page 31.

498 79 4
                                    

AKWAI ƘADDARA 31.

Gaba ɗaya maganganun shi sun sata a wani yanayi ta kasa fassarashi ko ɗaurasu a mizanin da zata fassarasu, in har tace ta gane shine akan zai rabasu kenan? To ta wace hanya?
Bata jin akwai hanyar da zai bi ya rabasu ko yayi ƙoƙarin hakan dukkansu biyu sun miƙa lamarinsu ga Allah shi kaɗai zai karesu.

Haka ta koma gida ta sanar da Mama abin da ya faɗa, Mama bata kawo komai a ranta ba tace mata kishine hakan karta damu.

Duk babubuwan da suka faru akan idonta tana cikin motarta mai duhun gilashi tana hangosu, ta daɗe da shigowa layin tana bin gidajen da kallo.
Tana gani ya bar gurin ta kunna motar tana binshi a hankali, har ya samu abin hawa ya hau, da dan gudu ta zo ta bigi abin hawan.
Da kyar mai adaidaita ya samu ya saita kan adaidaita dinshi ya samu guri ya faka, Mustapha ya mutukar tsorata da hakan yana ganin yayi fakin ya fito itama dai dai lokacin ta fito daga cikin motarta ta nufi gurin su.

A harzuƙe Mustapha ya ƙarasa wajenta dan ranshi dama a bace yake ga koma wannan matar na neman kasheshi da ranshi.

"Allah baku hakuri fatan ba ku ji ciwo ba." Jin kalaman matar yasa ya fasa mata rashin mutuncin ya tsaya kallonta, babbar mace da kuɗi ya zauna mata.

"Bawan Allah sannu ko." Ta ƙara faɗan hakan dan ganin har lokacin ya kasa furta komai.

"Ba komai." Yace yana ƙoƙarin barin gurin dan komawa gurin mai adaidaita da ya tsaya a gefe.

"Ji mana, anan unguwar kake?" Yaji ta ƙara tambayar sa. Juyawa yayi ya kalleta yana daga mata kai.
"Eh lafiya?"

"Ni ma anan nake gidana yana layin farko, in ba damuwa muje in sauƙe ka a in da zaka je."

"Nagode amma bana bukatar hakan."

Ranta ya ɓaci da jin maganarshi wai yau itane tana rokar alfarma amma kuma aƙi mata, anya wannan zai taimaka mata.
Ganin neman abu take a gurinsa ya sata ƙara faɗin.
"Shikenan sai wani lokacin."

Bai ce komai ba ya ƙarasa wajen mai adaidaita ya sallameshi ya koma gurin motarta da ta tayar tana ƙoƙarin barin gurin ya buɗe ya shiga.
"Muje."

Bata ce komai ba tana barin gurin yana nuna mata hanya har kofar shagonshi da yake sana'ar sa ta samu guri ta faka motarta.

Yana ƙoƙarin buɗewa yaji kulle ya juya yana kallonta da alamar tambaya.

"Manene haɗin ka da ita?" Tambayar da ta watsa mishi kenan.

Da alamar tambaya ya ce. "Wa kenan."

Fuska ta yamutsa kamar bata son magana ko faɗan sunan tace.
"Murshida."

"Kin santa ne?" Ya tambaye ta shima da mamaki.

Kai ta ɗaga mishi. "Na santa, menene alaƙar ka da ita?"

"Ita ce wacce zan aure." Ya bata amsa kai tsaye.

Dariya tayi na rainin hankali tace. "Wacce dai kake so."

"Eh hakane buɗe min na fita."

Ba musu ta buɗe mishi ya fita ta ja motarta tana barin gurin dan ji take tamkar buƙatarta ta biya.

....

Bai bar wajen aiki ba sai yamma lis a ya koma gida, gidan ba kowa sai Aunty Ani da Noor da Sanjidah, Zaituna ta ɗauki Raudah sun fita.

Bayan ya shiga ya watsa ruwa ya ɗauro alwala magriba ganin lokaci yayi ya fita falon ya samu Noor zaune tana kallon series film da suke kallo duk yammaci.

Kujera ya samu ya zauna yana maida kalonshi ga TV ko zai fahimci wani abun.
"Ni kam mai kuke kallo anan?"

Dariya Noor tayi hankalinta gaba ɗaya yana ga kallon da take.
"Da daɗine Yaya."

"A hakan?"

"Eh dan baka kallo amma da zaran ka fara zaka ji daɗin shi."

Baya jin zai ji daɗin kallon series film shi ko yana yaro yafi son ganin cartoon balle yanzu da bashi da lokacin hakan, haka ya zauna baya fahimtar komai har aka ƙira magriba ya mike dan tafiya masallaci.

Bayan ya dawo ya saka abu a cikinshi ya samu keɓewa ya kira sanyin idaniyarshi suka taɓa hiran da rabi da kwata shi yake yi dan har lokacin ta kasa sakewa suyi hira mai tsawo dashi, shi har mamakinta yake yadda take ƙin mishi magana ba kamar farkon haɗuwarsu ba.
A haka su kayi sallama da juna ko wanne ya kwana da annashuwa a zuciyarshi.

...

Cikin sati ɗaya da ya rage aurensu Batul dangi da yan'uwan suka fara isowa na ko wani ɓangaren amare, aure uku kuma auren fari a cikin gidan Mallam Yusuf.
Hada hadar bikin da ake yi shi yasa kowanne ke kallon lokaci na tafiya da wuri, kullum dare sai ya ƙirata sunyi hiran da tin bata sakewa dashi har ta fara, tun lokacin kuma bata sake saka Mustapha a idanunta ta ba, ta bar abin kamar yadda Mama tace ta bari barazana ce kawai.

Kwana uku saura ɗaurin aure suka shirya kamu, inda su kayi a filin gidan Aunty Sameera kasancewar babbane, tsakaninsu iyaka su mata su kayi.

Amare ko wacce da irin atamfar da tasa, ƙawayensu kuma dukkansu anko iri ɗaya su kayi kasancewar duk ƙawayensu tare su kayi makaranta aji ɗaya.

Ƙannen amare suma tin daga kan Aneesa, Amal, Khausar, Khairiyya, Laila, Jamila sunyi ankon iri ɗaya sun sha kyau abinsu, haka su kayi taro lafiya suka gama lafiya har karfe tara. Bayan an watse ya rage ƴan matan gidan daga kan amaren zuwa kannensu , suka rage aka kunna musu kiɗa suka sha rawarsu a tsakanin su cike da annashuwa tamkar ba su ba.

A gajiye likis suka tashi a taron suka koma cikin gidan Aunty Sameera da nan suka kwaso kayansu suka dawo dan gidansu cike yake da ƴan'uwa, ko wanne burinshi ya samu ya kwanta tin safe suke zirga-zirga.

Wanka ta samu tayi ta saka simple doguwar riga ta kwanta a kan katifar da ta gani a ɗakin tana jin hayaniyarsu a falon ta kasa fita dan ta gaji, tana cikin haka ta tuna da wayarta da yake cikin jakarta, tashi tayi ta ɗauki jakar ta ciro wayar ta duba missed nashi biyar da saƙo daya, buɗe sakon tayi ta gani akan yana ta ƙiranta bata ɗauka ba.

Ji tayi gaba ɗaya ba daɗi ita fa wayar nema ta manta dashi, saƙon ta tura mishi cewa bata kusa da wayar suna hidima ne, tana gana turawa ya ƙirata bayan ya karanta.

"Hidimar mai kuke yi?" Taji ya tambayeta.

"Bikin sisters ɗina mana." Dan ita tama manta bata sanar dashi ba.


Keep liking...

Pharty Bb.

Nagarta Writers Association.

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now