page 5

732 125 0
                                    

AKWAI ƘADDARA 5.

Washegari Murshida bata bar gida da wuri ba sai wajajen karfe tara dan abinda tayi jiya taji kunya sosai har bata son tunawa, tara da rabi ya sameta kofar gidan Alhaji Mudassir Timber, inda take sa ran Bagus ya fita, bugun kofarta yayi dai-dai da buɗe get din gidan, baya ta taka a tsorace jiran ganin mai fitowa.

A hankali ya tuƙo motarsa ya fito a gidan dai-dai wajenta ya tsayar da motar tare da sauƙe gilashin motar, jin motar ya tsaye ya sata ɗago idanuwanta, karaf suka haɗa ido wanda ya sa bugun zuciyarta karuwa, shima nasa ɓangaren hakan ta kasance, ji yayi zuciyarsa ta bada wani sauti jin kwayar idonta cikin nashi.

Da hanzari tayi azamar kawar nata idanun, can kasan makoshi tace. "Ina kwana."

"Lafiya lau, ya mutanen gida." Ya samu furtawa akan leɓɓensa, bata iya amsawa ba, gani hakan ya sashi ɗaga gilashin motarsa tare da ja.

Da kyar ta taka ƙafarta ta ƙarasa cikin gidan, a falon gidan tayi sallama kafin ta samu damar shiga duk halin gidan suna babbar falon ƙasa, har gurinsu ta ƙarasa ta gaidasu, kamar yanda suka saba amsa mata yau ma haka cikin fara'a da sakin fuska yau ma haka, kafin ta fara yin aikinta.

Yin ranar sukuku ta gabatar da aikinta har yamma, tana ganin karfe biyu nayi tayi aikin yamma wajajen uku da rabi ta gama ta bar gidan, dan bata shirya ƙara sanyashi a idanuwanta ba.
Da daren a gidansu Mama sai da ta tambayeta meke damunta inda ta tabbatar mata da gajiyace kawai.

Kwana uku suna wasan ɓuya ana huɗu ya kasance ranar Lahadi, misalin ƙarfe sha ɗaya na safiya ta gama aikinta tana zaune saman wani kujera dake ajiye kasan bishiya in ka zagaya ta bayan gidan, bishiyoyine a jere reras da kujeru gurin kamar wajen shan iska, mutanen gidan basu cika zuwa gurin ba ganin hakan ya sata mai da gurin wajen zamanta.

Abubuwane suka taro sun cika masa ƙwaƙwalwa, tambayoyi yake dasu ya rasa mai amsa masa, wa zai tunkara? Mamma ko Aunty Ani? Mahaifinsa bai bashi fuskar kawo mishi tambayoyinsa ba? tun bayan abubuwan da suka faru shekarun baya yake da bukatar ƙarin haske, ko tashi rayuwar haka zata kare ba gaba ba baya?

Buɗe lumshashshun idanuwansa yayi tare da ƙoƙarin tashi daga kan three siter, tin safe yake kwance yake aikin tunanin mafita, ganin yana neman sawa kansa ciwon kai ya sashi tashi, kofar da yake sadasa da baya shi ya nufi ya buɗe ya fita, a hankali yake tafiya har ya iso kwanar da zai sadashi da wajen da yake zama in yana bukatar hutu.
Can ya hangota zaune ta ɗaura kanta samar kujera ta tsurawa reshen bishiyar ido, in zai iya kwatantawa yau kwana uku basu haɗu ba. Murmushi yayi ya nufi wajen gani yake kamar bata son haɗuwa dashi.
'Ta cika ji da kai.' Ya faɗa cikin zuciyarsa, hakan ko ya sashi kara murmusawa.

Ƙamshin da yake shiga kofofin hancinta shi ya fargar da ita daga tunanin data faɗa, karkata kanta tayi dan ganin inda ƙamshin ke fitowa, idanuwanta ta sauƙe cikin nashi, da azama ta miƙe tana gyara zamanta.

Murmushi samar fuskarsa har yanzu bai gushe ba ya ɗauki kujera ɗaya daga cikin jerin kujeru ya zauna.

"Sannu fa."

Yace da ita yana kai dubansa ga sararin samaniya dake ɗauke da hazo kasancewar yanayi na sanyi.

Bata iya amsa wa ba sai cewa tayi.
"Kana bukatar wani abu ne."

Kai ya girgizar har yanzu bai sauƙe ƙasa ba, tana ƙoƙarin tashi ya dakatar da ita ta hanyar faɗin.

"Yi zamanki ni na zo na sameki, in ma tashine Ni zan tashi."

"Ah a ba haka bane ina da abin yi ne" Faɗin Murshida na girgiza kanta.

Sai lokacin ya dawo da kallo shi gareta. Ko itama na gudunsa kamar yanda sauran ke yi? Amma ai ita ba abinda ya hadusu? Hasali bai yi sati Haduwarsu ba? Ko suna ganin abinda shi baya gani ga duk wacce ya raɓa sai tayi kokarin gudunshi?

Ganin tana niyar barin wajen ya sashi dawo da hankalinsa.
"Zo kiyi zamanki Kinga, gurinnan ya zame min wajen ɗebe kewana ba mai zuwa, amma tunda kinyi katsalandan zuwa, za kina iya zuwa ko yaushe."

Murmushi Murshida ganin bai yi fushi ba, ganin ta murmusa ya sashi yaji ransa ya sake ga shakkun da yake ciki.

"Ba komai wani lokaci zan dawo." Ta faɗi hakan tana ƙoƙarin barin gurin.

"Kema kina guduna?"
Ya jefa mata tambayar da ya samu kansa da fadar haka.

Juyawa tayi ta kallosa, fuskarsa kaɗai zata nuna tsantsan damuwa. Taku biyun da tayi dan barin gurin shi ta maimaita ta dawo garesa saman kujerarta ta zauna a dadare.

"Baki bani amsa ba." Bagus ya faɗa yana tsareta da idanunsa.

"Ni ba gudun ka nake ba, gani nayi kamar bai dace in zauna a gurin da kake zaune ba." Faɗin Murshida cikin sanyin murya.

"Saboda Ni waye? Sarki ko mai mulki?"

Girgiza kanta tayi ta kasa cewa komai hakan shi ya basa damar cigaba.
"Ni ba kowa bane face ɗan adam irin kowa, ko kinga na taɓa nuna miki wani hali? Ko kema kina mini kallon da sauran mutane ke yimin? Banda da siffar yan adam ne ko mai? Ko kuma..."

Ya kasa ƙarasa maganar saboda wani abu da ya tsaya matsa a wuya. Jin yayi shuru ya sata daga idanunta ta kalleshi, kallo daya ta mishi ta gano tsantsan damuwa da neman amsar tambayoyinsa.

"Ke nake saurara." Ya faɗa yana katse shirun.
'Ita ko mai zatace? Duk yabi ya daureta da jijiyoyin jikinta.

"Kinga ki faɗamin me kika sani ko kika ji game dani?"

"Ni ba abinda na sani illa kai ɗan gidannan ne kamar kowa, kuma banga wani hali ko wani mugun abu tattare da kai ba." Ta samu bakinta da furtawa.

"To mai yasa suke guduna?"

"Su wa?" Ta tambayeshi tana son ƙarin bayani.

Tsaki yayi tunawa da yayi ita da wacce yake magana da ita bata san komai ba game dashi hasali bata daɗe da zuwa gidan ba balle tasan abubuwan da suka faru.

"Zaki iya tafiya." Ya faɗa mata yana mai da kanshi ga kallon reshen bishiyar.

Bata matsa a inda take ba ta samu bakinta da furta. "Kana yawan addu'a, Allah kawo maka sauƙi a dukkan lamuranka."

Ta faɗa ta tashi tabar gurin, da kallo yabi bayanta har ta ƙurema ganinsa yaji dadin addu'arta a hankali ya furta ameen.

Anan ya faɗa doguwar tunani dolene ya tunkari iyayensa da dimbin tambayoyinsa, su kaɗai yake da yaƙinin zasu iya bashi amsa.
Wa zai tunkara Mamma ko Aunty Ani???

Please like!!!

Pharty Bb
Wattpad phartybb
Okada phartybb
WordPress www.phartybb.wordpress.com
#comment
#like
#phartybb
#onelove
NWA

AKWAI ƘADDARAWhere stories live. Discover now