page 4

777 116 2
                                    

AKWAI ƘADDARA 4.

Tana ganin yana kusanto gurinta zuciyar ta ya bada wani irin bugu, amma ta dake ta ci gaba da harhaɗa plates din, har ya ƙaraso kusa da ita yana kallon yanayin ta akwai tsoro a tattare da ita amma ta dake.

"Kina bukatar taimako?"

Ya faɗa yana ƙoƙarin daukar warmers, kallon ɗaya ta masa ta girgiza kanta alamar ah a, bai kulataba ya ɗauki manya manya biyu ya nufi hanyar kitchen, ajiyewa yayi ya dawo itama ta gama ɗeban sauran ta kai kitchen, ganin ba abinda ya rage ya sashi barin gurin.

"Nagode."

Ta faɗa can ciki tsammaninta ma ba zai ji ba, juyawa yayi ya kalleta da murmushi kwance saman fuskarsa kafin ya wuce ɗakinsa, ajiyar zuciya ta sauƙe ta fara goge gurin, duk iyalan gidan sun san daraja da girman Ɗan Adam.

Sai biyar da rabi ta gama ayyukanta tama Hajiya Maryam da Aunty Ani sallama ta kama hanyar gida.

Da isarta abinda aka mata ya dawo mata, ranta taji ya baci, ɗakinsu ta shiga Khausar da Laila suka nufota.

"Oyoyo Yaya."

Rungume ƙannenta tayi tana ajiye food flask na hannunta.

"Na kawo muku abu mai dadi amma baza kuci ba sai munyi sallar magriba."

Tana faɗa tana cire hijabin jikinta ta rataya saman kofa, Khausar da Laila har rige rigen fita suke, murmushi tayi ta bi bayansu ganin Mama na sallah bare ta gaisheta.

Bayan sun gabatar da sallah ta buɗe flask din tuwone daya tuku na semovita da miyar igushi yaji bushashshan kifi, bayan ta ɗibarwa Mama ta zauna ita da su Khausar da Laila suka ci abinsu ko ta kan tuwon gidansu basu bi ba, anan take duk ɓacin ranta na gidan ya wuce, burinta taga mahaifiyarta da ƙannenta na farin ciki.

Washegari.

Da farin cika ta tashi wanda ta rasa dalilinsa amma tabar abin abin akan yanayin da taga Mama da Khausar da Laila, karfe takwas ya mata a kofar gidan Aunty Ani, aikinta ta fara ganin ba wanda ya farka a gidan, mamaki take ace mutum har karfe takwas bai farka ba saɓanin nasu gidan tin asubabi babu mai komawa, wanke wanke ta ke yi bayan ta gama shara da mopping.

Jikinta tane ya Bata ana kallonta, tsaye yake wajen kusan mintuna biyu da shigowarsa, kanta ta juyar kamar basa za tayi magana ba tace.

"Ina kwana? Kana bukatar wani abu ne?"

Ƙarasowa ciki yayi yana amsa.

"Lafiya lau, Ya kike? Haɗamin tea sauri nake yanzu aka ƙirani emergency."

Yayin da yake mata duk wannan maganar ita kuma ta bar wanke wankenta ta fara ƙoƙarin haɗa masa batace kala ba, bayan ta gama ta miƙa masa ya amsa tare da fadin. "Thank you."

Bata ce komai ba sai murmushi da tayi ta koma wajen sink taci gaba da aikinta, a inda yake ya fara sha burinsa yasha ko kaɗanne ya fita, juyawa tayi taga yana sha a tsaye, kamar baza tayi magana ta juya.

"Ba kyau shan abu a tsaye."

Ya tsinci muryarta a dodon kunnesa, gurinta ya kallo kamar ba ita tayi maganar ba, ƙarasawa gurinta yayi tare da ajiya cup din ya kalli agogon hannunsa tara ta gota.

"Nagode da tunatarwa, sai anjima."

Yana faɗin haka ya fita a kitchen din sakamakon saurin da yake, bin bayansa tayi da kallo, kamarsa da ƴan gidan daban.

Share zancen da take yi tayi ta ci gaba da aikinta, bayan ta gama ta iyalan gidan suka fito ta gaishesu suka amsa mata kamar yadda suka saba da fara'a da murmushin da baya wucewa a fuskokinsu.
Bayan sun gama suka koma falo ta tattara wajen goge, tana cikin yin aka rangaɗa sallama tare da shigowa cikin falon, matashiyar budurwace da baza ta wuce shekaru ashirin da biyar ba tare da ita ƙaramar yarinya da shekarunta zai kai goma.
Amsa wa mutanen falon su kayi da gudu ƙaramar tayi gurin Hajiya Maryam ta faɗa jikinta "Mamma."

Rungume ta Hajiya tayi tana son yarinyar.

"My sweet daughter Barka da dawowa."

"Nayi kewarki Mammana."

"Nima haka My Raudah".

"Ni fa Rau?"
Cewar Aunty Ani tana kallonsu.

Murmushi Hajiya Maryam tayi tace.

"Ke naki gaisuwar sai anjima."

Dariya Aunty Ani tayi tana kallon masu shigowa ƴar suce Noor da ƴar yayan Babansu Zaituna, da sallama a bakinsu suka ƙaraso wajen iyayensu, bayan sun amsa musu suka tambayi ƴan gida, kasancewar Noor da Raudah da Sanjidah sun samu hutun makaranta, Noor da Raudah suka tafi gidan ƙarin babansu hutun sati biyu yau suka gama suka dawo tare da Zaituna sa'ar Noor.

Da sallama ta ƙarasa wajensu hannunta ɗauke da faranta ruwa da abin motsa baki, Noor da Zaituna ta gasar ganin zasu girme mata da kaɗan, ba laifi suka amsa mata cikin fara'a kafin tabar wajen.

"Wacce ita?"

Noor ta faɗa tana tsiyayan ruwan da Murshida ta ajiye.

"Murshin Mamar Murshida." Aunty Ani ta faɗa.

"Itace Murshidn?" Noor ta faɗa tana neman ƙarin bayani.

"Eh ba ruwa ta yarinyar aikinta kawai take yi."

"Yafi mata ai dan wasu masu aikin basu da kamun kai." Cewar Zaituna na ƙoƙarin kawar da maganar.

Karfe biyar ya shigo gidan da sallama ya shigo da gudu Raudah ta gurinsa ya ɗagata sama.

"Little sister."

"Am back big brother."

"Welcome back my dearest, Amma gaba gaba baxan iya ɗaukarki ba kinji nauyinki."

Turbine fuska tayi tana cewa "Ni dai bani da nauyi "

"Uhm uhm fa Raudah."

Yayin da yake zaman a ɗaya daga kujerun falon, Zaituna da Noor suka gaishesa ya amsa yana musu Barka da zuwa, bai jima ba yayi hanyar bedroom nasa, mintuna arba'in ya fito cikin doguwar jallabiya.

Ta musu sallama tana ƙoƙarin barin gurin ya fito ganin ta nufi hanyar fita shina ya fasa ƙarasawa ya ɗan d'aga murya.
"Mamma zanje masallaci magriba ta kusa."

"Bakaci komai ba fa." Ta faɗa dan tsayarsa.

Bai bata amsa ba ya fita yabi bayanta, tana fita ya fito ba tayi tsammanin zasu haɗa hanya ba, ganin shi kawai tayi gefenta yana tafiya, ɗan dakatawa tayi ta kallosa, hanya yake kallon.

"Ina wuni Ya aiki?"
Ta faɗa tana ci magana da tafiyarta.

"Lafiya kalau ya naki aikin."
Ba tayi tsammanin amsa daga gareshi ta tsinkayi muryarsa cikin kunnenta.

"Ummu Allahamdulillahi." Ta faɗa tayi gum da bakinta, tafiyar kurame su kaci gaba dayi har ya iso bakin masallaci dake layin unguwar su, anan taga ya tsaya. Wato dama masallaci zaije shine ya jera tafiyarsa da nata.

"Sai gobe ko, ko kina bukatar rakiya?"
Maganarsa ya dawo da ita sai yanzu taga ashe itama ta tsaya ganin ya tsaya.
A kunyace ta girgiza kanta sosai taji kunya. 'To ina hankalin ta ya tafi, ganin ya tsaya, me zai tsayarta ita?
'Dama ina ke ina haɗa tafiya dashi, hanyane kawai ta haɗalu ba yanda ya iya.'

Tafiya ta fara kokarin yi tayi taku uku ta tsinkayi muryarsa.

"Don't worry gobe zan miki rakiya har gida, yanzu ina sauri ne."

Da hanzari ta ɗago idanuwanta tana juyowa, murmushi yayi mata yana daga kansa alamar eh.
Cike da kunya ta juya taci gaba da tafiyarta ji take ma tana harɗewa da irin kallon da yake mata.

Nagarta Writers Association.

Pharty Bb
Wattpad phartybb
WordPress www.phartybb.wordpress.com
Okada phartybb.
#comment
#like
#phartybb
#onelove

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now