ABDUL-MALEEK (BOBO)

By BilynAbdull

203K 11.2K 90

Labarin mai nuni da muhimmancin biyayya ga iyaye, gujema son zuciya, soyayya, zuminci, tare da cakwakiya tsak... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
31
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
29
30
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50
51
52
53

28

3.5K 207 1
By BilynAbdull

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 29

*_Assalamu alaikum. Happy new Islamic year 1439AH. Wish you all the best in this new Islamic year. Amen thumma Amen._*
4⃣8⃣

Mota yakoma yad'auki d'aya daga cikin wayoyinsa, sai hura hanci yakeyi, bugu biyu akad'aga, ad'an kausashe ya ce, "Ammar ina buk'atar yaranka.
    My guy lfy kuwa?.
  Mtsooowww wasu wawaye aka turomin, so nad'an koyar dasu zaman tarbiyya ne.
   Murmushi Ammar yayi, Dan yasan waye abokin nasa, okey kabani 15m. Katsal.
   Baice k'alaba ya yanke wayar, cikin motar yakoma ya zauna, amma murfin abud'e yake, k'afafunsa duk suna k'asa.
   Mintuna kad'an saiga motar police, tuni aka yayibi karnukan farauta acewar BOBO aka watsa amota.
   Bobo yakalli police d'in ya ce, " kukaisu asibiti, abasu kulawa ta musamman, zuwa gobe kuma natsincesu a Stations, yana gama fad'a yashige motarsa.
   Suma 'yansan Dan mota suka shiga, harya tada mota wani police ya kwankwasa MASA, sauke gilas d'in yayi yana kallon matashin police d'in batareda yayi maganaba.
  Umm yaya dama cewa nayi kozamu fara rakaka inda zaka tukunna.
   Fararen idanunsa yad'ago, wad'anda ahalin  yanzu sukad'an canja kala zuwa jaa, no karka damu Musadiq kuje kukaisu asibiti, sune keda buk'atar taimako baniba, saidai zuwa gobe kutabbatar da sunk'ara cin ubansu, harsai sunfad'i wanda yaturosu.
    d'an murmushi Musaddiq yayi wanda daga gani akwai sanayya tsakaninsa da bobo, ya ce, "ok yaya ALLAH ya tsare.
   Shima bobon murmushi yayi tareda jinjinama musaddiq sannan yaja mota yay gaba.
    Musaddiq yabi motar da kallo yana murmushi, shidai arayuwarsa yana k'aunar ya Abdulmaleek domin mutumin kirkine, yanzudai kalli anturo mutane dansu cutar dashi, yakuma sassanbad'esu amma saboda adalaci ya ce, " akaisu asibita abasu kulawa ta musamman, (ALLAH sarki aunty Ni'ima, ALLAH yajik'anki, inama kina darai har yanzu, daduk gidanmu sainace kinfi kowa dace da miji nagari).
   “araina na ce, "kenan k'anin marigayiya Ni'imane shi?.”🤔

   Guri yasamu yay farking cikeda tak'ama yanufi office d'insa, sai rissinawa ma'aikatan wajen suke suna kwasar gaisuwa, ransa a6ace yake danhaka ko amsa musu bayayi, hannu kawai yake d'aga musu.
    Sakatariyarsa ta jinjina kai, aranta ta ce, " yau kuma boss afusace akazo?.
   Zama tayi bayan yashige, turare tad'auka tak'ara fesama jikinta tareda k'ara gyara  fuskarta, sannan tanufi office d'in.
       Kamilu masinja yata6e baki yana fad'in yarinya wahala bata ishekibane, nasan ko matan duniya sun k'are wlhy oga bazai sokiba.
    Ahankali ta tura k'ofar tashiga, yana zaune akan kujerarsa ta alfarma, kwance yake acikin kujerar idonsa alumshe yanad'an lilawa ahankali, tabishi da kallo zuciyarta na zungurarta da wani Abu, a zuciyarta ta ce, "ALLAH ya mallaka minkai amatsayin mijina.
 
Na ce, " hummm."

K'arasawa tayi Inda firij yake, tad'akko drinks da cup tanufi inda yake.
    Saida tagama tsiyaya lemon sannan ta ce, "oga ga abinsha ko kana buk'ata?.
    Baice mata komaiba, saidai yabud'e idanunsa dasukayi d'anja Dan 6acin rai.
   Waye yazo nemana?, yafad'a cikeda karsashi.
    Tuni takama kanta, cikin d'ari² ta ce, ''mutum 3 sunzo nemanka amma biyu sun had'u da yalla6ai Kamal.
   Ya ce, "d'ayanfa?.
Ta had'iye yawu kuut, d'yan Ra'is ned'an gidan........ Hannu yad'aga mata alamar baya buk'atar k'arin bayani, yay mata nuni tatafi.
   Tafiya take cikeda salo tana juya mazaunai, hartakai k'ofa ya ce, "k zonan.
   Cak tatsaya k'irjinta na dukan uku², ahankali tajuyo saitaga bama ita yake kalloba waya yake dannawa, jiki a sanyaye tace sir gani.
     Idanunsa akan waya ya ce, "k sau nawa zan fad'a miki karki sake zuwamin nan da k'ananun kaya office?.
   A zuciyarta ta ce, " danka k'yasane, amma afili saitace sorry sir zan kiyaye.
   Tsaki yaja, har yanzu idonsa nakan waya ya ce, "wlhy daga yau kika sake banzar shiga kikazomin office abakin aikinki, 6acemin anan!!!!.
    Dasauri tafice Dan atsawace yay maganar.
   Yay kwafa tareda fad'in stupid gal kawai.
    Waya ya d'auka yakira kamal, bugu d'aya ya d'auka, kamal kana office ne?. Eh Abdulmaleek, ka isone?.
   " eh yanzu na k'araso".
   Okey ina zuwa.
     Laptop yajawo yafara danne dannensa, bayan wasu 'yan mintuna saiga kamal, hannu yabashi suka gaisa, sannan ya zauna.
   Wai ina ka mak'alene?.
   Laptop d'in gabansa ya ture gefe, yadafe tebir yana kallon Kamal, kabari kawai d'an uwa inacan an ritsani za'a kashe.
    Ban ganeba?, kisa kamar ya?.
    Ajiyar zuciya bobo ya sauke, ya CE, "wlhy kuwa kamal, wasu k'anan karnukan farauta aka turo waisu kar6i takardu a hannuna, nasandai bai wuce aikin wawayennan ba.
     Suwa kenan?.
Ra'ees da babansa mana, Dan babu wasu takardu ahannuna saina kes d'insa, kuma sakatariyata tace yazo nemana.
   Kwarai kuwa d'azu Nazo danmuyi magana baka nan, to ayayin shigowata mun had'u, zaifita nikuma zan shigo.
    Humm, kamal lokaci yayi dazan fito naci uban mutanen nan fa.
   A'a Abdulmaleek karkayi haka, har yanzu munada sauran bincike kaima kasani.
   Hakane, amma wlhy natsanesu.
   Wlhy nima hakantake, yanzudai bara naje, inada wata shari'a anjima kad'an, idan mungama zan dawo.
   Okey saika dawo to.
    
Tunda kamal yafita yabar office d'in bobo yafad'a duniyar tunani, tunanin Rahma ya kanainaye zuciyarsa gaba d'aya, haka kawai yarinyar tana birgeshi, ko kad'an batada damuwa.
    Murmushi yayi tareda kauda tunaninta yamaida hankalinsa ga tuno Wanda zai iya turo masa 'yandaba,  yamik'e Dan har yanzu ransa a6ace yake, wani wawan huci yafurzar tareda naushin iska, waini za'a turoma 'yan daba yafad'a cikin k'araji, yacije le6ensa yana gyad'a kai humm zanyi maganin koma wane d'an iskane.
     K'arasawa yayi gaban firij ya tsiyaya lemo akofi yakoma jikin windown office d'in na gilas ya tsaya, hannunsa d'aya a aljihu d'aya rik'eda kofin.
    Ahankali yakai kofin bakinsa yakur6i lemon, idonsa akan mutanen dake fitowa awasu bak'ak'en jeep,  Alhaji Abdurazak yafad'a yana gyad'a kai tareda ta6e baki, yad'anyi shiru alamar tunani, amma miyasa tunanina bai kawomin kai acikin wad'anda zasu iya turamin 'yan daba ba?.
   Yasaki murmushin nan nasa na mugunta.
    Sakatariya taturo k'ofar da sallama.
   Bai juyoba amma ya amsa sallamar.
   Ta ce, "sir.......
Hannu yad'aga mata, ya ce, " kice yashigo.
            Tad'an zaro ido Dan abin yabata mamaki, bayau Alhaji abdurrazak yafara zuwa office d'innan ba, kuma duk sanda yazo oga baya bashi damar shigowa, Amman yau tunkan tafad'i ko waye yace yashigo, kuma tasan yagansa ta inda yake tsaye, kai lamarin da mamaki.
  Itadai haka tak'arasa tasanar da Alh Abdurrazak, shima abin yabashi mamaki amma saiyayi tunanin ko bobo yaji tsorone.
     
Bobo yana tsaye baikuma juyoba har Alhaji ya zauna, saida yaja tsawon Minti biyu sannan yajuyo, taku yakeyi cike da isa harya k'araso mazauninsa.
    Abin ya harzuk'a Alhaji amma saiya dake.
      Bobo dake lila kujerarsa ahankali, idonsa akan alhajin ya ce, "Alhaji mike tafe dakaine?, yay maganar cikin salonsa na isa.
      Alhaji yacije le6en jin haushi, saikuma yayi murmushi Barrister nazo maka da Business ne.

Bobo-- hummm wane irin business?.

Alhaji-- Akan aikine.

Bobo--- miyasa saini?.

Alhaji-- saboda ka cancanta.

Bobo-- kayi kuskuren fahimtar hakan.

Alhaji-- miyasa kayi gaggawar yanke hukunci?.

Bobo-- saboda hakane yadace, kuma nasanka nasan kaina, bamu dace da had'a business ba.

Alhaji-- a'a Barrister ka saurareni.

Bobo-- mizaisa na saurareka?.

Alhaji-- Saboda nayimaka bayani yanda zaka aminta dani.

Bobo yayi murmushin rainin hankali, Alhaji miyasa kakeson takuranine?.
      Kayi hak'uri maganata mai muhimmancice tasha banban data baya Barrister.
     d'an kafeshi da ido bobo Yayi, dayin tunani na second 20, yalumshe idonsa ya ce, " INA saurarenka.
    Murmushi Alhaji yayi, azuciyarsa ya ce, "dole ka saurareni aii, yagyara zama yana fad'in Barrister dama akan maganar yaron aboki nane Alhaji sunusi dala, nawa kakeso mubiyaka ka lalata shari'ar?.
    Bobo bai amsa masaba, hasalima hankalinsa yana kan bodyguard d'in Alhajin dake k'ok'arin zarar wata takarda da bobo ya ajiye akan Derk's d'insa. Murmushi bobo yayi ya ce, " mai gadi zaka saidama mai k'osaine?.
    Dasauri bodyguard d'in yacire hannunsa Yakuma matsa baya.
     Bobo ya girgiza kai yana maida kallonsa ga Alhajin, INA saurarenka.
     Alhaji da haushi yakashe, jiyake tamkar yasa aharbe MASA bobo Dan haushi da tsanarsa dayayi, yazaro sigari yasaka abaki, dasauri d'aya daga cikin bodyguard d'in yakunna leta zaisakama alhajin....hannu bobo yad'aga masa, yatashi tsaye tareda rankwafowa akan tebir d'in yasaka yatsunsa biyu yazare sigarin bakin Alhajin yana girgiza kai, sorry Alhaji ba'a shamin sigari a office, saboda yana lalata lafiyar maisha da mai shak'ar warin.
    Ya ajiye masa kusadashi akan tebir d'in, gata nan idan katashi tafiya zaka iya d'aukar kayanka, Yakoma ya zauna.
   Wani Abu ya danna yay k'ara saiga sakatariyarsa da Sauri tashigo, bai kalletaba ya ce, "kawoma Alhaji abin sanyaya mak'oshi Dan yana buk'ata.
     Okey sir, tafad'a cikeda girmamawa.
     Alhaji kam ya k'ame azaune, lallai yak'ara tabbatarwa yaron nan d'an iskane, amma zasu gyaramasa zama, a fusace Alhajin yamik'e yakar6i lemon da sakatariya tamik'o masa yay jifa dashi, kofin yadaki bango ya tarwatse.
     Wata dariyar rainin hankali bobo yayi, yamik'e yana tafa hannayensa wooow! Alhaji ammafa ka burgeni, kaga yanda kayi d'innan haka nayima yaranka Nima d'azu da safe, saidai banbancin d'ayane, kai Kofi kafasa, nikam mutane na jibga.
     Aburkice Alhaji yake kallon bobo kuma atsorace, amma saiya danne yahad'e fuska tareda Nuna bobo da d'anyatsa, kai k'aramin tantiri kashiga hankalinka, yaro kai k'aramin naman dajine idan yanzu mukaso saimu hallaka ka tamkar yanda muka hallaka.........haba Alhaji mikakeson fad'ane haka?.
       Bodyguard yay saurin Tatar numfashin Alhajin.
      Bobo yayatura hannayensa a Aljihu yana murmushi, ya ce, ''no no no mai gadi, Daka barsa yak'asa fad'a kaga ya ragemin nauyin bincike, amma babu laifi hakanma ngd sosai  yak'are maganar da d'aga fad'a yana ta6e baki, aii kobai fad'aba nasan yanaciki.
   Yakuma gyara tsayuwa, yataka daf da Alhaji ya tsaya, ya ce, "Alhaji kakirani k'aramin naman daji.
   Bakayi k'aryaba, tabbas ni naman dajine mai amsa suna *_ZAKI_*, ni zakine bana 6arnar banza, ammafa duk sanda naji yunwa kowa Shiga hankalinsa yakeyi, Ku saurari fitowata Dan duk sanda naji yunwa saina lak'umeku amatsayin abinci mafi Girman k'an k'anta darashin daraja............
    Kai!!!!. Alhaji yakatse bobo atsawace, yanunashi da d'an yatsa Abdulmaleek Aliyu kataka a sannu zakinma yanada nasama dashi ko'a cikin dajin.
   Dariya bobo yayi ya ce, " hakane Alhaji akwai manya manyan namun daji adokar daji, wad'anda sukafi zaki Girman jiki harda shekaru, amma girmansu baya hana zaki ya kacaccalasu aduk sanda ya harzik'o, barema idan yanakan ganiyar k'uruciyarsa, Dan haka Alhaji abdurrazak bulama Ku saurari matashin zaki yana nan tafe gareku, zaka iya barmin office kuma ka saurari sammaci, Dan zan maka ka akotu kaida karnukan farautarka, inason bin ba'asin bibiyar numfashina da kukeyi.......
   Fuuuuu Alhaji yafice batareda yaji k'arshen zancen bobo ba, jiyake idan yakara minti d'aya a office d'in zuciyarsa zata bugane kawai.
   Wani wawan tsaki bobo yaraka Alhaji dashi.

_(Na sauke nannauyan numfashi Dan ganin anrabu lafiya bobo baikai dukaba, danni yanzu tsoronsa nakeji)._

*_bayan kwana uku._*
      Yau tsawon kwanaki uku safna tanata sak'awa da kwancewa, kullum Neman hanyar dazai kaita gidan Rahma takeyi amma tarasa gaba d'aya, tayi wujiga² saboda rashin mafita.
    Ganin babu yanda zatayi yasa tasaki jikinta tanata harkokinta, agefe kuma kullum saita turama bobo message.
   Tunbaya kulawa har yaudai yaymata replay, wani uban tsalle tazuba Dan dad'i, tad'ane gado tanata tsalle abinta.
   Ganin yayi mata replay yau yasa tak'ara masa wani massage d'in na kalamun soyayya masu dad'i, amma har dare babu amsa, data kirama saiya katse kiran yakashe wayar duka.
    Lamarin ya Sosa ranta amma saita dake, tana fad'in k'ila baya kusada wayarne.
  
Nidai araina na ce, "hummm.

*_kotu_*
    Ayaune kuma su bobo suka koma kotu.
    Bobo bai k'asa aguywa ba yakawo manyan hujjoji da shedu masu k'arfi wad'anda suke nuna haneef ya aikata fad'e ga muheebat. Ciki kuwa harda muheebat d'in kanta, wadda ya sulaiman yayma aiki ayanzu haka tana magana.
     Bobo yak'arasa kusada muheebat ya ce, " muheebat kotu tanasonji miya faru dake aranar 16/8/2017?.
       Muheebat matashiyar yarinya mai wayo, tagyara tsayuwa, idonta na zubda hawaye ta ce, "yaya aranar  data kasance 16/8 mama ta aikeni shagon Haleedu domin nasayo mata sabulun wanka.
   Fitowata kenan Haneef yafito daga gidansu da mota..............

Continue Reading

You'll Also Like

1.9M 121K 73
# Scribe _ Aster_Rain # Start Date [ 5.1.2021] # End Date [ 26.5.2021] # Total Chapters _ [52 ]- Extra [15 ] Complete # Cv photo credit to orginal...
188K 18.9K 73
လှပကြော့ရှင်းသော ချစ်ခြင်းမေတ္တာသည် အမုန်းတရားမှ စတင်ပေါက်ဖွားလာခြင်းဖြစ်၏။ Own Creation by Moe(JE Rain)
2.4M 152K 97
လူတိုင်းပါးစပ်ဖျားမှ ဇမ်းဆိုတဲ့ကောင်က အပေအတေကောင်လို့သမုတ်လဲ သူတို့သတ်မှတ်ချက်အတိုင်းသွားပါစေ.....ကိုယ့်ထမင်းကိုယ်စားပြီး သူများစကားတွေကိုထိုင်ခံစားန...
1.7M 69.2K 79
ငါလား.... စိတ်ချ...... နိဗ္ဗာန်ရောက်ရင်လည်း မင်းကိုပဲ ချစ်နေအုံးမှာ.......... သုနေတင်ထွဋ် ကမ္ဘာပျက်သလို လေပြင်းမိုးသံတွေထ...