I dedicated this page to you 🤗❤️

Pharty Bb.

Nagarta Writers Association.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now