page 62.

488 72 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 62.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb

Washegari wajen karfe bakwai ya farka, bai tasheta ya lallaɓa yayi wanka, bayan ya saka kaya ya ɗauki paper da pen ya rubuta mata note ya ajiye a gefenta yana bata peck a goshinta ya fita, ko cikin ɓangaren su Aunty Ani bai shiga ba ya shiga motarsa ya fita.

Acan ya samu Abubakar yazo, bayan sun gaisa suka nufi office din Dr Nura, anan ya musu iso ga Dr Kabeer, bayan tambayoyi da Dr ya masa ya sashi yin test kusan uku, Nurse ya ƙira ta diɓa jininsa ta tafi dashi lab dan yi yace su jira zuwa nan da 30minutes, haka suka jira suna ɗan jansa da hira dan ganin ya fara shiga damuwa.
Kusan mintuna ashirin da shida Nurse din ta dawo ta miƙa Dr Kabeer kafin ta fita ya maida hankalinsa ga test ɗin, bayan ya gama dubawa ya kalli Bagus yana cewa.
"Dr Azeez duk bincike ya nuna ba abinda ke damunka, sai dai ina da wani nazari a kan hakan."

Bayan sauƙe ajiyar zuciya da yayi gama sauraron Dr Kabeer yace.
"Menene kuma Dr?"

"Are you married?"

"Yes 3 months ago."

Papern test ɗin ya miƙa masa da kuma wanda ya rubuta magunguna yace.
"Gobe kazo da madam a dubata may be rashin lafiyar ka na da alaƙa da ita."

"Dr.."  Ya furta hakan da mamaki.

Murmushi Dr Kabeer yayi yace.
"Don't worry everything will be fine."

"Ok thanks for your help." Ya faɗa suna tashi.

Da haka suka bar office ɗin, office nasu suka isa anan ya tarar Warmers masu kyau a basket da komai na breakfast da note a gefe, ɗauka yayi ya buɗe dan ganin mai a ciki.
'Please Mijin ka taimaka ka saka abu a cikinka kafin kasha magani please I Love You.'

Murmushi yayi yana ciro wayarsa a cikin aljihunsa ya ƙira lambarta, ringin biyu biyu ta ɗauka yace.
"Repeat what you said?"

"I love you." Ta faɗa tana kashe wayar.

Farin cikine ya ziyarci zuciyarsa bata taɓa furta masa hakan ba kai tsaye, duk da a cikin wayane amma yaji daɗin hakan.
Kaɗan yaci abincin yasha magungunan da Dr Kabeer ya rubuta masa ya ɗan huta, yaji daɗin shi har ya samu ya duba marasa lafiya duk da Dr Aisha tace ya bari yace yana jin daɗin jikinsa.

Ƙarfe ɗaya ya baro office ɗin da shigarsa gida kamar ya sani bangaren Aunty Ani yayi a can ya sameta suna cikin falon, Sanjidah na mata kalaba suna kallonsu, kowa yaga shigowarsa banda ita data bawa ƙofar baya hankalinta naga kallon da take na thriller movie duk a tsorace take.
Har ya zauna gefenta bata sani ba, yatsun hannunsa ya ɗaura saman wuyanta ya fara mata tafiyar tsutsa, a wani razane ta sake ihu tana tashi tsaye gaba ɗaya wajen suka saka mata dariya har dashi.
Rai ta ɓata ganin hakan yasa ya tsagaita dariyarsa yana tashi ya kama hannunta yace.
"Keep quiet sisters, zo muje muyi kallonmu a can ki rabu da wannan yaran."

Bata ko juya ta kallesu ba ta bishi, bayan sun isa bangarensu wanka yayi ta kawo masa abinci, kasa ci yayi yace ta dama masa kunu, hakan ko aka yi ta dama masa, yasha ba laifi kafin yasha magani haka ya hanata komawa wajensu kuma ya hanata kallo da fitinarsa ta biye masa.

Har dare sai bayan sallar magriba kafin da ya tafi masallaci ta koma, shima yana dawowa nan yayi ya samu ahlinsa gaba ɗaya zaune, sai yanzu yaji rayuwarsa ta fara sabuwa, sun yi hira anan kafin Aunty Ani ta korasu bangarensu ganin dare yayi sosai, bayan komawarsu sun kwanta zazzaɓi ya zuba masa, sai da ya sha magani kafin ya barsu su kayi bacci.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now